← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 111

Sashe 73

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

alokacin sai Allah yazo ya dora ma alhaji rafi'u giwa wani irin hakuri akan bilkisu ya cigaba tsabgoginsa da harkar kasuwancinsa da muamula da sauran ya'yansa ."sai gashi ita daga baya ta kasa hakuri tayi ta zuba ido yaushe ne bilkisunta zata zo ?"yaushe ne zata dawo garesu a tun shekarun goman nan gashi har an haura shekara ashirin bilkisu shiru tun tana ganin abun kamar film har sai da'aka d'auki wannan shekarun babu ita babu labarinta tasan cewar lallai bilkisu tayi fushi mai tsanani dasu kuma babu tabbas din zata dawo domin duk inda take a yanzu ta tsaya bisa qafafuwanta  kuka take sosai," wannan ciwon na rashin bilkisu ciwo ne da kullum yake cin zuciyarta wanda take jin bazai ta'ba warkewa ba har qarshen rayuwarta ,tunda zuciyarta tayi nisa daita ta rasa wani bangaren na rayuwarta ."tana zaune tana kuka yaya mahmud ya shigo d'akin bakinsa d'auke da sallama ,ganin halin da take ciki ya bita da wani irin kallo kafin ahankali ya qaraso gareta jikinsa na d'aukar rawa ya durkusa agabanta ya kamo hannun ta cikin nashi babu abinda ya tsana kamar ganin hawayen iyayensa balle mahaifiyarsa da bai da kamarta a duniya kukanta har cikin zuciyarsa yake ji "mum kiyi hakuri ki daina kuka nan ki fad'a min damuwarki kafin tace wani abu tuni hotunan bilkisu guda uku dake rike a hannunta suka zubo."

yabi hotunan da kallon mamaki yana jin wani iri acikin zuciyarsa dama gangar jikinsa nan take jikinsa yayi mugun sanyi domin kuwa ko bata fad'a masa damuwarta ba yasan kukan rashinta take yi nan take yaji da akwai yadda za'ayi ya dawo mata da bilkisunta da zai yi amman sun rigada sun ma kansu alqawari muddin ba itace ta dawo da qafafuwanta babu wanda zai taka zuwa gareta ,ya matso sosai kusa daita yasa kanshi akan cinyarta yana jin yadda zuciyarsa take ta fasa yana jin kamar sune silar kukan mahaifiyarsu ,yana jin duk laifinsu ne da suka taru suka had'a kai akan kin auren bilkisu ina ma sun sani sun amince a tun farko sun inganta rayuwar yaron da yanzu suna cikin walwala da farinciki  ." nan take shima hawaye suka fara gudu akan kuncin soja aka rasa mai rarrashin wani acikinsu ."yaya mahmud yayi amfani da qarfin zuciya irin tasu ta sojoji ya cigaba da bata hakuri da rarrashinta "kiyi hakuri nasan bamu yi miki adalci da muka biyewa son zuciyarmu akan rayuwar bilkisu ba ,munyi nadamar abinda muka aikata agareta , kuma a yanzu a shirye muke da muje gareta, zamu dawo da yaruwarmu cikinmu mu cigaba da rayuwa ,mu had'u gabad'aya mu dinga faranta miki ."

wani sanyin dadi ne ya ziyarci zuciyar hajiya rahma dan ta dade tana mafarkin zuwan wannan ranar ta dade tana rokon allah yasa ya'yanta su fahimceta sosai yaya mahmud ya gyara kanshi akan cinyarta "ina mai sake baki hakuri ki yafe mana ko zamu samu sausauci abinda muka aikata, bai kamata mu biye miki alokacin da kika d'auki zafi akan bilkisu ba ,kamata yayi mu zamanto masu rarrashinki da baki hakuri tare da nasiha ki rungume qaddarar bilkisu amman sai muka zama mune gaba  gaba gurin  nuna isa da iko  tare da jayayya da hukuncin ubangiji ,yau gashi bilkisu ta kar'bi qaddarata ta manta damu ta cigaba da rayuwarta cikin kaskanci batare data nemi mu ba bare ta nemi taimakonmu  wanda mu abinda muka kudurta kenan aranmu tasha wahalar rayuwa ta wulakanta ta tozarta tasan amfaninmu sannan ta dawo garemu mu kuma mu samu damar nuna mata kuskurenta na za'bar wani ta barmu sai gashi tayi hakuri kuma ta  jure duk wani tsanani  ta cigaba da rayuwarta ta bar zukatan mu da tarin kewarta ."

ahankali hajiya rahma ta kai hannu tana shafa kanshi tace "kukan ya isa haka mahmud ni baku min laifin komai ba hassalima hukuncin da kuka zartar da yardata da kuma amincewata ne na yafe maku duniya da lahira ,ni dai ka nemi sauran yanuwanka kuyi magana a tsakaninku ina son ganin bilkisu kafin mutuwata, wallahi mahmud nayi nadamar abinda nayi ma bilkisu ku kawo min ita kafin mutuwata duk da nasan mijin data aura bai cancanta daita ba amman na hakura tunda qaddararta kenan ya d'ago kanshi yana kallonta kafin ya saka kafin ahankali yasa hannunshi ya rike kunnuwansa "I promise you mum in sha allahu very soon zamu kawo miki bilkisu har cikin d'akin nan ya qarasa maganar yana sakar mata murmushi itama murmu shi tayi tana jin wani dadi sanyi at the same time tana tunani aranta daman tasan addua bata faduwa kasa banza Allah mai amsa addua, ta godewa Allah da yasa mahmud ne ya fara fahimtarta domin shine yafi kowa zafin zuciya da d'aukar zafi tunda har ya sauko tasan saukowar sauran ma bazai yi wahala ba ."

Alhaji rafi'u  yayi sallama ya shigo d'akin yana
kare musu kallo, yana ganin  farin cikin a kwance a fuskar kowanensu wanda ya jima bai gani ba haka nan shima with a smile yana godewa Allah daya
bashi family d'inshi da kuma ya had'a masa kansu guri d'aya. yace. "ahhh ana mommy and son time ne haka ?" nima bari nazo ayi dani, shikenan sai ya zama daddy mommy and son time." dukansu suka kwashe masa da dariya cikin farincikin da kwanciyan hankali hajiya rahma ta kasa hakurin rike maganar
bakinta ,ta tashi taje ta rike hannun alhaji rafi'u tana murmushin jin dadi  “dadynnmu albishirinka "dake wani lokacin haka take ce masa tamkar yadda yoroba kan kira mazajen aurensu " murmushi ya sake yi sannan yace "mumynmu goro "!ta kallesa tace kuma  dole sai an bani tuk'uici" tana magana tana dariya yace momynsu "an gama amaryata ran gidana ,dadybmu mahmud  yace very soon zai dawo  mana da bilkisu cikin gidan nan very soon zamu ga bilkisu da yan jikokinmu " yadda take murna kamar karaman yarinya, shima alhji rafi'u ya biye mata sunata dariya suna magana tare da murna yaya mahmud kuwa kamar kasa ta bud'e ya nutse a cikinta haka yakeji dan haka ya yunkura ya tashi da sauri ya bar musu dakin yayinda alhji rafi'u da hajiya rahma suka cigaba da tautaunawa kuma duk akan bilkisu ."

*****

Bayan kwanaki bakwai din da mr ata yasa aka turawa nadiya sakon an dauketa aiki tazo domin interview ranar da kwanakin ya cika ya dauki maryama zuwa kamfaninsa na ATA dake cikin ikeja wani office dabam  ya kai maryama  yace ta zauna shi kuma ya shiga office dinsa ya zauna  kusan awa uku da zuwansu inda ake ta faman yiwa sabbabin ma'aikata interview amman nadiya shiru  babu ita babu alamunta nan hankalinsa ya fara tashi ya mike tsaye ya fara zariya yana  kai kawo  daga office dinsa zuwa office din da  maryama  take amman ita sam bata ma lura dashi ba  ita kanta hankalinta naga babbar kofar shigowa ne yayinda pencil ne a bakinta tana cizawa tana tunanin nadiya akaro na karshe ne yana shigowa zuwa inda take ya fixge pencil din bakinta ta waigo  a natse  ta kallesa wanda shi daman  kwayar idanunshi na kanta shiru sukayi suna kallon juna kafin ahankali ta motsa lip's dinta "so.."karki ce min wani sorry !”yayi saurin katseta ta hanyar cewa haka yana furza mata hucin numfashin bakinsa kafin ahankali yaja qaramin tsaki ya cigaba da magana"me yasa zaki dinga over thinking haka ?".

Maryama ta sauke numfashi cikin tsananin damuwa sannan ta mike tsaye ta tsaya kusa dashi "har yanzu  ina mamakin nadiya da karfin halinta ne  sannan ina mamakin abinda yasa ta bawa wani numberta ya kira akan nazo aiki da wuri anya kuwa babu cutarwa acikin lamarinta "wannan kuma ya rage naki da hankalinki da tunaninki baki ta'ba ganin mutun ba koda a hira  shi wancan mataccen bai ta'ba  baki labarinta ba amman ki bari ta shigo muku gida kuma har ki kaita d'akinsa yanzu idan ya zamo ta ajiye wani mugun abu acikin d'akin fa ?ko kuma akwai abinda ta shirya maki akan hanyar ki ta zuwa aiki  yasa tasa aka kiraki kizo aiki da wuri ?duk hakan zai yuwu, ku duk wanda yazo maku da maganar masoyi sai kuyi saurin yarda dashi  saboda gaku yan gani kashenin soyayya ."ya fad'a yana fesar da iska”.

"bare ni akan ya sadam kam idanuna sun rufe kuma ina saurin yarda da duk wanda yazo  gareni da sunansa ko maganarsa ." tsaki yaja tare da yin shiru yana kallonta yana jin wani zafi aransa, ta kalli agogon hannunta "sir did you realize one thing ?" yana jinta kuma stil tsumammum idanunshi na kanta amman yayi mata banza "wallahi idan banga nadiya ba yau bazan ta'ba samun kwanciyar hankali ba  har qarahen rayuwata duk rayuwar da zan gudanar acikin kunci zanyita "numfashi ya sauke kana ya lumshe tsumammun idanunshi yace "ina tabbatar miki sai kinsan gskyar da take boye miki dan rashin kwanciyar hankalinki zai iya shafar aikina ."na gode sosai sir !” ta fad'a adaidai lokacin da wani ma'aikaci ya shigo ya mika masa cup cike da girmamawa ya amsa ya  kai cup din coffee bakinsa ".ya fara kurba ahankali ahankali.

Maryama ta dubesa a tsanake yana shan coffee yana lumlumshe idanunshi "bansa yadda zan misata maka farincikina ayau ba ina jin kamar ka bani komai dake cikin duniyar nan  ne ,na gode na gode sosai sir "maryama waya fad'a miki ina yin duk wannna abun saboda ke ne ?ta kallesa a matukar tsorace gabanta na wani irin  fad'uwa "yes ki daina kallona haka ni duk abinda nayi ina yi ne dan company dina  ne kamar yadda na fad'a miki yanzu banason wani abu ya samu aikina idan ban yi abinda zuciyarki zata damu natsuwa ba kasuwancina zaiyi rauni sakamakon ina son na had'a miki aiki biyu a qarqashina .”ya qarasa maganar yana sake lumshe mata ido .tsaki taja a kasan ranta "wannna anyi mugun miskilin mutun  mai shegen girman kan tsiya mai  fuska biyu kawai sai ya nuna kmr ya damu da mutun sai kuma ya dawo ya bullo da wani salo  ta fad'a a kasan ranta tana hura masa hanci ".
Chapter 73 · 0% Book details