Sashe 19
Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta qara taku biyu ta tsaya gabansa cike da girmamawa tace "amman sir kana ganin ya dace abarta ta cigaba da aiki damu alhalin bata cancata ba ".?oh yanzu ne kikasan bata cancata ba ?yayi mata tambayar a wulakance tare da d'ago kanshi ya tsura mata ido "só .."sorry sir bansan mugun halinta ya kai haka bane shi yasa na .." "enough !ya furta a tsawace yana d'aga mata hannu "ke kinfi kowa sanin ko ni waye ba'a sani haka zalika ba hanani idan nayi niyyar dakatar daita ba sai kince ba ". yana gama fad'ar haka yace "leave my office! da sauri ta juya tana cewa "okay sir. " sorry sir !ta fice."wani dogon tsaki ya sake ja tare da ajiye file din hannunsa ya kai hannunsa daidai habarsa ya rike yana ciza lip's dinsa da karfi ."
shiru yana zaune yana sake sake can yaja tsaki tare da sake mikewa yana zagaye office din "bai ka mata nã bar maryama haka ba dole ne na nuna mata kalata domin na lura yarinyar bata da tsoro shirunsa da qarfafan idanunshi basa firgitata ya kamata na shigar da tsorona cikin zuciyarta kai da kake bukatar ta soka idan ka shigar da tsoronka sai ya kenan ."?mr ata yayi shiru a tsaye kamar gunki yana nazari da tunanin abinda zai yi sai ga d'aya daga cikin wayoyinsa ya d'auki sauti a natse ya juya yasa hannu ya d'auki wayar dake ringing ya soma magana cikin had'addden turancinsa "No it will be possible zuwa gobe zaku samu ok ba damuwa." yana gama fad'ar haka kashe wayar ya ajiye wayar ya cigaba da tunanin maryama ."yanzu me zai faru idan yarinyar nan batayi aikin nan gobe ba ?"yayiwa kanshi tmbyr hannu ya kai goshinsa yana murzawa ahankali "adamcy ka natsu ka bar yarinyar nan tayi aikinta kai ma abinda kayi baka kyauta ba sam sam bai dace ba ,dole ka tunzura zuciyar maryama ya dace ka barta tayi aikinta ."numfashi ya sauke yayi taku biyu ya zube akan kujera yana kallon saman office din wani murmushi dole ya bayyana akan fuskarsa yana cewa zuciyarsa "duk duniya ke kad'ai ce macen da zata kawowa adam rainin hankali ya barta ta kwana lafiya ."
A matukar gajiye maryama ta qarasa gida , ga tarin gajiya ga 'bacin ran mr ata bata iske umma a parlour'n ba sai dai taji alamu tana kitchen dan haka kai tsaye d'akinta na bangaren umma ta shiga ta ajiye jakar aikinta tana sauke numfashi sannan ta shiga bayi ta dauro alwala ta fito ta gabatar da sallah la'asar byn ta idar ta fito zuwa parlour inda ta iske umma zaune tana gyara efo,ta samu guri ta zauna acikin daya daga cikin kujerun parlour'n tare da yi mata sannu da gida "umma ta amsa cike da kulawa maryama ta yi shiru gbdy ta kasa yin komai hatta aikin da ta kan taya umma idan tana gida bata yi yunkurin yi ba bare wani aikin mr ata wanda take jin a yanzu bata da lokacinsa." umma ta kalleta a tsanake tana nazarinta sai dai bata ce mata komai ba yayinda maryama ke kukan zuci zuciyarta na mata zafi da qunci. gashi bata da damar nunawa saboda yanzu ne umma zata fita shiga tashin hankali shiyasa tayita danne quncinta ita kad'ai."
ganin idan ta cigaba da zaman falon umma zata fahimci damuwarta dan har ta fara tambayarta da kwayar idanunta yasa ta mike ta koma d'aki ta kwanta tana danne damuwarta batayi cikakken minti goma ba umma ta kirata ta fito jikinta a sanyaye ta tsaya tmkr wata mara lafiya "lafiyarki kuwa tunda kika dawo na ganki wani iri meke faruwa dake ?"ahankali maryama ta nuna wa umma bata da damuwar komai yanayin aiki ne "amman shine zaki shige d'aki ki zauna ke kad'ai ga "? ba zama nayi ba na d'an kwanta ne ,"kwanciya adaidai wannna lokacin da magriba ta karato ?shiru maryama tayi dan yanzu kam bata da abun cewa ba umma ta tsura mata ido kafin ta cigaba da magana "ni nasan kina da damuwa yau kina dai son boye min ne ."
"Allah umma babu wata damuwa kawai dai yanayin aiki ne babu dadi ta fad'a tana zama kusa daita umma ta mike ta shige kitchen batare da tace mata komai ba dan tasan lallai akwai abinda ke damunta maryama umma ta fito rike da wata roba ta cigaba da aikinta yayinda maryama ta dan saki ranta kad'an tasa hannu suka cigaba da aikin tare da umma tun umma na saka mata ido domin son sanin damuwar maryama har ta sake domin dai ta fahimci babu komai din yanayin aikin ne kamar yadda ta furta abinda umma batasani ba shine kowace second da dare ke karatowa tashin hankali ga maryama domin kuwa damuwarta qaruwa sukeyi duk lokacin data tuna yanayin data baro mr ata da yanayin tashin hankalin some ta biyo dashi sai taji zuciyarta ta buga da qarfi .sai hawaye ya cika idanunta da sauri take dannesu ."
Hannunta ta cire ta kwantar da kanta kan hannun kujera ta shiga duniyar tunani had'uwarta da mr ata gobe shi yafi komai gigitata matukar tsoronsa take ji bata san yaake take samun kwarin gwiawar musayar yawu dashi ba,anya kuwa zaki aiki gobe ?"tayiwa kanta tmbyr "no bazan je aiki gobe ba gara nayi zamana "to me ke nan kikayi ?ai kin sake qarawa kanki sabon laifi kiyi qoqarin ki qarasa masa aikinsa idan Allah ya taimakeki kafin gobe zai huce kai maryama karki je wannan mutumin bashi da kirki sai ya wulakantaki " zuciyarta ta gargadeta mikewa tayi tsam ta shiga d'akinta ta shig toilet ta kunnawa kanta ruwa tana qoqarin jan numfashi da karfafa zuciyarta karta yankewa hukunci kin zuwa aiki gobe dole itace qarama kuma dole itace zatayi hakuri da duk wani abinda zai yi domin ta samu damar cigaba da aikinta cikin salama ."
Karfe shida daidai ya mike ya soma tattara abubuwan amfaninsa ya fito domin wucewa gida
Bayan sallar isha' i bayan yayi wanka ya sanya gajeren wondo da farar riga ya kwashi wayoyin kasuwancinsa guda biyu ya fito zuwa parlour qasa qafafunsa sanye cikin wasu hadadden silipas farare sol ga qamshin turarensa red na tashi ta koina a sansar ajikinsa kai tsaye dinnig ya nufa ya ja kujera baya kad'an ya zauna yana daddana wayarsa daya . yana zaune saman dining dayar wayarsa ta soma ringing ya d'auka ya duba yaga mai kiran mutanen da suka bashi aiki ne dan hk ya manna wayar a kunnensa tare da yin shiru yana sauraran mai magana "."ai nace maka it will be possible tomorrow zuwa 11 am haka I think komai yayi ready okay yana gama fad'ar haka yayi discounting din kiran ya soma neman layin maryama kira biyu yayi mata bata d'aga ba har zai hakura dan bai saba 'bata lokacinsa akan kira ba da zarar yayi kira d'aya baa d'auka ba shikenan zai hakura sai dai a biyasa ."
Amman wannan karon sai ya tsinci kanshi da kasa hakuri ya cigaba da kiranta ai a karo na hud'u ne ta dauka batare da sanin ko shine mai kiran ba"Slm alaikum ta furta cikin sanyayyar muryarta mai matukar sanyi da ratsa sansar jiki "shiru yayi yana jin yadda sautin muryarta ke saka bugun zuciyarsa na qaruwa fiyye da kaida yayinda kowace jijiya dake jikinsa ta natsu tana amsar sakonni daga muryarta wani irin shauki soyayyarta ne ke fizgarshi bai san sanda ya kai hannusansa daya daidai saitin qirjinsa ya fara shafawa ba daga can bangarenta ya sake jiyo sautin muryarta "hello wake magana ?ta sake furta muryarta cike da rauni hannunsa daya ya cire daga qirjinsa ya kai daidai tsakankanin dogon hanshinsa zuwa goshinsa sai da ta sake maimaita hello sannna ya fixgo magana da kyar yace "hello !sai kuma yayi shiru yana jin wani irin mummunar faduwar gaba ".
"An kira mutun kuma anyi shiru dan Allah wake magana ina son na kwanta bacci ." sauri ware idanunshi yayi sosai tamkar tana gabanshi "wato ma ba aikinsa bane agabanta bacci zatayi? ahankali ya kalli agogon wayarsa yanzu tara zata buga "idan mutun bazai yi magana ba ni gsky zan kashe wayata." ya lumshe idanunshi yana furzar da iska mai zafi yayinda sonta ke sake huda zuciyarsa dama gangar jikinsa tana cikin haka sai ga umma tace "ke kuma da waye ?"wallahi umma kirana akayi tun dazu na d'auki kiran amamn tun daga hello basake cewa komai ba" muga number ko irin daya ce da wacce ake kirana ayi shiru."
maryama ta sauke wayar a kunnenta tare da katse kiran yayinda umma ta qarasa inda wayarta take ta dauko ta dawo kusa daita ta mika mata wayar "umma ba number daya bace ."to Allah ya kyauta amman babu dadi a dinga kiran mutun ayi shiru ni yanzu ma yanke shawarar bazan sake daukar kiran layin ba koma Kiyi min blooking din layin na huta inji cewar ummah "uhm umma ki barshi kawai idan mai shi ya gaji ya daina kiranki tana rufe baki wani kiran ya sake shigowa wayar maryama the same number daaka kirata ,da kamar bazata dauka ba sai kuma tayi tunanin ta dauka idan baa yi magana ba ta kashe wayar gabad'aya dan haka ta dauka tare da sallama sannan tace hello wai wake magana ne ?"
A zafafe yace "zakice baki gane mai magana ba ?"ni gsky ban gane mai magana ba hassalima ban san number ba bare muryar mai magana "okay kina magana da mr ata "what !? ta fad'a tare da zaro ido waje jikinta na d'aukar rawa daga haka bata sake cewa komai ba ta katse kiran jikinta na wani irin rawa "tabbas muryarsa ne" shikenan na rasa aikina inna lillahi wa inna ilaihi rajiun umma ta matso kusa daita ta zauna akan hannun kujerar da take zaune tana tambayarta "wani aikin zaki rasa ?cikin kuka ta girgiza mata kai tana saka hannu ta rufe bakinta saboda wani kukan da yake sake kufce mata.