← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 111

Sashe 59

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da tausayawa maryama  ta kira sunanta har sau biyu sultuna!sultana !!sai dai sultana bata tsaya ba sai ma qarasa wucewa  da sauri tayi ,kai tsaye marayama ta bar abinda take ta juya ta nufi kofar   office dinsa  tana cewa "may I coming sir ?sai daya sauke naunayen ajiyar zuciya jin sautin  muryarta mai sanyi sannan yace "coming !”dan tun safe bai ji muryarta ba sai yanzu ta shigo cikin office din a natse ta tsaya agabansa tana kallonsa a lokacin yana duba wani file dan haka bai dago ya kalleta ba ta cigaba da kallonsa a tsanake “kyau iya kyau ai dole mata su rikice akanka ganin ya shareta kuma tasan halinsa idan zata shekara tsaye matuqar bayi niyyar yin magana ba bazai mata ba  .”dan haka muryarta a sanyaye tace "sir ina son nayi magana da kai ko zan iya ?”shiru yayi batare daya dago ba har ta cire da zai yi magana sannan ta jiyo sautin muryarsa acan kasan makoshi “uhm go and ahead “.

“Dan Allah sir me yasa kake yawon yiwa sultana ihu ko hantarrta fiyye da kowa acikin ma’aikatar nan alhalin ita din yaruwarka ce ta jini ?yana jinta amman yaki yin magana sai ma ajiye file din hannunsa yayi ya d’auki wani ya cigaba da dubawa "a zahirin gsky babu kyau abinda kake mata ai ko babu komai ita din jininka ce, kaga koma meye a tskaninku bai dace ka dinga disgata irin haka ba .
an ji mu idan ka mana ba wani abu bane kasancewar mu din ba komai bane a wajenka, amman ita kamata yayi ka manta komai idan ma akwai abinda tayi maka ka jata ajikinka  "."ke wacece da zaki min wannan tmbyr ?" shiru tayi tsabar kunyar data mamaye ilahirin sansar jikinta Kmr ta nitse qasa haka taji  ".sai daya  gimtse ya murtuke fuska cikin tsare gira sannan ya sake maimaita mata tambayarsa "wacece ke tukunna  ?"shiru maryama tayi ta kasa cewa komai duk da tasan zai iya aikata abinda yafi haka .”

“cikin ni dake waye ya rike past dinsa ya kasa manta komai “?ke da kika kasa manta abinda ya wuce a rayuwarki zakizo kina fadawa mutane  nonsense and rubbish ".yayi mgnr yana tsareta  da tsumammun idanusnhi masu matukar firgitarwa .“cikin ni da ke waye ya rike past disa fad'a min da har zakice na manta komai na jata ajikina ?"zuwa wannan lokacin ranta a matukar bace take kallonsa har ya rufe bakinsa ". "daman kana sane da past dina ne ?tai masa tamabayar zuciyarta na wani irin tsinkewa .
yay shiru yana kallonta d'an bashi da amsa da zai bata "koma dai menene zaka iya bata  chance sir saboda soyayya tana bukatar kulawa kuma duk lalacewa kaso mai sonka sannan kayi amfani da damarka dan sultana na matukar sonka ." tana gama fad'ar haka  ta juya har tayi taku biyu ta jiyo  Amon muryarsa cikin yanayi na tashin hankali "wannna shine tunaninki "ta tsaya cak tare da juyowa tana dubansa kafin ahankali  ta qara taku biyu  ta yadda zai iya jinta sosai ".

“Bai wai shine tunanina ba, haka ne tana sonka kuma har ta furta hakan a yanzu wanda ni bansan sau adadi nawa tasha furta maka tana sonka ba amman dukkanin alamunta sun nuna .karka ga wai dan kana da kyau da kudi tare da nasaba kanemi ka wulakanta mutumin da ya damu da kai dan so .."are you still arguement with me?ya fad’a hk ta hanyar dakatar daita tayi shiru tana kallonsa taba jin wani irin mummunar fad'uwar gaba mai tsanani ."
Tana kallonsa cikin yanayin na jin kai ya mike ya tura kujerar da yake zaune akai baya kad'an ya fara taku zuwa inda take tsaye cikin tsananin tashin hankali taja baya da sauri jikinta na dan kyarma ya sake matsota sosai kamar zai rungumeta ajikinsa har suna iya jiyo bugun zukatansu cikin tsuma da karkarwa maryama  tasa hannuta d'aya ta tokare qirjinsa dashi ji tayi kamar ta daura hannunta a saman  dutse nan da nan ta  soma  furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ,hasbunallahu wani imal wakil acikin zuciyarta.”

cikin d'an d'aga murya ya soma magana "ai nasani nasan ke kadai ce zaki iya wannan karfin halin ina fad'a kina fad'a ba .?"jikinta yaji yana rawa a saman qirjinsa ,naunayen ajiyar zuciya ya sauke sannan ya soma ja da baya tare da dauke kwayar idanunshi akanta yana mata gargadi da idanunshi ya koma mazauninsa ya maida hankalinsa kan laptop dinsa muryarsa can kasan makoshi yace "ba laifinki bane   nasan dalilin dayasa kike min haka "me ka fad'a  sir ? I don't know kuma karki qara tamabayata ."yayi maganar yana sake gargadinta da kwayar idanunshi sannan ya sake kai idanunshi ga laptop."karkayiwa mgnr wata fassaran dabam ni dai kawai na baka shawara ne  dan ka gyara ina ma mata zasu kasance irina ?"dan ni bana daga cikin matan da zasu tsaya batawa kansu  lokaci  akan nmj ".

“really?
ya fad’a tare da dago kanshi yana dubanta  muryar a fusace "ke  da kika kasa manta mutumin daya mutu arayuwarki saboda son da kike masa shine zakice bakya daga cikin matan da suke iya bata lokacinsu akan nmj"? kenan ke din ba mace bace ? ko kuma ke din makaryaciya ."ta bud'e baki zata sake  magana taji sautin muryarsa yace "go ....."mutuwar tsaye tayi,ta saki baki tana dubansa har sanda ya sake cewa "I saida go back to your work." ta juya da sauri ta fara tafiya "kai mr ata mugun mutun ne ,a gaskiya sultana baki yiwa kanki adalci ba ko kuma nace zuciyarki ta cuceki irin wannan mutumin zaki so “? Kwata kwata mutun bai da fahimta  Jifa daga fad'a masa gaskiya ya hau kan mutun  yana qoqarin razana mutun har  yasa hanjin cikina ya fara  hautsenewa ta qarasa  fitowa  tana bugo masa kofar da karfi ."

Shi kuwa mr ata  tana fita wani irin dariya ne ya taso masa tun daga kasan zuciyarsa har zuwa kan lip's dinsa na kasa a zahiri ma kana iya hango hakan a tattare dashi dan kasa rike dariyar yayi "uhm tana cikin rukunin mata jarumai ,sannan karfin halinta na matukar burgesa most especially dakiya, gata da shegen tsoro amman tana qoqarin gurin dannewa ta fad'a min mgn son ranta lallai ba a banza zuciyata ta rasa sukuni akanta ba, daman kuma an halicceta ne dani ,duk abubuwa da yake mata yana  mata haka ne saboda ya auna gudun zuciyarta akanshi kuma ya gano adadin gudunsa da alamun nan kusa zuciyarta zata makance a soyayyarsa ,shi din kwararren dan kasuwa ne sannnan kuma kwararren mai gane shaukin só né a karon farko aka fad'a soyayyarsa tabbas zai gane duk da cewar tana da jarumta amman kuma akwai burbushin  tsoronsa da qaunarsa acikin kwayar idanunta "marayama kenan rigima zalla ko ina ruwanta da matsalar wata ?ban da rashin sani irin nata ina ita ina bawa wata damar ta so   abinda zata so daga baya ."

flaks cup din tea ya d'auka ya kai bakinsa yana kurba ahankali yana kallonta  tana kai kawo "me yasa ma na shiga harkar wannan mutumin taja tsaki tana rike kanta "wallahi yau ya gama bata min rai ta fad'a  a fili tana  furzar da iska mai zafi tana cigaba da sake neman number  "cikin saa aka dauka akace " hello  daga can bangaren "he..hello maryam ta furta cikin rawar murya bai bari tayi mgn ba ya cigaba da nashi mgnr "allah yasa  kece mai wayar nan ina ta kiranki kina tare da saurayinki ko mijinki ne ni dai bansani ba na fad’a miki kin yarda da  wayarki amman baki tsaya ba yanzu ina zanganki na baki wayarki maryama tayi shiru tana jinsa har sanda ya dasa aya ,kawai ta tsinci kanta da ce masa kana ina yanzu?" ta fadi haka ne saboda ta gano wanda ke damunta da kira yace"Ina nan Ikeja ta wajen jara shopping mall "wai muna da d'an nesa dan ina wajen aiki amman da ace daga gidanmu bamu da wani nisa amman ko zaka iya kawo min wayar wajen aikina sai na baka kudin mota har ma da qari ?"okay babu matsala a ina awajen aikinki yake ?."nan take maryama ta fad'a masa  sannan ta koma cikin office tana zance  zuciya.”

Bayan awa biyu mr ata ya shigo office din a natse gabadayansu suka natsu suna sauraran bayaninsa  bayani yake masu akan nan da sabon wata  zasu bar wannan kamfani zuwa wani dabam su cigaba da gudanar da aikinsu amman hankalin maryam naga kofar shigowa jira kawai take taga daya daga cikin securities yazo kiranta ,muryarsa a dake ya kira sunanta "maryam!  ta juyo da sauri tana dubansa tare da cewa "sorry sir! ya lumshe idanunshi ya cigaba da masu bayani still dai  ta sake maida hankalinta zuwa ga bakin kofa tana wasa da yatsun hannunta can sai ga d’aya daga cikin security   yace "wacece maryama hussein ? batare daya shigo ba bare yasan ko mr ATA yana gurin " nice !" ta fad'a da sauri ga wani can a waje yana neman ki ,okay na gode ta juya ta kalli mr ATA a tsanake tace "excuse me sir zan dan ga wani a kasa yanzu zan dawo "waye shi ?ya tmby ransa a matukar bace yana tsareta da kwayar idanunshi "wani ne!” ta bashi amsa atakaice "ba zaki koina ba ,ko bakiga abinda muke yi bane?na gani sir amman wannan kiran yana da matukar mahimanci “ta fad'a tare da wuce abunta .yayi  shiru yana binta da wani kallo mai tattare da zallar kishi ma’aikatan dake zaune a gurin babu wanda bai girgiza da abinda maryama tayi ba ."

Ayi hakuri dashi

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 28
Chapter 59 · 0% Book details