← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 111

Sashe 21

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shiru mami tayi tana rike da hannunta tana nazarinta “ki dinga tausayawa kanki maryam ,ki duba halin da kike ciki komai zai iya faruwa dake “ina tausayawa kaina mami bansan me yasa na kasa cire damuwar nan araina ba.” ta fad’a jikinta na d’aukar rawa “dan allah maryam ki ciresa gabad’aya aranki saboda muna tsananin bukatarki da abinda ke cikinki a raye “mami yaya baya sona baya son cikin da nake d’auke dashi na d’auka zai d’an sauko ko dan cikin jikina “shine ya fad’a miki haka ko kuwa hasashenki ne ya fad’a miki haka ?cike da sheshekan kuka tace “mami yanayinsa ne ya nuna min haka “ki rabu dashi ke dai kiyi fatan ki rabu da cikin lafiya “ta kalli mami ido cikin ido tace “mami ina ji ajikina mutuwa zanyi “gaban mami yayi wata irin fad’uwa tana sake damke hannunta cikin nata tace “in sha allahu mryam bazaki mutu yanzu ba kima cire wannan zance aranki nasiha da kwantar da hankali mami tayita mata tana karfafa mata gwiwa har taji zuciyarta ta d’an yi sanyi .”

Cike da natsuwa mr ata ya dawo parlour’n yana cincin magani har lokacin maryam na zaune tare da mami inda mami ta tsiyaya mata sobo a cup ta mika mata ko kallon inda suke bai yi ba kai tsaye hanyar step ya nufa har yayi taku uku ya jiyo sautin muryar mami ta doke dodon kunnensa “adamcy !”cak yaja ya tsaya batare daya juyo ba, kusan second biyar yana tsaye har sai daya sake jiyo murya mami “kana jina fa ka wani tsaya ni zanzo na sameka ko me kake nufi ?”ahankali ya juyo ya zuba hannuwansa duka cikin aljihunsa ya soma takowa zuwa inda suke batare daya kalli inda mrym take zaune tana dubansa ba “ka samu waje ka zauna .”ta nuna masa opposite din kujerar da take zaune babu mutsu ya zauna yana duban yatsun hannunsa “.

Parlour’n ya d’auki shiru baka jin motsin komai sai na tv da ac dake aiki acikinsa sai kuma saukar numfashin mrym dake fita da karfi tana kallonsa tana jin tsantsar soyayyarsa na sake hud’a zuciyarta bayan soyayyarsa da take ji har da tsananin shaawarsa kamar taje ta kwanta ajikinsa ta rungumesa tsam tsam ajikinta “adamcy baka ga maryam bane ?”uhm na ganta sweetheart !amman shine kayi uwar watsi daita ?“to me zanyi mata sweetheart ?”ni kake tmby me zaka mata ?”kai bakasan abinda zaka mata ba ?”mace na d’auke da cikinka tsawon wattani yau lafiya gobe babu amman ka ganta kayi kamar baka ganta ba ko bazaka ce mata komai ba ai ko dan cikinka dake jikinta ka …”no sweetheart ! yayi saurin katse mami cikin ‘bacin rai “ sai daya furzar da numfashi mai zafi kana ya cigaba da magana cikin zafin rai “ba cikina take dauke dashi ba sai dai cikinta “ya fad’a yana tsaida kallonsa ga maryam din “.

maganarsa ta daki kunnuwan mrym sannan ta wuce har cikin zuciyarta wanda ya sake kunno mata damuwarta da take ta qoqarin dannewa acikin zuciyarta “bance ina son na haihu daita ba shiyasa bana bukatar wani ciki daga gareta wannan cikin ba nawa bane nãta ne har abada kar wanda ya sake dangantani da cikinta “sharrrr…”sai ga wasu hawaye masu zafi sun zubo mata akan kuncinta ahankali ta fara rera kuka mai ban tausayi fuskarshi ya daure sosai “ban san ma me yasa ta kwaso jiki tazo ba “kana hauka ne ?to wallahi bari kaji baka isa ka hana mrym zuwa inda muke ba dole mrym ta shigo cikin gidan nan “well tazo wannan ba damuwata bace da zuwanta da rashinsa duk d’aya ne a wajena maganganu marasa dadi ya dinga fad’awa mrym mami dai a qarshe tayi hakuri ta danne zuciyarta tasa masa ido batare data qara cewa komai ba amman adame take sosai game da lamarin adamcy mutun Kmr sheid’an bai da yafiya kuma abu baya wucewa a wajensa .”

mrym ta sake kallonsa taga har lokacin ita yake kallo yana sake murtuke fuskasa byn ya gama ya mike ya nufi hanyar step yana cewa “sweetheart sai da safe .”
Mami tayi masa banza tana qoqarin gogewa maryam hawaye . sauka maryam tayi daga kan kujerar da take zaune zata zauna kasa kan tayis mami tayi saurin rikota”a’a maryam muje d’akina taja hannunta suka nufi d’akinta tana rarrashinta ahankali mami ta zaunar daita akan gado tana shafa bayanta tana mata sannu amman ita bata wannan take ba kukan tausayin kanta kawai take da abinda Ke cikinta mami ta janyo pillow tasa mata abayanta tana sake rarrashinta sai data ga sautin kukanta ya ragu sannan ta fice daga d’akin zuwa na ata byn fitar mami maryam tayi kuka sosai tmkr ranta zai bar gangar jikinta .”

Tana zauna shiru tana kallon saman d’akin kukan abinda ata yayi mata a yanzu ne ko kuma na tashin hankali da zata shiga anan gaba ne idan ta haihu take yi batasani ba ?tayi bitar maganganun ata tana son tayi placing dinsa a scale daidai da rashin daidai a iya fahimtarta tun suna yara tasan yana da mugun kafiya da muguwar zuciya sune ma manya flaws dinsa kuma har yanzu da girma yake zuwan masa bai rage komai ba .”tasan tunda yace bai son cikin tasan komai zaayi ko sama da kasa zasu had’e bazai qaunaci cikin ba .ita kuwa me tayiwa rayuwarta haka?“ta cutar da kanta da abinda Ke cikinta da tasan zata kasance a cikin wannan tsaka mai wuya din data hakura bata kusamcesa ba ”

Bangaren ata kuwa yana zaune a d’akinsa ya natsu acikin kogin revenge ,yadda har yana qoqarin yayi lossing kansa “bazan ta’ba karbar cikin jikinki ba wannan shine hukuncin da zan miki ta yadda a gaba idan an sake halittoki a duniya bazaki sake reaping din wani ba .”da sauri ya kalli kofar shigowa mami ce ta shigo ranta a matukar’bace ganin itace ya sauke naunayen ajiyar zuciya yana ciza gefen lips dinsa ta nunasa da babban d’an yatsanta “adamcy ka kashe ka huta gbdy tunda kafin bukatar haka “ ya d’ago idanunshi ya kalleta kawai “eh gara ka kasheni kafin naga mutuwar mrym “to ni sweetheart meye laifina ne ?duk abinda nayi akan gskyta nake yarinyar nan nace banso kin matsa na hakura na rungumeta as ending tayi raping dina har yau ina kan shan magani sanadiyyar pills din datayi min amfani dashi” bayan shi dumu dumu na kamata da tukunyar tsafi yau datayi nasara akaina me zaki ce ?mami tayi shiru tana dubansa “ tabbas ya fita gsky .”dan ita kanta taji ciwon abun bare shi to amman yane zatayi maryam dolenta ce bata da yadda zatayi daita .”?

Zazzafan numfashi ya fesar “taya zan iya yafe mata sweetheart bare naso abinda tayi ta’adanci wajen samunsa ?”wallahi sweetheart matukar na riga wannan yarinyar mutuwa bazan yafe mata ba ,gara ma kiyi mata fatan mutuwa watakilla zan iya yafe mata idan bata duniya.” jikin mami yayi mugu mugun sanyi “hankalinta yayi matukar tashi cike da tashin hankali ta cigaba da mgn “babu wanda ya wuce qaddara adamcy wannan alamarin yana cikin qaddaearku .sannan kowani dan adam mai laifi ne “haba sweetheart me yasa wasu lokutan kike kin gsky ne ?wannan qaddara ne ko tsabar iskanci ko son rai ?”qaddara ne adamcy “no no!! sweetheart iskanci ne kawai “ta matso kusa dashi ta zauna tare da kamo hannunsa cikin nashi “munji munyi laifi ka zama mai yafiya domin Allah da kanshi yana son bayinsa masu hakuri ni kuma ina son adamcy nah ya kasance acikin jerin mutane da allah yake so dan Allah ka yafe mata kodan halin da take ciki .”

numfashi ya sauke sannan yace naji zanyi tunani akai daga hk bai sake cewa komai ba ya runtse idanunshi .”na kawo maka abincin nan ne ?”anya sweetheart abincin nan zai samu shiga ? bari naje na kawo maka ko kad’an kaci bai ce mata uhm ba bare uhm har ta fice byn wasu mintuna ta dawo d’akin daya daga cikin masu aikinta na biye daita mai aikin ta ajiye tray ta qara gaba yayinda mami ta zuba masa abinci sai da mami ta matsa masa sannan ya fara ci bawani abinci kirki yaci ba ya ture plet din gefe ahankali ya maida bayansa ya jingina da kujera da yake zaune akai tare da zamowa kad’an yana duban maminsa itama mami shi take kallo “ba dai har ka koshi ba adamcy ?”ya d’age mata girasa d’aya “ko na hado maka tea ne ?dakin ya dauki shiru har tsawon minti goma batare yayi ko tari ba sai da mami ta sake yin mgn yace mata baya bukata gajiya mami tayi da zaman ta fito ta koma dakinta ta cigaba da rarrashin mrym .”

Ranar kwana marym tayi batayi bacci tana juyi da tunanin matsayar rayuwarta yayinda maganganun mr ata yake barin kunnuwanta da zuciyarta su huta “bance ina son na haihu daita ba shiyasa bana bukatar wani ciki daga gareta wannan cikin ba nawa bane nãta ne har abada kar wanda ya sake dangantani da cikinta tayi wani irin juyi da karfi wanda yayi sanadiyyar da yar cikinta ta qara tokare mata qirjinta ta runtse idanunta gam .”haka ma mami bata runtsa ba da zarar taji motsinta zata mike ta tamvayeta ko akwai abinda take bukata ko akwai inda ke mata ciwo .”washegari tun da sassafe mr ata ya fice daga gidan ya wuce office wanda sai lokacin maryam ta samu damar runtsawa . bai jima da fita ba sai ga yaran mami gbdy tare da nana hauwa’u sun taho daita gida daga hospital kai tsaye d’akinsu aka wuce daita wanda ya sha gyara sannan suka dawo parlour’n mami inda mami take sheida masu abinda adamcy ya fad’a mata akan mrym daren jiya “kalmarsa sunyi tsauri dayawa akan mrym yace “bazai yafe mata ba nasani mrym tayi kuskure amman yayi hakuri mana haka .”
Chapter 21 · 0% Book details