← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 111

Sashe 85

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A matuqar gajiye maryama ta shigo bangaren umma bakinta d’auke da sallama sai dai falon shiru babu alamun kowa dan ta shiga d’akin umma bata ganta ba ,sai dai jin alamun saukar ruwa abayi ta fahimci tana ciki ta fito ta shige d’akinta tai wanka tare da yin sallah bayan ta idan ta d’auki wani littafi tana dubawa sai dai ta kasa fahimtar komai ,dan madadin ta fahimci abinda ke cikin littafi sai ma ta shiga nazarin maganar madam some da kuma mganar mr ata da yayi mata a shekanjiya da kuma abinda ya faru a wannin da suka gabata “uhm !ta sauke numfashi da karfi tana cewa “madam some kenan gsky tunaninki akaina sam bai yi ba ta ina zan fara kai kaina cikin halaka ,ni ko sona mr ata yake koni na kamu da sonshi ai sai nasa wuka na raba tsakaninmu bare babu dayan biyu ta fad’a tana sauke numfashi tana zaune ta jiyo sautin muryar umma tana kiran sunanta “maryama! na’am umma ta amsa tare da fitowa ta sameta zaune a natse ta gaishe da umma yayinda umma ta riko hannun maryama tana dubanta kafin ahankali ta mike tsaye tare daita suka shige dakin umma , maryama ta zauna a bakin gado tana duban fuskar umma yayinda umman ta dawo kusa daita tana kallonta tare da dafata tana cewa “ya mai gidanki “yana lafiya da matsalo linsa , umma ban fad’a miki bane ya bawa kowa kyautar mota amman ni ya hanani amman ni bai dameni ba ina neman taimkon Allah ne umma tai shiru tana sauraron maryma har sanda ta dasa aya sannan tace “ amman dai gsky bai kyauta ba ,uhm umma manta da wannan mutumin kullmu maganrsa I don’t like bad behavior in this company ga tarin wulakantani da yake “.
“kawai fa taimako yayi min nayi qoqarin yi masa godiya amamn umma kinga uban wulakancin da mutumin nan yayi min sai kin tausaya min umma tai murmu shi irin nasu na manya kana tace “ai tunda yana iya taimako ai yana da kirki kad’an maryama ta yatsina fuska “ shifa abinda na fahimta yana da miskilanci tare da tarin wulaqanci kuma baya bukatar yayi maka abu kayi masa godiya”banda abunsa to meye acikin kayi ma mutun abu yayi maka godiya .”ni dai abinda zan fad’a miki shine kibi komai ahankali karki zake daywa ,idan mutun yana da irin wannan dabiar kana sanin yadda zaka tafiyar dashi ne,ki kula sosai kiyi duk abinda yake so kinji maryamata” naji umma in sha allahu na gode sosai yauwa diyar albarka allah yayi miki albarka ta amsa da “Ameen.

Mami ce zaune tare da yaranta mata uku aunty shahida,khadija da kuma zabiba yayinda mryam da nana hauwa’u ke zaune a d’akin sun kulle kansu suna zantawa,ahankali aunty shahida tace “alkubus fa kikace mami bayan tsawon shekaru “wallahi shahida ,ni kaina abu yayi matukar bani mamaki tun bayan rasuwar mahaifinku bai sake cinsa ba wanda hakan ya zamo silar da kowa ya daina cinsa acikin gidan nan kawai jiya bayan ya shigo yace shi zai ci nayi matukar mamaki .”gaskiya ne mami dole kiyi mamaki shekarun da yawa fa mami ta numfasa irin nasu na manya tace “kunsan wani abu ?”duk suka tsura mata ido suna sauraronta “ba kuyi tunanin wani abu akansa ba ?”atare suka girgiza mata kai me kike tunani akansa mami ?”inji cewar aunty khadija mami ta bud’e baki da zumar cigaba da magana sai ga ATA ya shigo yana qoqarin wucesu mami tace “yauwa ga adamcy din ma ya shigo ,ahankali ya tsaya yana dubansu “adamcy ka qaraso mana “yau ma nayi maka alkubus kuma nasan zakaji dadinsa fiyye dana jiya dan na jiya anyi aikinsa cikin sauri yau kam a natse akayisa .”

shiru yayi yana kallon fuskar mami dake kwance da tsananin farinciki “adamcy mami ka qaraso ka zauna mana” inji cewar aunty shahida still dai shiru yayi yana sauke numfashi gabad’aya suka tsura masa ido suna jin tsananin qaunar d’an uwansu, jiki a sanyaye ya soma taku sai dai hankalinsa da natsuwarsa baya gurinsu yana ga maryamarsa ahankali har ya qaraso zuwa inda suke inda aunty shahida ta kamo hannunsa ta zaunar dashi a kusa daita “wai kaci alkubus jiya ?”ka tuna da poverty din dady kenan khadija ko kin tuna lokacin da dady yake raye mami kusan kullum sai tai masa alkubus har compotetion ake gurin ci “murmushi aunty khadija tayi tana dubansa inda shi kam hankalinsa baya garesu cigaba da zantawa sukai cikin tsananin farinciki shi kam kasa cigaba da zama yayi acikinsu ya soma qoqarin mikewa adaidai lokacin da aunty shahida tace “a zubo mana muci tare dashi da sauri mami ta shiga kiran masu aikinta yayinda ahankali ATA ya yunkura da kyar ya mike ya haye samansa da idanu suka bishi gbdy yanayinsa ya sake canzawa ba kamar yadda yake abaya ba .”

yana shiga parlour’nsa ya zauna zagwab akan kujerar tare da yin shiru yana zurfafa tunaninsa “ mai yasa zuciyata zata min haka?” bazan ta’ba yarda zuciyata ta kamu da wata soyayya ba. numfashi ya sauke da qarfi yana hura hanci ya rasa dalilin da yasa maganarta ta tsaya masa arai kuma take masa ciwo .ahankali ya kai hannunsa ya ciro flower data siyo masa yana kallon yana jin wani irin tuttukin bakinciki mai had’e da shaukin qaunarta “
yana cikin wannan halin mami ta shigo parlour’n tana kiran sunansa “adamcy nah !kiran sunansa da mami tayi ne ya dawo dashi cikin haiyacinsa yayi sauri ya maida flower ya boye yana dubanta a tsanake “muna cikin tsananin farinciki daka dawo mana da cimar mahaifinka cikin ahlinmu “shiru yayi kawai yana kallonta kafin ahankali mami ta kamo hannun sa cikin nata taso muje kaci acikin yanuwanka bai mata mutsu ba sai dai ya zare hannunsa ya cire yar saman suit dinsa da niktie ya biyota har zuwa parlour’n kasa inda yan’uwansa ke zaune “ta zaunar dashi a tsakiyarsu bai wani ci mai yawa ba ya sake mikewa mami ta kallesa a natse har kayi me “sweetheart kinsani bana son cin abinci mai nauyi jiya ma dai naci ne yana gama fad’ar haka ya haye sama .”

Da misalin qarfe tara na dare da mintuna ashirin a natse ata yake saukowa parlour’n mami wanda yake d’auke da motsin mami dake waya tun kafin ya qaraso ya fahimci yan’uwnasa sun kama gabansu “wannan shawarar taku bazan ce batayi ba ,amman sanin kanki ne zulfa’u kinsan halin d’an naki da ra’ayin kanshi shi din ba kamar kowa bane ,har yanzu ban gama da matslar maryam ba .”wallahi koni abinda yake cikin raina kenan dan zamansa haka ya fara damuna..”guri ya samu ya zauna ya kasa kunnuwansa yana sauraron mami cikin natsuwa wanda zamansa ita ta katse hirar ammi ,ta zuba masa idanun wanta gabad’aya wanda hakan ya tabbatar masa da maganar sa suke cike “sweetheart!”ta zuba masa ido kawai tana saurarensa “ina tunanin next two weeks in sha Allahu nake son na wuce zuwa uk akwai sababin desing da wasu companies ke so na sabuwar shekara akan qarafe manyan motoci daman kuma na baro aikin da dadewa amman ina ganin zani domin a qarasa komai “:Kai kawai mami ke gyada masa cike da alfahari da kuma farinciki irin gwazon da Allah ya bawa d’aya tilo da take dashi Masha Allah Allah yayi maka albarka Allah ya tai maka suna zaune suka jiyo sallamar sultana cike da jin kai .mami ta sauke numfashi tana dubanta cike da tsananin kulawa dan ita kowa nata ne tace “sultana kece a daren nan?”wallahi nice mami ,ta qaraso ta samu waje kusa da ata ta zauna sannan ta gaishe da mami .”

Mami ta amsa tana tamabyarta abida “tana lafiya ta ma ce na gaisheki ina amsawa ya aikin da fatan dai kina jin dadin aiki da yayanki ?”mami ta fad’a tana murmushi “to babu laifi ta fad’a tana dubansa wanda shi ko kallonta bai yi ba dan idanunshi ma na kan tv yana kallon labarai ganin irin kallon da take masa yasa mami ta mike tace “bari na shiga ciki dan da alamun wajen yayanki kikazo?”murmushi sultana tayi .”bayan mami ta shige ciki ta iske maryam tsaye “akwai abinda kike bukata ne ?”maryam ta Kai hannu tana shafa kitson kanta tare da yatsuna fuska “babu abinda take bukata tana dai son ta fita taga muradin zuciyarta ne ganinsa ya fiyye mata komai dake cikin duniyar nan “kinyi shiru maryam !mami ta sake mata magana da kulawa “wai Ina son na sha custard ne “okay bari na kira tabawa tayi miki barta kawai mami zanyi da kaina ta fad’a tana qoqarin ficewa numfashi kawai mami ta sauke .”

tun daga nesa maryam ta hango sultana durkushe a gaban adam dinta tana masa magana gabanta ne yayi wani irin fad’uwa har sai da yar cikinta ta motsa,da sauri ta matso daf dasu ta tsaya adaidai lokacin da sultana ta cigaba da magana “ya adam ina sonka kamar yadda ka sani bansan yadda zanyi da rayuwata ba dan idan ma nace zan hakura da kai tabbas nayiwa kaina karya “nan take maryam ta tsinci kanta da zubar da hawaye tana qoqarin maganin sabuwar maseefar data kunno Kai cikin rayuwarta ga wata maseefar da me zataji? ta furta a fili jikinta na rawa ,yayinda ata yayi shiru yana sauraron sultana shi har kullum yana mamaki matan dake da qarfin zuciyar fad’awa nmj suna son shi “ wallahi da dai na rasaka gara na rasa rayuwata dan zan iya kashe kaina .”Idanunshi ya zuba mata kafin ahankali ya fara magana cikin zafin rai “ ke wai ni sa’an wasanku ne”? yayi maganar cikin tsananin fushi”tunda bazaki iya rayuwa babu ni ba to kije ki kashe kanki dan ko matan duniya sun qare sanin kanki ne ni adam bazan ta’ba kasancewa miji gareki ba ki tashi ki wuce abinda yafi mutuwa ma kije kiyi wannan ba damuwata bace.”
Chapter 85 · 0% Book details