← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 111

Sashe 80

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Numfashi ya sauke yana cewa “is okay na fahimceki” na gode sosai Allah ya biya maka bukatunka na alkhairi a kasan zuciyarsa ya amsa da” ameen!”tana qoqarin fitowa daga cikin motar kira ya shigo wayarta ahankali ta koma ta zauna tare da ciro wayarta sunan umma ta gani yana yawo akan screen din wayar da sauri taja koren maddani tana qoqarin kai wayar kunnenta ya rike tsintsitar hannunta tare da saka wayar a hands free “maryama kina ne ?”kiyi maza ki qaraso gida yau alkubus nayi mana nasan zakiji dadi sosai”kyakkywan murmushi ne ya bayyana akan fuskar maryama sannan tace “sosai kuwa umma nah gani nan yanzu zan shigo ,to shikenan kiyi sauri kinsan idan yayi sanyi bashi da dadin ci” umma ta fad’a cike da kulawa “yanzu nan zaki ganni ummata sai kin shigo umma ta fad’a tana katse kiran inda maryama ta kalli mr ata fuskarta da bayyananne murmushi “tabbas ya yarda matar na tsananin sonta wanda hakan yasa yaji zuciyarsa ta dan bata wani matsugune acikinta har bakin get din gidansu ya rakota sai daya ga shigarta sannan ya juya ya wuce gida .”

Ahankali ya shigo parlour mami ya ajiye yar saman suit dinsa akan hannun kujera idanunshi na kan mami dake tsaye ta d’ago ta kallesa a natse kafin ahankali ta qaraso zuwa inda yake ta tsaya tana tambayarsa”lafiyarka meke faruwa na ganka haka ?”shiru yayi kawai yana hura hanci tasan halinsa a duk sanda yayi haka baya bukatar acigaba da damunsa akan abu “ ka qarasa d’akin ka kayi wanka kazo kaci abinci kanshi kawai ya gyada sannan ahankali ya zagayeta ya haye sama bayan wasu mintuna mami taji shiru bai sauko ba ta nufi dakinsa a zaune ta iskeshi shiru cikin yanayi na tsananin tunani ta zauna kusa dashi “wai meke damunka ne “?ta tamabyesa cike da kulawa “babu abinda ke damuna sweetheart ko kina tunanin akwai abinda zan iya boyewa kyakkywar mahaifiyata ?”harara shi tayi tana cewa ”akwai mana sau nawa ina tambayarka abu kace min babu komai alhalin kuma ni nasan da komai din .”shiru yayi batare da yace uffan ba “nifa nasan halin d’ana,nasan yanayinsa kuma nasan yanayin damuwarsa kawai dai ka fad’a min “ya kamo yatsun hannunta cikin nashi yana cewa “babu komai sweetheart just believe me, I can’t believe you adamcy amman dai me kake son kaci muna da rice and stew da farfesun kan rago muna da tuwon semoveter da miyar danyar kubewa da cat fish, muna da light soup daakayi mix dinsa da kan rago da kayan ciki da busashen kifi muna da ..” sweetheart alkubus zanci .”

“ alkubus zaka ci bayan shekaru masu yawa rabon daka ci “?“yes shi zanci sweetheart ya fad’a yana lunshe mata tsumammun idanunshi shiru tayi kawai tana kallonsa ,kin bude idanunshi yayi saboda gabadaya jinsa yake acikin wani iri yanayin kamar ya yi kuka ko ya samu salama a zuciyarsa da Kyar ya bude idanunshi sakamakon jin shirun mami “kiyi hakuri sweetheart nasan bazan samu ba “babu wannan ranar da d’ana zai ce ga abinda zai ci ni kuma na kasa masa tayi maganar kamar zatai kuka “na dade ina expecting haka kullum burina naji kace zakaci abinci da mahaifinka yafi so shiyasa naji maganar wani iri”bari naje nayi maka just ka bani lokaci kad’an yanzu zanje nayi maka alkubus “ ta mike ta fita da sauri tana goge gutun hawayen daya cika gefen idanunta.”

“Kai umma qamshi allubus din ya cika koina agidan nan ,da gaske maryma?allah kuwa barin ma qamshin miyar maza maza kije kiyi fresh up kizo kici tun kafin yayi sanyi “okay umma ta fad’a tare da nufar hanyar dakinta da sauri .” bangaren mr ata zaune suke shi da mami akan gado tana bashi alkubus abaki “sweetheart !”bata amsa ba ta tsaya tana kallonsa me kike tunani haka ?”ina tunanin wasu abubuwa da suka gabata ne sannna kuma ina kallon kyakkywan d’ana .”sweetheart ki daina dogon tunani haka kinji kin rasa abba amman kuma kina damu biyar ina son ganinki cikin farinciki’ “uhm ta furta a kasan ranta sannan ta soma mgn “kana son ganina cikin farinciki amman zuciyarka ta kasa amsar zabina kuma farin cikina ?”tayi maganar cike da rauni ina tsananin jin tausayin maryam” yanzu haka nata rayuwar zai kare cikin rashin jin dadin rayuwa?mai yasa adam?ni abinda nake so kuma yafi komai mahimanci arayuwata shine ka yarda ka kuma amince da cewar cikin jikinta naka ne kuma zaka so shi kamar yadda naka uban ya soka ya kuma nuna maka gata ,ina son naga murmu shi akan fuskar maryam I just want to see the smile on her face .”shiru yayi yana kallonta kafin ahankali ya motsa lips dinsa “sweetheart kin kasa fahimtar zuciyar adamcy dinki abinda bazai ta’ba yuwa bane is not possible na amince …”

Cak zuciyar mami ta tsaya ta daina bugawa yadda ya kamata tare da zuba masa idanunta” ki rabu da damuwar yarinyar nan kawai ta girbi abinda ta shuka dan Allah sweetheart ki bar min maganarta ,ki barni a yadda na tsaida zuciyata shiru ne ya biyo baya kafin ahankali ta cigaba da motsa labbanta “batun wacan yarinyar fa ?”yayi shiru kawai yana dubanta fuskarsa da alamun tambaya “wacan yarinyar data shigo rayuwarka nake nufi ko ..”ko itama bazaka ce wani abu akanta ba ka kawo min ita ni zan fad’a mata cewar kana sonta kuma nasan zata fahimceni ina son naga ka zama cikakken mutun adamcy duk da kai baka bin umarnina ni zan maka komai amatsayina na uwa zan baka farinciki daka qasa bani saboda tsnanin son da nake maka ta qarasa maganar kamar zatai kuka “tunda naji zuciyata tana son ganin yarinyar tabbas rayuwar adamcy nace .”shiru yayi kawai tare da zuba mata idanunshi yana shafa fuskashi da tafin hannunsa yana tunain maganganun maryama wanda har lokacin zuciyarta tana ga wani ,gabansa ne ya dinga bugawa da qarfi “sweetheart karki damu maryama zatazo ta ganki “

Mmn Sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.

38

A kaikaice mami ta kallesa sannan tace “maganata ta tabbata kenan ?ATA ya bala’in tsurawa mami Ido yana kallonta fuskarsa d’auke da mamakinta yayinda kwakwaluwar sa ta shiga maimaita masa abinda ta fad’a yanzu “maganata ta tabbata kenan “.to me hakan yake nufi?” “adamcy!“ ta kira sunansa tare da riko tafin hannunsa cikin wani irin yanayi mai cike da tashin hankali da jin tsoron abinda take son fad’a ,shi kam kallonta ya cigaba dayi cike da rauni tare da yin kasa da murya yace “sweetheart ina jinki “da gaske adamcy son yarinyar nan kake tunda gashi kace zata zo? numfashi ya sauke yana cigaba da kallonta “itace fa ta matsa masa da batun tana son ganin maryama yanzu kuma ga abinda take fad’a “wai meyasa sweetheart take masa haka ne ?numfashi ya janyo da kyar ya fesar sannan ya motsa lip’s dinsa yana cewa “sweetheart nifa ban fahimceki ba?” ya qarasa maganar yana mai kawar da kanshi daga kallonta “adamcy nasan ka fahimceni sosai ba iya zargina ba ,hatta zuciyata ta aminta da son da kake ma yarinyar nan abida naso ya faru akan mar…” .“sweetheart abar maganar nan .”ta sake bud’e baki har ta soma magana ya juyo da sauri yace “dan Allah sweetheart karki sake cewa komai akan yarinyar nan ,itama maryama baza tazo ba shikenan “ya qarashe maganar cikin ‘bacin rai da rauni a fuskarshi ,ya rasa dalilin da yasa take masa haka idan ma son yarinyar yake me ye laifi aciki tunda shi ba yaro ne da zaa dinga masa irin haka?.”tace tana son gani yariya yace yaji sannan kuma ta shigo masa da batun wata maryam abinda ta rigada tasani ne ko maganarta baya son ana masa,wannan matsalar na cikin abinda yasa yake son ya auri maryama a boye sai bayan sun haihu sannan ya fad’a mata dan yasan kota amince ya auri maryama to fa kullum sai tayita masa mitar rashin kasancewarsu da wannan banzar maryam din ”.

“Me yasa?kuma saboda me za’a bari “?me yasa zaka d’auki zafi daga ‘yar wannan maganar har kace baza tazo ba ?”tayi masa tambayar ajere tana dubansa cikin tsananin tashin hankali duk da dai tafi son shi da maryam dinta amman kuma hakan bazai sa taki son abinda yake so ba dan arincikinsa shine nata “kayi shiru kana jina kayi magana mana,sarkin zuciya. “Kai dai ba’a ta’ba yin hirar arziki da kai batare da ka shigo da zafin zuciya ba ,kanshi ya juya tare da zare hannunsa cikin nata ya had’e waje d’aya ya fuskanci mahaifiyar tashi cikin sanyi yace “ba maganar zuciya bane kawai dai gani nayi rashin zuwan nata zai fi zuwanta samun kwanciyar hankali”amman dai kasan kana son yarinyar nan “inna lillahi ya furta yana runts ido “babu wani batun inna lillah gskyr dake cikin zuciyarka nake son nasani “dan girman Allah sweetheart ki bar maganar nan kuma maryama bazata zo ba dan nasan zuwanta ba zai kwantar miki da hankali ?
”girgiza masa kai tayi alamun a’a.”karka damu ka kawo min ita Ina son naga ka sake ajiye iyali a karo na biyu, zaka auri yariyar nan kuma anan kusa idan ma bazaka iya sheida mata kana sonta bane ni zan sheida mata da kaina karyata taki amincewa ,dan banga macen duniya da zaace mata ga miji kamar d’ana tayi rejecting ba gara ma ka natsu ka kawo min ita ni na sheida mata d’ana yana sonta tunda kai girman kan tsiya bazai barka ka iya sheida mata ba.”numfashi da ajiyar zuciya ya sauke atare still idanunshi na kallonta .mami ta jima zaune suna hira irinta d’a da mahaifiya sannan tai masa sallama ta sauko qasa ta shige bangarenta .”
Chapter 80 · 0% Book details