← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 111

Sashe 42

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma ta sauke wani ajiyar zuciya tana damke hannun maryama cikin nata cikin muryar kuka ta soma magana “ba akan sadam bane maryama”to akan menene haka umma kike min asarar hawayenki ?”ina jin araina kamar wata rana zaki gujeni alhalin bani da kowa daga Allah sai ke maryama zuciyata tana tsananin qaunarki maryama rashin sadam ya tabani matuka amman rashin ki shi zai fi komai damuna “numfashi da naunayen ajiyar zuciya maryama ta sauke sannan ta yunkura ta mike ta zauna kusa da umma tana goge mata hawaye tana cewa “a gsky umma baki ta’ba min abinda ya ‘bata min rai ba irin wannnan lokacin ba domin baki d’aukeni kamar yadda na d’aukeki ba nan take umma ta soma girgiza mata kai “umma nifa yar halak ce kuma nasan hallaci kuma zuciyata tana qaunarki fiyye da tunaninki bana tunanin akwai wata ranar da ni maryama zan juya miki baya ba duk runtse duk wuya umma nah tare ban ta’ba jin cewar bakece kika kawoni duniya ba zan kasance dake muddin rai mutuwa ce kawai zata rabamu dan Allah ki daina wannan tunanin ki daina tunanin zan gujeki ni amarki ce haka kema amanata ce ta qarasa maganar tana zubar da hawaye .”

Umma ta rungume maryama ajikinta umma kuka maryama kuka aka rasa wanda zai rarrashi wani acikinsu sai dai har ga allah umma ta samu natsuwar zuciya domin bata son abinda zai nisantata da maryama idan ba aure bane .kuma a kullum tana mata fatan samun miji na gari sun d’auki sama da mintuna talatin suna kuka sannna umma ta soma shafa bayanta tana cewa “kukan ya isa haka maryama kiyi min afuwa yau ummanki ta sakaki kuka sheahekan kuka kawai maryama take tana narkewa ajikin umma “dan allah umma ki daina wannan tunanin aranki “in sha allahu maryama bazan sake ba kuma na gode matuka da qaunarki allah ya barmu tare allah yayiwa rayuwarki albarka Allah ya azurtaki da samun miji na gari wanda zai kular min dake ya kuma rike minke amana addua sosai umma tayita mata tana shafa bayanta har maryama ta samu natsuwa .”

Parlour’n ya d’auki shiru har na tsawon minti goma sannna umma tace “tashi muje ki kwanta gobe zaki office ta fad’a tana mikewa tare daita ajikinta ta d’aukar mata jakar aikinta da d’ayan hannunta suka nufi d’akin maryama umma na sake kwantar wa maryama da hankali ,ta ajiye mata jakar akan table sannna ta kwantar daita akan katifa ta zauna a gefenta tana tofe mata jiki da addaua tana cigaba da shafa bayanta tamakar wata yarinya qarama maryama tace, umma kije ki kwanta ki huta kema “to maryama sai da safe, Allah ya tashemu lafiya ta mike ta fito ta shiga dakinta ta hau Kan gadonta ta kwanta “.bayn fitar umma da kusan awa uku amman maryama ta kasa bacci sai faman juyi take kwance ta mike zaune ta duba wayarta taga lokaci ya wuce sosai dan d’aya ta kusa jin idanuwanta basa jin bacci ta janyo jakar aikinta ta cigaba da aikinta ahankali ahankali ta dinga jin kamar motsin shigowar mutun tayi tsam da ranta tare da dakatar da aikin da take na wani lokaci ta kasa cigaba aikinta ta kasa kunneta sosai  ko zata ji takun tafiyar mutun  sai dai bataji komai ba har tsawon wasu mintuna dan haka ta maida hankalinta kan takardar gabanta ta cigaba da aikinta .sai dai haka nan ta dinga  jin zuciyarta na tsinkewa tare da jin mummunar faduwar gaba  .”

domin ta samarwar zuciyarta natsuwa ta ajiye takardar dake Kan pillow  ta yunkura ta tashi ta sauko daga Kan gado ta soma tafiya a hankali cikin sand'a har ta fito zuwa babban falon gidan ta tsaya shiru tana kallon koina ta  cikin hasken da bai gama haskaka falon ba, ta kai idanunta ga kofar shigowa taga kofar a kulle take dan haka ta sauke numfashi ta koma ta cigaba da aikinta bayan wasu lokaci ta soma jin bacci dan da kyar take iya bude idanunta tashi tayi tana hamma tare da cewa " gashi  ina tsananin jin bacci gashi banga ma aikin  dake gabana ba ."
ta fito zuwa falo ta nufi kitchen ta dauko dan qaramin prepand mai zurfi ta zuba ruwa kadan dan tea take bukata ta daura akan gas ta kunna ta tsaya har sai da ruwan yayi zafi  ta hada tea ta zuba a cup ta fito tana sha a ahankali ..qarar faduwar abu taji ta daidai bangaren d’akin yaya sadam ta tsaya cak tason ta qara ji amman shiru .”

sai dai batayi tunanin komawa dakinta ba ta  fara tafiya a hankali zata dakin inda taji motsin qarar faduwar abu har tayi taku biyu  sai kafarta tayi tuntube da takalmin aunty hassna ta sauke numfashi sannan ta tsuguna ta dauka tana cewa "bansa sai yaushe aunty hasana zata daina shigowa da takalmi har parlour' ba, idan ya zama dole ai akwai takalmin yawo a parlour ba irin wannan ba da zai cire maka farce , takalmi  Kmr katako gashi abun haushin ma sai tazo da takalmi amman idan ta tashi wucewa ta sai ta barshi ta kama gabanta haka .ta qarasa inda suke ajiye takalma ta ajiye nan  ya kamata da irin wadan takalmar wannan abu ya dauki hankalinta yasa bata shiga dakin ba ta  koma dakinta ta zauna  ta tankwashe kafafaunta ta dauki takarda wayarta taji ta dauki qara ta lalubo wayar ta manna a kunnenta"okay yusura nima ina Kan aiki bazan kwanata ba sai na kammala byn ta kammala ta ajiye wayar wani kiran ya shigo taja tsaki waye kuma adaidai wannnan lokacin ? ta lalubo ta dauka tana duba number bata san number ba kamar bazata dauka amman sai tayi tunanin ko emergency call ne  ta dauka tana cewa "hello !

Daga can bangaren taji ance "maryama hussein ce maaikaciyar AGC company “yes sir okay gobe muna bukatar ganinki a kamfanin da misalin karfe bakwai daidai ana gama fadar haka akayi discounting din kiran tayi shiru tana tunanin wanda ya kirata wannan dai ba muryar mr ATA bane ta lumshe idanunta tana cewa babu mamaki ko cikin yan'uwansa ne wani Ke bukatar yin aiki daita dan haka bata sake yunkurin tashi ba gara ta qarasa kafin wani aiki ya shigo mata gobe tana hamma tana aiki har ta qarasa ta kwanta   da zumar tayi bacci amman ta  kasa runtsawa har aka kira sallah ko byn daaka idar ma bata iya komawa ba dan haka ta yi wanka tayi shirin zuwa aiki ."Karfe bakwai daidai a AGC company tayi mata koda ta shigo ma'aikatan babu wasu mutane sai tsirarrun mutane dake kai kawo da securities da masu share maaikata ta kama hanya zuwa sama nan ma dai bbu kowa koina shiru kai tsaye office dinsu ta shiga tana sauke numfashi ta cire jakar kafadarta ta ajiye akan table ta ciro takardun zanenta tana dubawa ta sake duba agogon hannuta  .”

“gsky yau nazo da wuri sosai ko da yake  na huta da complain din madam some kullum sai tayi complain akaina to gashi itama bata zo ba tukun.” ta fad'a tana  sauke numfashi tare da tuna yadda take mata idan tazo late "Mis maryama hussein why are you always late ?ta fada da irin muryarta ?tana lumshe idanunta  tare da saka hannunta cikin aljihun doguwar rigar dake jikinta yayinda hannunta daya ke tokare da table din gabanta exactly yadda mr ata shi kuma yake yi har da qara taku biyu ta tsaya Kmr yadda yake yi .murmushi ya bayyana akan fuskarta sakamakon tuno mr ata datayi tana jin wani iri ajiknta shi kuma matsalarsa always complain “baki daukar aikinki da mahimanci a tunaninki ke din professional ce bana bukatar mutane da basa daukar aikinsu da daraja kullum bakya son zuwa aiki da wuri , kullum da excuse din da kike kawao wata rana zan dakatar dake aiki ta fada a fili .kamar ance ta juya bayanta tana juyo kawai taga mutun tsaye ya jingina jikinsa da kofar shigowa idanunsa kyam akanta  sanye cikin kanana kaya irin shigar jiya sak yayi sai dai kalar kayan dabam yana rike da farin glass dinsa,yayinda hannunsa daya na soke cikin aljihun wondonsa kmr koda yaushe yayi shiru yana jifan da wani irin mayataccen kallo mai tsantsar kashe sansar jiki .”

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 20

  A matukar rikice ta juya tana mai   had'e hannu wanta waje d'aya tana jin wani irin mummunar fad'uwar gaba  mai tsanani "gabad'aya yanayinsa yayi matuqar tsoratata. a bangaren mr ata kuwa wani sanyi dadi ne ya mamaye sansar jikinsa sakamakon d'aura kwayar idanunshi da yayi  akan sanyi idaniyansa da sanyi safiyar nan , wani tunani maryama tayi wanda yasa ta juyo da sauri tayi taku biyu ta tsaya kusa dashi muryarta na rawa tace "good morning sir"! bai amsa mata ba ya qarasa shigowa cikin office din sosai yayi kmr yadda yake
yi a duk sanda ya shigo  hannunsa d'aya cikin aljihun wondonsa  yayinda d'ayan hannun kuma ya d'aura   akan table . shiru tayi tana ciza harshenta kamar tayi dariya dan wannan salon nasa yana matukar burgeta kuma yana sakata jin nishad'i acikin ranta sai dai ganin yadda yayi mugun had'e rai fiyye da kullum dan fuskar nan tashi sam babu annuri kirki yasa tayi maza  ta sanyawa jikinta natsuwa tare da lumshe idanunta na second biyar sannan ta bud'esu fess akan kyakkyawar fuskarsa ta sake gaishesa a karo na biyu ". “good morning sir ?!
Chapter 42 · 0% Book details