← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 111

Sashe 11

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin zufa ne ya shiga tsatsafo masa akan hancinsa da ilahirin jikinsa ,ahankali ya kai hannu ya lalubo wayarsa ya soma binciken unguwar da take domin dai yana bukatar yaga yanayin tsarin unguwarsu "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ya furta a fili yana mai sake tsurawa wayarsa do tagumi yayi da hannu d'aya yana tunani irin rayuwar da mutun zai yi a irin wannan bazar unguwar numfashi ya janyo da kyar ya sauke sannan ya soma neman layin mb yana d'agawa yace "kazo yanzu yanzu ina AGC yana gama fad'ar haka yayi discounting din kiran ya kira salim da ammar."yayi baya da kujerar da yake zaune yana ciza lip's dinsa da qarfi babu abinda yake gani acikin kwayar idanunshi sai kyakkyawar fuskarta mai mugun kyaun gaske da yanayin jikinta tana rayuwa acikin unguwarsu imagenation dinta kawai yake tun daga qarancin shekarunta har zuwa sanda ya fara daura kwayar idanunshi akanta ,yanayin tsayinta da dogon hancinta shine yafi komai fito da ainihin sahihin kyawunta da Allah yayi mata ya numfasa yana sake lumshe tsumammun idanunshi "hakika maryama iyayenki sun iya haihuwa tunda suka haifa muradin zuciyar Adam .”yana cikin wannan halin sai gasu ammar sun bayyana a gabansa ."

SALIM ,AMMAR ,M.B duk suka zuba masa idanu suna kallonsa fuskarsa a sukwane kuma d'aure take kamar ko wani lokaci sai dai kallo d'aya sukai masa suka fahimci akwai abinda ke damunsa duk suka samu gurin suka zauna sukai shiru suna jiran suji abinda zai fad'a masu."ahankali ATA ya lumshe tsumammun idanunshi tare da sanya hannunsa d'aya adaidai saitin qirjinsa yana murza daidai inda zuciyarsa take beating very fast bayan kamar second goma ya ware tsumammun idanunshi sosai akansu yana kokawa da lamarin princess dinsa saka makon matsayinta daya fahimta domin duk a tunaninsa bai d'auka zata fito daga irin area daaka fad'a masa ba ,ya d'auka zai ganta acikin royal family ne ko wani babban attajirin ne mahaifinta sai a yanzu ne ma ya fahimci bayan mugun abinda take rufe fuskarta dashi har da ma unguwar da take rayuwa aciki ya janyo rashin had'uwarsu .wani abu ya had'iye mai d'aci daya tsaya masa a mak'oshinsa kafin ahankali ya mike tsaye ya tsaya ajikin bangon office din tare da tura hannuwansa duka cikin ajihun wondonsa ya tokare qafarsa d'aya da bango yana cigaba da dubansu kamar zai yi kuka cikin kasa da murya ammar yace "Adam ya'akayi ne ?ka taso mu daga kan ayyuka masu mahimanci meke faruwa ?meye dalilin taramu dakayi ?ammar yayi masa tamvayoyin a jere duk da jikinsa ya bashi akan maryama ne dan idan akan kasuwancinsu ne bai zai nemi har da mb ba dan meye had'in soja da kasuwanci ."

"kasani ammar! "ata ya fad'a yana kokawa acikin ranshi "kasan dalili kiranku ammar amman kafin nan nasa some ta kira yarinyar nan jiya amman gabad'aya kalamanta sun nuna bazatayi aiki dani ba, amman ni ba wannan bane damwta ." meye damuwarka ata ?"mb ya tambayesa cike da kulawa "sai da ata ya sauke wani naunayen ajiyar zuciya sannan ya motsa lip's dinsa "wai princess dinace tayi rayuwa a irin wannan banzar unguwar ."yayi maganar cike da tsananin fushi yana zare hannuwansa daga cikin aljihunsa yayi taku d'aya biyu sannan ya tsaya cak atsakiyar office din tare da juya masu baya "gyaran murya salim yayi kana ya fara magana cike da sanyin murya "to meye aciki Adam kowani bawa ai da irin tasa kalar qaddarar "a ina take zaune ne ammar ?"inji cewar mb yayi tmbyr yana duban fuskar ammar ". "tana zaune ne a unguwar gwagulori "ina ne haka kuma ?""wata geto area ce acikin agege local government "cewar ammar "kunji abinda naji kuwa acikin zuciyata kamar ni Adam tariq Abdallah ace matar da nake haukar so ce tayi rayuwa a irin wannan banzar unguwa wani irin rayuwa ma tayi ?"gidansu ne ko haya suke yi ? Ata yayi masa tamvayar yana dungule hannunsa ya kaiwa bango naushi .da mamaki gabad'ayansu suka mike tsaye cikin tsananin tashin hankali suka qaraso inda yake suka rikesa suna kiran sunansa "what's wrong with you Adam ?" gabad'aya suka had'a baki wajen fad'ar haka."ka natsu mana ."

Shiru yayi kawai yana fesar da numfashi da iska mai zafi daga bakinsa gbdy yanayinsa ya canza zuwa na tsananin damuwa, fixge hannunsa yayi yana shafa daidai qashin hannunsa daya bugu yana watsa ma ammar wani mugun kallo .da sauri ammar ya d'auke idonsa saboda mugun tsoro daya kamasa ya koma ya zauna ."mb ya kallesa cike da tausayawa domin dai ya fahimci tausayi ne mai tattare da tsananin son da yake mata yasa shi shiga damuwa janyosa yayi ya zaunar dashi yana cewa "ka kwantar da hankalinka Adam haka rayuwa take kai a tunaninka zata zamanto diyar wani kamar yadda ka kasance to shi Allah ba haka yake son ganinta ba sannan ba hk tsarinsa yake ba ,ganin damarsa ne ya hada masoya masu wadata waje d'aya haka ganin damarsa ne ya hada talaka da mai arziki ." nasan kasan dukkanin rayuwa rubutaccen lamari ne daga rabbi yadda yaso haka zai yi ,saboda haka kasan duk wannan mai sauki ne a wajen Allah fatan mu yarinyar ta amince da soyayyarka tun da ka rigada ka gano Inda take .”

shiru ata yayi ya fad'a kogin tunani sosai hankalinsa ya bar duniyar da yake ya lula dashi can duniyar maryama inda zuciyarsa ta shiga hasko masa ita tare da wani tana rayuwar aure daahi . wani dogon tsaki yaja yana sake taune gefen bakinsa da qarfi saboda zafin kishin da yake ji hakika idan yace yaji dadin kasancewarta a bazawara yayi wa kanshi karya yaso ace shine mutun na farko da zai fara muamula ta aure daita bawani katon bazan can ba "Adam ka daina zurfafa tunani da yawa akanta tunda already kasan ta ta'ba aure ,tunda ta ta'ba aure kasan dole wani abu zai shiga tsakaninta da wanda ta aura ita kad'anta kake so kuma ko a wani hali take zaka kasance daita ." "jin an dafa kafad'ansa yasanyashi sauke kwayar idanunshi akansu "ba shiga damuwa ko dogon tunanin zaka tsaya ba abinda ya kamata kayi yanzu ka gaugauta aurenta domin ka inganta rayuwata kayi ma iyayenta duk abinda kasan ya dace ."inji cewar mb "Allah kad'ai yasan irin rayuwar datayi acikin wannan banzar unguwar mb ku duba map kuga yanayin tsarin unguwar datai rayuwa aciki inna ilaihi "ya sake furtawa yana yarfe hannu alamun abun na masa ciwo ".kai yanzu meye damuwarka da unguwarsu ? unguwarsu kake so ko ita ?"salim ya tambayesa wani kallo yayi masa yana fesar da huci yana sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri." rabu dashi salim dan ma bai shiga lungun unguwarsu bane yasa yake fad'ar haka ."wani sabon zufa ne ya karyowa ata yayinda salim ya barke da wata irin dariya yana cewa "ai daidai kenan kamuwa da soyayyar yar talakawa zai sa wasu abubuwa su..."wani mugun kallo ata ya watsa masa wanda yasa salim yayi shiru yana kunshe sauran dariyarsa "ba hararar mutane ya kamata kayi ba kayi maza kayi abinda ya dace ku fahimci juna da yarinya ka aureta kafin wani yazo yayi maka shigar sauri "wannan duk ba matsala bane zan yi duk yadda zanyi ta dawo karkashin ikona . "fatan nasara abokina sun dan jima suna tautau nawa kafin daga baya kowannensu yayi masa sallama ya wuce suna fita yasa a kira masa baba gali "

*******

Cikin sauri sauri maryama ta fito daga bangarensu tana wa Aunty sallama kai tsaye part din umma ta shiga domin tayi mata sallama ta saka mata albarka tana rungumeta ajikinta "fatan alkhairi diyata "na gode umman ,maryama tai murmushi ta qarasa gurin hjy granny " Kiyi min addua kakata "allah ya tsareki maryama allah yasa zaki fara wannan aikin a saa sosai sukai mata addua ta soma kokarin barin parlour'n suna tsaye suna kallon bayanta suna rakata da addaua ."tana daf da kaiwa bakin kofa sai ga sallamar baba gali da aunty hassana tana ganinsu tai saurin durkusawa har kasa ta gaishesu"baba ina kwana aunty hassana ina kwana ? bata gama rufe bakinta ba sai ga mahaifiyarta itama ta shigo adaidai lokacin da yake amsa mata da "lafiya! Atakaice yana qare mata kallonta tare da cewa ina zuwa haka ?zani aiki ne ta bashi amsa jiki a sanyaye."what !? ya furta da karfi ai kuwa gara dana daka sammako ai wannna aikin baza kiyishi ba saboda ke na shigo bangaren nan .a matukar tsorace maryama tabishi da kallo kafin daga baya kalmar "inna ilaihi wa inna ilaihi rajiun ya dinga fitowa daga cikin bakinta tana maimaitawa nan take jikinta yayi sanyi." "ungu nan ki karanta, emvelop ya mika mata tasa hannu ta karba jikinta na cigaba da rawa a firgice ta dinga bin rubutun sako ne daga AGC compaing wani sabon tashin hankali ta sake shiga mai tsanani tana dafe goshinta ."

"ki karanta a fili so that kowa da kowa yaji babu yadda ta iya ta soma karanta sakon a fili jikinta na wani rawa gabadayansu shiru sukai suna sauraronta zufa ne ya karyo mata sakamakon anyi cancelling sabon aikin data samu sakamakon AGC compaing na bukatarta sai kuma kamfanin gidan burodi wanda yake mallakin umma shima zai tashi domin zaa hana duk wani kamfani dake sarrafa flour bashi kaya jikinta ya cigaba da rawa kafafunta suka kasa daukarta ta sauke takadar tana furta "umma ki rikeni "! da sauri duk suka yi kanta banda mutun biyu baba gali da Aunty hasana "kasancewarki a AGC compaing shi zai sa kasuwancinmu ya cigaba da tafiya akasin haka kuwa kema kinsani sai dai a rufe kanfani mu zauna haka ya qarasa mgnr yana karbar takarda da ya bata ya kalli umma ya kamata kiyi wa wannna yarinyar magana idan ba haka ba zamu rasa komai ."
Chapter 11 · 0% Book details