← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 111

Sashe 18

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta dago daga abinda take tare da mikewa tsaye tana kallon farar takardar dake Kan table “a haka ne kike cika baki kin iya har da zaa yi alfahari dake this is totally nonsense “ ya fad’a yana jan tsaki .”sir a naka ganin zaka iya ganin kamar bai yi ba, amman mai zai hana ka bari na kammala tukun sai kasan matsayin da zaka bashi “nace abu bai min ba kina agurment dani ?yayi mgnr adaidai lokacin da sectary dinsa ta qaraso ta tsaya a bakin kofa cikin tsananin tashin hankali.”sir wannan ai ba argument bane bayani nayi maka sai magana ta gaba ai sai daka tabbatar da kwarewata kafin kasa a nemo ni kuma ina tabbatar maka babu kamfanin da zaa kai zanena su kushe suce bai yi ba ,duk wanda kaga ya kushe zanena to hassada ce .” ta fad’a tana kallon cikin kwayar idanunshi kallo daya zaka mata ka fahimci ranta a ‘bace yake “ taya na kwantar da hankalina domin nayi maka abinda ya dace amman tun ban kammala ba ka fara zariya kana kushe min aiki amman idan kana ganin akwai wanda zai maka fiyye da nawa a kamfanin nan kana iya bashi yayi maka
ko da yake babu wanda zai iya shiyasa ka..”hussein maryama! taji an kira sunanta bata juya ba dan tasan ko wacece “how dare you argument with sir ?

“No ma ba argument bane ina dai fad’a masa abinda ya zamo gaskiya ne kawai taya tun ban qare aiki ba yazo ya tsaya min yace bai yi masa kyau ba this is totally nonsense .” ta fad’a tana hura masa hanci qirjinsa ne yayi wani irin bugawa da karfin gaske ya dinga jin kamar ana tsira masa allura a duk wata jijiya dake sansar jikinsa “tunda ya kafa mata tsumammun idanunshi bai dauke ba har sanda ta dasa aya gabadaya tsoro tattare da matsanancin firgici ya kama sectary dan bata ta’ba ganin wanda yayiwa sir haka ba yana magana ana maida masa cikin fad’a wannan shine karo na farko “kallo biyu ma baka isa kayi masa ba bare jayayya ta magana dashi .office din ya dauki shiru baka jin motsin komai sai na bugun zuciyar mutun uku mr ata , some da maryama “shikenan ki cigaba zanga karshenki ya fad’a yana kokarin juyawa tace “sir ina ganin ma zan wuce gida yanzu dan akwai abinda zanyi .”da sauri ya juyo yana dubanta a tsanake Kmr zai cinyeta,in sha allahu zan kammala zuwa gobe, sannan ka rike min takardata ko zan iya kar’ba? shiru ne ya biyo baya, ganin hk yasa maryama ta kwace takadarta daya rike yake kokarin fita dashi ta saka cikin jaka ta ra’ba ta gefensa ta kama gabanta ta barshi tsaye da mamakinta har ta kai bakin kofar fita ta tsaya batare data juyo ba “karka damu sir I wil make sure a submit the design tomorrow by 7 dot .”ta wuce ta barshi tsaye yabi bayanta da kallo yana jin wani irin quna lallai akwai aiki agabansa ya fad’a acikin zuciyarsa sectary ta matso kusa dashi “sir kayi hakuri I will talk to her zata canja lumshe idanu kawai yayi ya koma zuwa office dinsa wani zufa na karyo masa
💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 8

Mutuwar tsaye mr ata yayi a wajen yana cigaba da kallon  hanyar da maryama tabi ,duk yadda yaso ya kai ga son motsa sansar jikinsa ko ya  bar office  din zuwa nasa ko ya tsaidaita amman ya kasa  saboda  tsananin firgicin abinda tayi masa . "hakika ya yarda ya kuma amince wa zuciyrasa ya sadaukar wani mummunar abu na shirin faruwa dashi ,ko kuma yace alqadarinsa yazo qarshe akan maryama ." soyayyarta da yake tason boye mata take son lallai sai ya fito daita sarari kowa acikin ma'aikatar ya san da zamanta wanda shi sam babu tsarin haka a ra'ayinsa yafi son sai ya shigar da soyayyarsa cikin zuciyarta ta yadda  itama zata kamu da tsananin soyayyarsa sannan ma duk abinda zai faru ya faru ."

ji yake kamar yayi kukan abinda tayi masa a yanzu a gaban some. sosai zuciyrasa ke masa zafi da qunci gashi baya son tozartata sannan baya son ta janyo masa raini a wajen sauran ma'aikatansa ."kusa dashi some ta matso kad'an tace "sir kayi hakuri dan Allah "wani zazzafan numfashi ya sauke tare da naunayen ajiyar zuciya sannan muryarsa a tsarke ta fito tamkar mai koyon magana yace "karki bari maryama ta wuce gida kiyi maza ki  tsaidaita   lallai ki dawo tare daita ". some tayi matukar jin mamakin abinda ya fito daga bakinsa dan a tunaninta kalmar dakatarwa ce zata fito daga bakinsa amman sai  taji sa'banin haka ,dan haka bata  tsaya cigaba da jin mamakinsa ba cike da hanzari ta furta "okay sir sannan  ta fice da sauri tamkar zata hantsila yayinda maryama tuni ta sauka qasan ma'aikata tana  d'aga qafafunta a natse sai dai kallo d'aya zaka mata ka fahimci ranta a matukar 'bace yake dan wani irin tafasa zuciyarta ke yi."

ahankali tasa kai ta shiga cikin ma'aikatan dake  qoqarin fita daga cikin ma'aikatar sai ga some ta sauko tana ihun kiran sunanta "maryma! mryma !! sarai maryama ta jita amman tayi mata banza taki juyowa bare ma tayi tunanin zata tsaya ta saurareta kanta a kasa ta qarasa ficewa "securities karku bari yarinyar ce mai doguwar riga ta fita ku tsaidaita min ku tsaidaita !!sai dai ina tuni koda suka je tsaidaita tuni maryama ta tsaida mai adaidaita ta shige tana bashi umarnin su wuce ."
cikin tsanani tashin hankali some ta rike kugunta tana kallon bayan motar da maryama ta shiga yayinda hankalinta na qara tashi dan bata san yadda zata fuskanci mr ata ba ."tsabar mamakin maryama yaki barin zuciyarta bata san rashin mutuncinta har ya kai haka ba ,mr ata din zata dinga sa'insa dashi."? "Mai take taka dashi ?shiru tayi na second biyu kafin daga bisani ta girgiza kai ta fara tana zance zuci "anya ma kuwa babu wata a qasa ?sosai ta dinga tariyo irin kallon da mr ata din yake bin maryama din dashi  a d'an tsakankanin wannan lokacin  saurin kawar da tunaninta tayi domin tana jin hakan ba mai yuwa bane mr ata bazai ta'ba kamuwa da son maryama ba, wasu irin mata ne bai gani ba a rayuwarsa, bai kamu da soyayarsu ba sai wata maryama ."

bangaren mr ata kuwa cikin tsantsar 'bacin rai ya nufi office dinsa gabdaya duniya ta chakud'e masa waje d'aya jira kawai yake some ta dawo masa da maryama ya samu yayi mata ko mari d'aya ne  ya d'an huce abinda tayi masa zai d'auki komai amman ban da raini .  ahankali ya fara zariya acikin office din kwakwaluwarsa na sake tariyo masa magan ganun mryma sosai zuciyrsa ta dinga motsawa ."
da sauri some ta biyo bayansa zuwa office dinsa kamar wacce aka jefo haka ta shiga office din  cikin tsananin tashin hankali ta kame nisa kad'an dashi tana had'e hannuwanta waje d'aya yayinda zuciyarta ke cike  da matsanancin tsoro da fargaba ,magana take son yi amman ta rasa ta inda zata fara dan tasan  shi kamar yunwar cikinta kad'an daga halinsa sai ya huce akanta."

"ina ma hakan zai faru da zai fiyye mata sauki akan action din da zai iya d'auka dan tasan ita kanta ba tsira zatayi ba tunda fushinsa ba iya kan wanda yayi laifi kad'ai yake tsayawa ba ."zariya ya cigaba da yi tamkar wanda yayiwa sarki karya yana sake aunawa kwakwaluwarsa maganr mryama .daga kalmominta ya gane komai fa ya sauya agaresa yanzu ne zai gane shi din ba komai bane dan bai isa ya dakatar daita aiki ba kamar yadda ya saba yiwa sauran worker's dinsa  sai daí bazai barta haka batare daya hukuntata ba dan dole ma ya ganar daita kurenta ko dan gaba anya kuwa adam zaka iya d'aukar mataki akan maryama "?yayiwa kanshi tamabyar yana mai juyowa."

cak ya tsaya sakamakon ganin some tsaye a bayansa dan bai san da shigowarta ba aikuwa ya  kafeta da tsumammun idanunshi  tamkar itace tayi masa laifi , haka nan taji gabanta yayi wani irin mummunar fad'uwa da sauri ta soma magana  cike da in inna "sir.."!sir !!  kayi hakuri ban samu damar tsaidaita ba amman ka barta dani  hakika zan bari tayi datasani abinda tayi maka , ina ganin ma wannan shine karonta na qarshe da zata tako cikin ma'aikatan nan da sunan aiki ,dan ko zamu d'auki komai bazamu d'auki wulakancinta ba we can't take it any more cikin tashin hankali da tsoro take magana ." wani banzan kallo yayi mata mai tattare da jin tashin hankali mara misaltuwa wanda yasa take some tayi shiru cike da girmamawa tana dubansa ".

da sanyin jiki yake qarasowa inda take tsaye hannuwansa duka ya zura cikin aljihunsa wondonsa yana qare mata kallo atsanake  wanda shi a zahiri ba ita yake kallo ba fuskar maryama ce ke masa yawo acikin kwayar idanunshi ."kusan minti goma ya d'auka  yana kallonta sannan yaja wani dogon tsaki lokacin daya fahimci halin daya shiga ya  koma mazauninsa ya zauna yana sauke wani wahallalen numfashi sannan  a natse ya d'auki wani file ya rike kawai ba dan yin aiki akansa ba, gabad'aya ya rasa me zai yi ya huce  "sir kayi hakuri  zan rubuta mata takardar dakatarwa? ta fad'a tare da juyawa ta nufi kofar fita da sauri "wa ya baki damar aikata hakan ?."ta jiyo sautin muryarsa cikin tsananin fushi .cak ta tsaya tare da juyowa ta zuba masa idanunta tana mamakin jin abinda ya fito daga bakinsa ,sai dai  idanunshi na kan kallon file din dake rike a hannunsa ,sam  bazakace shine  mutumin da yayi maganar ba ".
Chapter 18 · 0% Book details