← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 111

Sashe 92

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali ta zauna akan hannun kujerar da umma take zaune tana cewa “umma ina kwana !”ta gaishe da umma tana daukar littafinta na jiya .umma ta amsa mata muryarta cikin wani irin yanayi maryama ta dubeta a tsanake qirjinta na bugawa so take ta gano ko akwai wani abu dan haka jikina a matukar sanyaye tace “umma ya naji muryarki tayi wani irin ?”me murya ta tayi maryama ?ta tambayeta tana dubanta “ai umma ji nayi muryarki tayi wani irin ba kamar yadda na saba jinta ba sannan yanayinki kmr kinyi kuka .”ta qarasa maganar tana jin wani irin mummunar fad’uwar gaba.murmushi umma ta sakar mata tana cewa “ke fa matslarki kenan saurin rud’ewa babu abinda Ke damuna kece ma zance yanayinki kmr kinyi kuka bama kamar bane kinyi kuka dan ga sheida nan a little danunki bata da ja domin ita kanta tasan tabbas a irin kukan datai dole za’a gane ba “tabbas nayi kuka umma amman acikin mafarki .”umma bata mutsa mata ba amman tasan ba’a mafarki bane azahiri tayi kuka amamn tunda ta zabi ta fad’a haka shikenan “na had’a mana tea mai dadi bari naje na kawo miki jirani ina zuwa .”umma ta mike ta nufi kitchen inda maryama tabi bayanta da kallo mai tattare da tsantsar qauna tana zaune umma ta fito ta dawo gabanta ta tsaya tana mika mata cup din tea “ga naki tea tasa hannunta ta kar’ba cike da girmamawa tace “na gode sosai ummata umma ta kai nata cup din baki ta kur’ba tana cewa kai tea din nan yayi dadi sosai hakan yasa maryama ta kai nata cup din bakinta ta soma kur’ba tana lumshe ido “gsky ne umma yayi dadi kuma ya sha bambam da sauran tea “kuma kinga bashi da wata wahalar yi ba idan zaki yi ki samu kanufari,lipton tafarnuwa mint leave da gayen nahna’a shikenan ina son ki koya dan bamu san wani irin mutun zaki aura ba, idan allah yasa mai yawon sha tea ne shikenan sai ki dinga masa irinsa” kai umma duk maganarki bata wuce ta aure nifa ynzu ba aure bane agabana kamar yadda na sha fad’a miki burina a yanzu mu bar gidan nan “nasani amman kibi komai ahankali” umma ta fad’a tana dubanta a natse kafin ahankali ta cigaba da magana ina son ki bani aron hankalinki jin haka yasa zuciyar maryama ta fara tsinkewa ina son nayi miki magana akan wani abu zuciyarta ce ta cigaba da tsinkewa yayinda ilahirin jikinta ya d’auki rawa babu shiri ta ajiye cup din hannunta ta tsura mata ido “muryarta a sanyaye tace “ina sauraronki umma “ina son Kiyi aure maryama bazan so ki cigaba da rayuwa haka ba wani irin ajiyar zuciya ta sauke mai qarfin saka makon ba abinda tayi tunanin bane “ muddin ban baki shawa rar kiyi aure ba lallai ban cika mai adalci ba ,aure yana daraja kuma zai kareki daga dukkanin wata matseefa “in sha allahu zanyi umma amman ba yznu ba dan ahalin yanzu babu wanda yace yana son maryamarki ko da yake kin dai san maryamarki da bakinjini .”ta fad’a tana dan murmushi “.

“ni maryamata bata da wani bakinjini kisa niyya sai Allah ya taimakemu ,shikenan umma naji bari na wuce aiki lokaci na tafiya .”har tayi taku biyu ta kira sunanta “maryama !ta tsaya cak batare data juyo ba ki tsaya bari naje na kawo miki custard lokacin data juya alokacin maryama ta juyo tana duba agogon hannunta, lokaci ya soma tafiya umma bata wani jima ba ta fito hannuta rike da wasu flaks guda biyu kanana
ta miko mata daya maryama ta kar’ba tana murmushin jin dadi “kai gaksy umma kina ji dani shiyasa nake sonki fiyye da komai kamra Kinsan kwana biyu nayi missing custard dinki ai shiyasa nayi miki dan nasan kina so ga naki ,wannan d’aya kuma na mai gidanki “what !”
Maryama ta furta da karfi jikinta har rawa yake tsabar rudewa “umma wa kenan kike magana akai wa custard ?wa kuwa bayan mai gidanki mr ata shi zaki kaiwa nasan bai ta’ba shan custard irinsa ba “what !” wai mr..”mr ata kike nufi ?ta fad’a murayarta na rawa me zai yi da wani custard umma?” ke kike tunanin mai zai yi dashi ke dai ki kai masa ki gani “murmushi maryama tayi tana cewa “amman dai umma da wasa kike ko ?” idan ba haka ba ta yaya zan kai wa mr ata custard?”

“to ke mai yasa kike mamaki ke dai nace ki kai masa kuma kice inji mamanki “no no umma karki damu kanki wallahi baki san waye wannna mutumin ba shiyasa ,mutumin da bashi da bambamci da hawainiya mutunin da zuciyarsa bata da bambamci data dutse kai zuciyarsa tafi ta dutse karfi mutumin da babu abinda yasani sai wulakanci da tozarci shine mutumin da kike tuannin na kaiwa custard?” ina bazan iya ba umma ba,” tsaya maryama ina son ki fahimceni kema na rasa gane kanki wata rana kice mutumin kirki ne wata rana ki canza magana ,ni wanne zan dauka aciki maryama tai shiru kawai cikin tsnanin damuwa dan tasa aiki ja umma take son bata ,duk abinda kike fad’a akansa ni dai abu daya nasani zuciyata tana son shi a haka duk rashin kirkinsa shine yayi nasarar dawo miki da farinciki da walwalarki dan haka ki amsa ki masa idan na isa dake idan kuma ban isa dake ba nasani.” lumshe idanu maryama tayi “.
“na fahimceki umma amman walalhi mutum ne shi mai wuyar shaani”nasani !wallahi umma da wahala ya karba ki fahimceni ba wai ina jayayya dake bane halinsa nasani “nace miki zai amsa ki kar’ba to ni yanzu idan na kai masa mai zance masa ?”
tai maganar tana dafe goshinta umma tace “ bazanki bin umarnina bane ?”babu shiri maryama tasa hannu ta kar’ba “yauwa sai kin dawo Allah ya tsareki “ ahankali ta juya ta bar bangaren da sauri inda ta bar umma tsaye tana kallonta “maryama kenan bazaki gane abinda wannna mutuminn yake nufi dake ba sai nan gaba kin kasa fahimtar mai yasa ya damu dake, me yasa yake yawon fushi akanki ,mai yasa ya damu matukar sai kinyi aiki akarkashinsa ,ni dai nayi imani akwai wani abu acikin ransa akanki, koma dai menene Allah kasa mu dace Allah yayi miki kyakkywan zabi mafi alkairi arayuwarki da addininki.”

Ahankali maryama ta shigo ma’aikatan tana gyara zaman jakar dake kafad’anta tare da rike qaramin jakar da umma ta sako mata flaks ciki duk ilahirin jikinta yayi wani iri yayinda zuciyarta ke cike da tsannain fargaba “maryama ki sanyawa jikinki jarumta sannan ki karkafa zuciyarki, yanayin yadda kike damun kanki akan abinda bai kai ya kawo ba, yanayin ne damuwa zata miki yawa.”
ki samu natsuwa ba dole sai kin bashi sakon umma ba zaki iya bawa wani ya shanye a madadinsa tana tafiya tana zance zuci a natse ta shiga office dinsu ta gaishe da mutanen data iske ,sai dai babu wanda ya amasa mata bare ya kalli inda take, sai yusura kad’ai ta amsa mata sa’banin jiya tana kallonta cike da tsananin tausayi da mamakinta dan har lokacin bata daina mamakin hotunan jiya da’aka tura masu ba .”

Maryama tana tsaye madam some ta shigo ta wuce ta gabanta tana kallonta tana zance zuci tare da nazarin maryma har a wannan lokacin zuciyarta bata bar mamakin mami da dalilin da yasa ta tambayeta tsakanin maryama da mr ata ba ,da kuma dalilin mr ata na cewa lallai ta tabbatar maryama ta shiga motarta kuma lallai ta kaita har unguwar su “amsarki itace mr ata yana tsananin son maryama haka ma mahaifiyarsa ta fahimci irin son da yake mata shi yasa ta kiraki jiya domin ta tabbatar
Numfashi ta sauke adaidai lokacin da maryama tace “good morning ma !” madam some ta amsa mata ,inda maryama ta samu waje ta zauna ta ciro littafinta tana dubawa sai dai bata fahimtar komai “maryama bai kamata kiki bin umarnin umma ba ,meye aciki ki kai masa idan ya kar’ba fine idan bai kar’ba shikenan sai ki bawa wani amamn idan kika ki bashi idan kin koma gida ta rutsaki me zakice mata?” ko idan tace ki rantse me zaki ce ?”.
shiru tai kawai tana tunanin yadda zatayi bayan wasu mintuna ta mike ta nufi office dinsa bata iske madam some a mazauninta ba dan haka ta soma qoqarin shiga ta ajiye masa ta kama gabanta inda ahankali madam some ta kai hannu ta dafata da sauri ta juyo jikinta na wani irin rawa lafiyarki maryama me kikeyi ?sorry ma ta fad’a bakinta da jikinta na rawa kina bukatar wani abu ne ?no ..”no ma .”meye wannan rike a hannunki ?”amm daman mamana ce tayi wa mr ata custard tace na kawo masa .”
nan take gaban madam some ya bada rasa haka ma sultana dake tsaye a bayansu dan tana hankalce da duk wani motsin maryama “kutumar uba can .”sultana ta furta tana cewa” lallai ma yarinyar nan yayinda madam some tace “shikenan kije ki fara aikinki kafin yazo dan har yanzu bai qaraso ba tukun, jiki a sanyaye ta juya bayanta da zumar komawa office tana gama juyawa taga sultana tsaye tana jifanta da wani rikitaccen kallo wanda yasa hantar cikinta kad’awa bata ce mata Uhm ba bare uhm uhm hakan nan yau kallon nata ya saukar mata da mummunar fargaba mai tsanani.”sultana ta cigaba da aika mata da mugayen kallo mai had’e da harara.”

Maryama na tsaye cikin tashin hankali da tsananin fargaba sai gashi ya shigo ya iskesu tsaye “good morning sir”. ta furta da sauri qirjinta na bugawa “morning “!kawai yace tare da kallon inda madam some take yace some kije ki fad,awa duk wanda aka turawa hotunan nan su goge kuma muddin ya fita nayi bincike na gano wanda ya fitar dashi qarshen aikinsa yazo bayan na d’auki mataki akansa” okay sir yana gama fad’ar haka ya shige office dinsa yayinda maryama ta sauke numfashi tana mai Jin farinciki ta koma office da sauri sultana itama ta juya ta shiga wani office ta samu waje ta zauna tana tunanin matakin da zasu d’auka akan maryama.”
Chapter 92 · 0% Book details