← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 111

Sashe 31

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mutumin data mikawa wayar shima dai cewa yayi bai gansa ba hasalima bai ma ta'ba ganin mai kama dashi ba" yana gama fad'ar haka ya mika mata wayar ya shige ya barta tsaye cikin tsananin tashin hankali ita kanta tasan mafarki ba gaskiya bane amman mai yasa zata damu kanta akan mafarki ?"saboda zuciyarki ta kasa hakura da cewar yaya sadam ya mutu ne"ta bawa kanta amsa da haka tana dafe foring head dinta tana cire wayarta a flight mode ." Inda mr ata yake can cikin tsananin damuwa sosai ,a natse ya fito daga office dinsa rike da wayar da yake ta faman neman layin maryama yana bin kowa da wani iri kallo, yayinda kallo daya zaka masa ka tabbatar da cewar baya cikin nutsuwa da walwalarsa duk da daman ba mai sakin fuska bane amman na yau din yafi na sauran lokuta nunawa ."yana cikin wannan halin ya samu kiran gaugawa daga Z&A dan haka ya kalli agogon dake d'aure da tsintsiyar hannunsa shabiyu daidai yanzu ta buga bai koma office dinsa ba ya zarce zuwa qasa direbansa a ruwa da escout dinsa suna ganin fitowarsa duk suka zabura suka mike da sauri aka bud'e masa gidan baya ya shiga ya zauna yana jin wani irin mummunar fad'uwar gaba hannunsa ya kai gwiwar qafarsa yana kad'a qafarsa d'aya yana tunaninta."

tafiyar mintuna ta kawosu Z&A" sanda direba  escort dinsa yayi parking atare escout dinsa suka firfito gbdyansu rike da bindiga suka  zagayesa inda direbansa a ruwa ya fito da sauri ya bud'e masa kofa ya fito ya nufi ciki har anan ma an fahimci tsananin damuwar da yake ciki ."har yaje ya dawo damuwarsa na nan sai ma ninkuwa da tayi ko cikin kamafanin ranar kowa yasan lallai akwai abinda ke damunsa dan haka kowa ya qara shiga hankalin sa, tun daya hawo saman bai ga alamun maryama ba gabansa ya cigaba dukan tara tara amman ya dake ya samu waje ya zauna ya soma gabatar da ayyukan dake zube akan makeken table dinsa yana mamakin rashin ganinta ."bayan kamar awa biyu da shigowarsa office ya sake duba agogon hannunsa yaga lokaci ya soma tafiya amman babu alamun shigowarta ."
ahankali ya mike ya tura hannunsa d'aya cikin aljihun wondonsa yana taku acikin office din duk wani motsi da zai ji sai ya saita idanushi kan glass door kasancewar ana iya hango duk wanda ya shigo amman sai yaga ba ita bace ,nan fa natsuwarsa ta qara barin gangar jikinsa ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai kawo yake daga cikin office dinsa zuwa wajen office dinsa zuwa office dinsu maryama kunnensa manne da waya yana faman neman numberta tare da sake duba ogagon dake d'aure da tsintsiyar hannunsa sauran mintuna talatin wad'an da zasu zo suga representaition dinsu su qaraso ."

daga sectary dinsa har sauran abokan aikin maryama hankalinsu a matukar tashe yake sakamakon yanayin da mr ATA yake ciki ,".yana tsaye sectary ta qaraso da hanzarinta ta tsaya kusa dashi cike da girmamawa idanunshi ya tsura mata yana son yaji mai zatace masa "sir har yanzu bata qaraso ba dan allah kayi hakuri sir gashi Ina ta kiranta bata d'aga kiran ya lumshe tsumammun idanunshi dan shima layinta yake kira tana shiga bata d'agawa fuskarshi a had'e ya tsare some da kwayar idanunshi kafin a hankali ya motsa labbansa "ina yarinyar data bawa zanen jiya ?" da sauri some tayi baya kad'an ta soma kiran yusura batare da 'bata lokaci ba yusura ta fito daga office dinsu ta bayyana a gabansu cike da girmamawa tana gaishesu idanuwansa masu matuqar tsoratarwa suka sauka akanta gabad'aya yusura ta rud'e "kinyi waya da maryama yau ?"no sir !ta bashi amsa a rude ".

"kirata ko zata d'auka jikinta na rawa ta soma neman layinta"kisa wayar a handsfree "okay sir tayi kamar yadda ya buqata sai dai tana kira ta d'aga muryarta a tsarke tace  "yusura !" maryama kina ina ?"da sauri mr ata ya fixge wayar ya soma magana cikin zafin rai "ke kina ne ?"kit yaji ta kashe wayar gbdy "oh shit ya furta yana dafe goshinsa yana fesar da iska mai zafi daga bakinsa yana jan tsaki byn second biyar ya sake tsare yusura da ido "akwai wanda zaki kira a gidansu yanzu domin muji halin da take ciki ?"tayi saurin gyad'a masa kai alamun eh !zufa na karyo mata "ok call !ya fad'a atakaice yana juya bayansa nan da nan ta soma kiran layin umma kira d'aya biyu umma ta d'aga byn sun gaisa ta tmbyeta maryama fa "?ai ta fita tun da sassafe lafiya yusura?"babu komai har yanzu bata qaraso office ba "zata qaraso in sha allahu dan tun sassafe ta bar gidan nan "okay to .ta fad'a tana gyad'a kai cike da tashin hankali ya wucesu zuwa cikin office dinsa da niyyar zama sai dai ya kasa zama bai sani ba tashin hankalin na meye haka na wanda zai zo ne ko kuwa na bai san dalilin rashin zuwan maryama  aiki bane ko yace mai tsaidaita ?."

sectary ta biyo shi tana kwantar masa da hankali akan zata zo may be hodop ne ya riketa tunda ance tun da sassafe ta bar gida ya kalli agogon hannunsa a d'age yana cewa " wani irin hodop ne wannan har biyu saura ?yayiwa zuciyarsa tmby," ganin har kusan karfe uku bata shigo ba ya d'auki wayarsa ya shiga neman chief emeka yana kiransa ya d'auka yana cewa "shigowar mu kenan yanzu nake shirin kiranka muna qasa ka turo a hawo damu sama shiru mr ata yayi ya kasa magana yana tunanin me zai ce masa "kayi shiru ko akwai matsala ne ?uhm bari dai a shigo daku "some !"yes sir kisa a shigo da cheeif emeka ita kanta sai data ji mummunar fad'uwar gaba ta fita da hanzari zuwa inda suke ta gasiehesu cike da girmamawa sannna tace su biyota madadin suga an wuce dasu conference hall sai suka ga an nufi office din mr ATA dasu ."

"Have a set !"suka zauna me za'a kawo maku coffee ko juice "?any one !suka bata amsa ta juya da sauri ta fita, hannu mr ATA ya mika masu suka gaisa d'aya bayan d'aya sannna suka fara zantawa akan abinda ya kawosu some ta shigo ta ajiye musu juice ta samu guri ta tsaya kusa da mr ATA."shiru office din ya d'auka baka jin motsin komai sai na saukar numfashinsu har kusan mintuna talatin babu alamun za'a gabatar masu da komai cheeif ameka ya soma mgn "ya kamata ace munyi abinda ya kawomu ".mr ATA ya shafa fuskarsa wannna shine karo na farko da zai nemi wani abu akan wani bil Adam "kayi shiru bayan kasan daga inda muke ?

"Ku dan jira kad'an wacce take aikin akan designs din ne bata samu qarasowa ba amman nasan zata qaraso zuwa nan da mintuna talati "tsaki chef emeka yaja da karfi yana cewa "wannna wani irin kasuwanci ne haka ?"kasan baka kammala aiki ba ka bari muka 'bata lokaci muka zo" ya fad'a yana mikewa tsaye shima mutumin da sukazo tare ya mike da hanzari what can of nonsense is this cheeif emeka ya soma zuba ruwan bala'i ta inda yake shiga bata nan yake fita ba sectary na basu hakuri da qokarin shawo kansu amman suka ki"

Cikin haka taji sautin muryar ata a kausashe "some stop beging them" ya fad'a yana mikewa tsaye ya zagayo daga mazauninsa basu dakatar dashi ba har ya fita ya bar masu office din ."Ko bayan fitarsa hakuri sectary take basu da kyar suka wuce yana ganin wucewarsu ya dawo ya zauna akan kujera yana juyi tare da jin zafin wulakancin da maryama ta janyo masa wanda tunda yake baa ta'ba daga masa murya a office dinsa ba sai yau ."shiru yay yana dogon tunanin abinda ya hanata zuwa wani tunani yayi ya mike zambur ya fito zuwa kasa direbansa na ganinsa ya mike da sauri haka masu tsaronsa sai dai ya datakar dasu ya shiga gida baya direbansa ya maida kofar ya rufe sannan ya zagaya da sauri ya bude gidan gaba ya shiga yana mai tada motar ."

Sai da suka hau Kan titi sosai yace "sir ina muka nufa agege" ya furta yana jan tsaki tunda ya fadi haka bai sake cewa komai ba har suka hau Kan titin da zai kawo mutun zuwa agege direba ya sake tambaya unguwar dasu dake map yake dubawa ".
"Market street"! sunan unguwar ya fad'a a hankali direbansa ya karya kwana zuwa unguwar sai dai inda matsalar take bai san gidansu ba direba ya d'an samu guri ya tsaya yayi parking a gefen titi "sir gamu a market street shiru yayi yana cizan lips dinsa kusan mintuna talatin yana tunanin ta ina zai fara neman gidansu "yarinyar da tabawa zane ce ta fado masa kamata yayi ya taho daita ! some ya soma qoqarin kira,kira  daya d'auka tana cewa "sir !"Ki tmbyr min yarinyar nan meye number gidansu maryama ?some tayi shiru cike da mamaki can tayi sauri ta shiga office dinsu yusura kafin ya fara mata maseefa sai dai wayam bata ga yusura ba nan da nan hankalinta ya tashi "sir banga yarinyar ba "gashi nima bansani ba dan James bai ta'ba fad'a min ba kawai dai unguwarsu ya fad'a da sunan maai..."call James ki tmbyesa yanzu karku 'bata min lokaci tace "okay sir ta shiga neman layin James ya d'auka "meye number address din yarinyar nan maryama ?dafe goshinsa yayi dan ya manta amman gidansu bai da bace ana shiga unguwar Kwanar farko gida na d'aya zuwa na biyar zasu ga gida mai kwarababben get baki nan ne gidan "okay tayi saurin discouting din kiran ta sake kiran Mr ATA ."
Chapter 31 · 0% Book details