← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 111

Sashe 81

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan fitar mami tashi yayi ya shiga bedroom dinsa ya qarasa inda system dinsa yake ya d’auka ya dawo kan bed dinshi ya kishingid’a akan gadonsa had’e da tokare hannunsa d’aya a gefen kungunsa sannan a hakan ya kunna system ya soma daddana keyboard din system dinsa yana amsa sakonin abokan kasuwancinsa yayinda bangaren maryama itama zaune take a tsakiyar gadonta ta rungume pillow a qirjinta tana tunanin abinda ya faru yau atsakaninsu sosai take tunanin abinda mr ATA yayi mata a yau din nan ,ahankali komai daya faru tsakaninsu yake zuwan mata daki daki har zuwa sanda ya kamo hannunta yace“tayi jump !”jump maryma” ya fad'a hankalinsa a matukar tashe yana sake hura hanci “wannan  shine best solution agareki ,shine kawai abinda zai kawo miki qarshen kuncin da kike ciki ,kuma shi zai kawo qarshen rayuwarki .”
”kina zubar da hawayenki a banza bayan Kinsan mutumin nan ya mutu baya raye "wani irin tsoro da matsanancin firgice taga ya bayyana akan  fuskarsa alokacin "oya jump!”har sanda ta soma kuka mai tsanani wanda ya zamo sanadiyyar kawar da tarin damuwarta wani irin naunayen ajiyar zuciya ta sauke mai qarfi tana cewa “duk rashin kirkinka da nake gani still kai din mutu min kirki ne ,ban ta’ba tunanin zaka zamo silar yayewar damuwata ba sai gashi acikin awanni ka zamo silar kawar da tarin damuwar da nayi shekara da shekaru ina dawainiya dasu.” “hakika kai din mai kyakkywar zuciya ne ,kawai da nice da wasu daga cikin mutane muke maka wani irin kallo ,duk da kana da wasu dabi’u marasa kyau amman dai kana da kyakkyawar zuciya .”ta furta a fili fuskarta bayyane da murmushin farinciki ta matse pillow dake makale a qirjinta tana cewa .”maryama tana godiya bisa qoqarin da kayi mata na gode sosai daka canza min rayuwa .”

ahankali mr ata ya d’auke kwayar idanunshi akan system zuwa wani bangare dabam tare da rufe system din gaba daya“ya d’aga kanshi sama kallon saman d’anki tunanin maryama yake yana jin kamar ya kirata “idan ka kirata kace mata me?”ai ita ya kamata ta kiraka no kai ya kamata call her and tell her how much you loves her dan idan ka bari wani ya sake sace zuciyar yarinyar nan zaka iya mutuwa for real you’re so much in love with her .”ya fad’a yana runts tsumammun idanunshi .a natse maryama ta sauko daga kan gado ta soma tafiya tana magana a fili muryarta cike da matsanancin farinciki “na gode sosai mr ata Allah saka maka da mafificin alkhairi.”
shima bangarensa mikewa yayi tsaye tare da yin shiru ya saka hannunwansa duka cikin aljihunsa
wondonsa yana magana a fili “lallai soyayya ya zautar da kamilar yarinya mai tsananin baseera da sanin kan aikinta yana matukar son furta mata cewar yana sonta amman soyayyar wannan mataccen da yake hangowa har yanzu acikin kwayar idanunta shine dalilin da yasa ya kasa fad’a mata ,hakazalika itama karon kanta shine dalilin da yasa ta kasa fahimtar inda ya dosa ina ma zata bashi damar daya d’an d’ana mata gard’in soyayyarsa.”amman zan yaki zuciyarta.
“ zan yi duk yadda zanyi na raba zuciyarta da tunanin kowa sai nawa ,zan dasa mata qaunata ta yadda zata kasa samun kwanciyar hankali sai tana tare dani.”cire hannuwansa yayi duka yaje ya bud’e wordrobe dinsa ya d’auko wani takarda ya rufe wordrobe din ya tsaya sosai rike da takardan yana kallo yana cigaba da tunanin maryama sosai yake jin tsananin soyayyarta na sake ratsa dukkanin sansar jikinsa kai kawo ya shiga yi acikin d’akin shi kad’ai yasan irin azabar da yake ji ajikinsa .”

Hotonsu maryama aunty abida ta tsaya tana kallo jikinta na wani irin rawa tmkr mazari “meye haka sultana? meke faruwa haka ?”mafarki nake ko kuwa gaske ne abinda nake gani adam ne rungume da wannan yarinyar ?shine aunty ai ba wannan bane karo na farko da suke lalatarsu a office sai dai wannan shine karo na farko da nayi qoqarin d’aukarsu batare saninsu ba bama fa AGC wannan abu ya faru ba d’aukar ta yayi taka nas suka bar kamfani zuwa ATA company .” “aikinsu fa kenan sai dai idan basu had’u da juna ba.” nan take gaban aunty abida yayi wani irin bugawa da qarfi tamkar wata matarsa “aunty da alamun yaya adam yana tsananin qaunar yarinyar nan “ai wannan ma ba abu ne mai yuwu ba sultana kinji yadda nake ji kuwa “ta mika mata wayar tana cewa” ai kallon wadan nan hotunan zai iya sa mutun yayi loosing temper dinsa .”wallahi aunty haka nake fama da wannan bakinciki kullum zuciyata kamar ta fashe ni nasan bazan ta’ba samun auren yaya adam ba kinsa zuciyata ta kamu da tsananin soyayyarsa .”ta qarasa mgnr tana dafe goshinta

“aunty kece kika dasa min soyayyarsa a zuciyata gashi nazo ina masa wani irin mahaukaci so da bazan iya rayuwa babu shi ba “sultana ta qarasa maganar cikin zafin rai “ki natsu sultana duk runtse duk wuya ina tare dake kuma zaki auresa sannan soyayyarsa da wannan yarinyar ba abu ne mai yuwuwa ba kamar ma ya lalace ya gama “me zaki iya yi aunty akai ?zanyi komai akai sultana “sultana ta matso kusa da auntynta tana cewa “aunty kibi komai a hankali karki yi bakin jini ki barni dashi “no no sultana gara ni nayi saboda kinsan halinsa bazai ta’ba d’aga miki qafa ba “yadda bazai ta’ba d’aga min qafa ba haka kema bazai d’aga miki ba amman da sannu ni zanyi maganinsa sai na watsa hotunan nan zuwa social media kowa ya san halin da yake ciki sai dai kafin nayi haka sai muyi da wajewa dashi zai aureni ko kuwa na yad’a idan ya amince fine idan kuma yayi taurin kai nima zan nuna masa kalar nawa taurin kai ta fad’a idanuwanta na kawo ruwan hawaye “.

“mai na rasa aunty da yaya adam bazai soni ba ?wallahi aunty ina tsananin son yaya adam yana da matukar mahimanci arayuwata ina mutuwar son shi amman shi ko kad’an baya qaunar sanyani acikin kwayar idanunshi .”mai yasa ya bawa maryama mahimanci haka arayuwarsa in takaita miki aunty a irin soyayyar da yakewa yarinyar nan baya iya juyata a office komai taga dama shi take yi kuma yana kallonta bai isa yayi magana ba amman kuma nasan duk yana yin haka ne saboda yana samun wani abu agurinta ka rasa ma sonta yake ko kuwa saduwa yake daita .?”ni babu ruwana sultana da ma koma menene a tsakaninsu ni dai ya barta kawai ya fuskanceki kema Kinsan dole kema kiyi closing dashi idan ya kama ki mallaka masa kanki ne duk kiyi domin dole ki zama suruka acikin gidansu dan bazan bari wata mace ta sake shigowa cikin rayuwar adam ba never .”sultana tayi shiru kawai tana duban yayarta dake tsaye cikin tsananin tashin hankali anya kuwa zata iya wannan kasadar mallaka masa kanta fa ta ina ma haka zata kasance a tsakaninsu mutunin da ko second biyar baya bata za dai ta tuntubesa akan aure idan yaki kuwa zata bashi mamaki .”

*****

Washegari

Ahankali maryama ta shigo cikin ma’akatan sanye cikin doguwar riga baka mai ratsin ash colour ajiki tayi rolling din kanta da mayafi ash yayinda qafafuwanta ke sanye da bakaken flat shoe haka jikinta wani irin sihirtaccen qamshi mai sanyi ne yake fitarwa,jikinta a sanyaye take tafiya makale da jakar aikinta sai dai kallo d’aya zaka mata ka fahimci yau din tana cikin farinciki .”a natse ta shiga lifter zuciyarta da kwayar idanunta cike da tsananin farinciki son d’aura kwayar idanunta akan mr ata kofar lifter na gama bud’ewa ta fito tare da mutane dayawa kowannensu ya d’auki hanyar office din da zashi .”kai tsaye hanyar office dinsu ta nufa a natse ta shiga fuskarta d’auke da murmushi
ta gaishe da abokan aikinta sannan ta cire jakarta ta ajiye akan table daidai saitin kujerarta sannan ahankali ta kai kwayar idanunta zuwa ga office din mr ATA ta hango kujerarsa empty da alamun bai zo ba tai shiru kawai tana cigaba da kallon office din kuma tana tunanin kalmomin da zatai amfanin dasu wajen gode masa domin ya cancaci tai masa godiya na mussaman amman gashi bai zo ba har yanzu babu mamaki yazo ya fita ne ? zuciyarta ta fad’a mata haka .”

ahankali ta tsuke qaramin bakinta kafin ahankali ta fito zuwa inda ta hango madam some zaune ta qaraso tana gaisheta “good morning ma ?”
”mornig maryama !”ta amsa mata tana dubanta da kulawa “amm ko mr ata yazo kuwa ?”no !bai zo ba amman dai zai zo yana kan hanya “okay maryama ta fad’a tare da juyawa ta koma office dinsu ta zauna zuciyarta na cigaba da tunaninsa haka fuskarta na cigaba da bayyana farincikinta.”
Ko cikakken minti shabiyar batai da zama ba qamshin daddaden turarensa ya soma karasowa inda suke ta juyo zuwa bayanta nan take kwayar idanunta suka sauka akanshi yana taku ahankali cike da izza da isa yayinda duk taku d’aya idan yayi sai zuciyar maryama ya buga da qarfin gaske sakamakon qamshin turarensa dake kusantota .”
ahankali ya shigo office dinsa na farko inda madam some take zaune hannunsa d’aya cikin aljihunsa ,yayinda jikinsa ke sanye da wani had’ad’den suit brown colour ,suma kanshi dana fuskarshi na kwance luf luf kamar ta yan india madam some na ganinsa ta mike tsaye da sauri cike da girmamawa tace “good morning sir ?.”
”morning ! ya amsa mata atakaice sannan ya nufi kofar shiga cikin office dinsa ya zauna yana juyi akan kujera .”
Chapter 81 · 0% Book details