← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 111

Sashe 103

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Maryama nasan kince wani abu” tai shiru kawai” ina jinki! “nifa babu abinda nace kawai dan dai kana jin haushina ne yasa kunnuwanka suka jiyo maka kamar nace wani abu “keep quiet bansan me yasa kika rainani over ba ,kisani na d’auki aikina da mahimmanci ban d’aukesa shirme ba sannan idan kinga zaki bimu fine idan kuma zaki cigaba da zama anan gud ya rage naki.” dumm taji gabanta ya fad’i “daman yace tazo aiki ne dan kawai ya samu damar wulakantata kome ?”tayi mugun zuba masa ido tana dubansa ya juya a natse ya fuskanci ma’akatan sa “guys ina fatan zakuyi aiki dani kuma zaku bini duk inda na bukata?”.sure sir okay back to work ”yana gama fad’ar haka ya wuce ya fita ko kallon inda take bai yi ba dan har lokacin haushinta yake ji kamar yadda ta fahimta Itama ko kallonsa batai ba sai dai abinda yayi mata ya dameta matuka idan tai bleming kanta akan saka bakinta cikin maganarsa ko zuwanta aiki sai kuma ta dawo ta bashi laifi wulakancin da yayi mata .”

Jiki a sanyaye ta bude littafi tana duba zane tana zance zuci “ya ma bari mutun yayi magana yaji me mutun zai ce amman yaki ya hau mutun da matsefa ,masefaffe kawai abinda ya kamata yace min me nake qoqarin cewa .?”Ko me yasa zai daddakemu daga nan zuwa wani guri da alamun inda zai maidasu din akwai nisa sosai may be shiyasa yayi masu kyautar mota amman ita ya hanata ko ita uwar wa ta kashe masa da zai bawa kowa ya hanata ?”tayi maganar tana jan tsaki a fili ita dai gasky zata samesa taji inda zasu koma matuqar akwai nisa daga unguwarsu bazataje ba ,gara ta hakura da aikin gabad’aya ta huta tunda daman akwai sharad’i akanta.”
ahankali ta soma qoqarin mikewa tsaye tana gyara zaman hijab dinta sai ga madam some ta shigo “yauwa maryama latest desing na royal palace zaki zana “okay ma ,zuwa yaushe ake bukata ?”eh to ko zuwa gobe da safe haka “okay ma zanyi qoqari in sha allahu .”

Madam some ta juya ta fita ta shiga wani office din ita kuma ta nufi office din mr ata bata tsaya neman izini ba ta fad’a kanshi na sunkuye yana duba wani file din zane sai dai nan take ya fahimci Itace ta shigo masa office babu neman izini,a natse ta qaraso ta tsaya a gabansa tare da goya hannuwanta duka abaya tace “sir !”ya d’ago kanshi ya had’e hannuwansa waje d’aya ya dafe ha’barsa tare da zuba mata ido .”amm daman nazo ne nasan inda zamu koma aiki idan wajen yayi min zan biku .”
“Idan kuma wajen bai miki ba fa ?”zan ajiye aikin gabad’aya”.ta bashi amsa kai tsaye batare da wani shayi ko ‘bata lokacin ba “okay lekki zamu koma”. “lekki!?ta furta a fili tana d’an ware idanunta ya gyad’a mata kai yana lumshe mata ido “ammm gaskiya Ina ganin zan ajiye aiki dan …”sai kuma tayi shiru ta kasa cigaba da magana “uhm Ina jikin dan me ?”dan na samu wanda zan aura mgnarta ta daki kunnuwansa ta wuce har cikin zuciyarsa tamkar ta soka masa mashi haka yaji maganartata a kahon zuciyarsa “yayi shiru kawai yana kallonta wanda kallon nasa yasa ta sunkuyar da kanta kasa dan bata son wannan kallon nasa mai firgitarwa .”

ahankali ya motsa lip’s dinsa yace “daga yaushe zuwa yau she ne har kika samu wanda zaki aura ?yayi mata tambayar kamar zai yi kuka ta d’ago kanta a natse har lokacin ita yake kallo fuskarsa a had’e “daga sunday wani d’an uwa zan aura”ta fad’a masa tana son tabbatar da abinda yake boye wa aransa,ya lamgwabar da kai gefe kamar abun tausayi “me yasa ni bazaki aure ne ba ?”yayi mgnr acikin ransa yana jin wani irin tuttukin bakinciki mara misaltuwa ahankali ya sauke hannunsa ya mike tsaye ya dawo inda take tsaye ya tsaya a gabanta yana lissafin abinda zai yi kamar bazai yi magana ba sai kuma ya motsa lip’s dinsa “ni me yasa bazaki aure ni ba sai wani dabam “.?

“Saboda baka sona!”.
“Saboda bana sonki ?” yes of course baka sona shi kuma yana sona kai kuma kace taimakona zakayi kaga gara na auri mai sona ba mai taimkona ba ,dan Kai daman kafi qarfin aurena bare km tun kafin aje koina ka fara da taimakona zakayi “naji but shi da yace yana sonki ke kuma kinji aranki kina son shi ko kawai zaki auresa ne dan kina son kiyi aure?” ta gyad’a masa kai tana cewa “eh to bawai ina son shi bane amman zan auresa dan naji ya d’an kwanta min arai nan take moond dinsa ya sake canzawa ya shiga kai kawo a filin office din .”Sosai tai mamaki yadda ya shiga damuwa “kar dai da gaske mr ata sonta yake kamar yadda ta fara tunani kamar yasan tunanin da take kawai taga ya dawo gabanta daf daita ya tsaya yasa hannuwansa ya rike kafad’unta yace “karki ga na shiga wani hali kiyi tunanin Ina yin shishigi ne acikin rayuwarki ,jikina ya bani baki son auren nan kuma banason ki auri wanda baki so kasancewar akwai illa saboda ni nan hakan ta faru dani kuma babu abinda auren ya haifar sai zallar damuwa ki manta da wannan ni ki aureni “

Tayi shiru tana tunani wannan Iko nashi “gaskiya ni dai gara na auresa zai fiyye min kwanciyar hankali akan na aureka shi mutun ne mai sauki hali mai kyakkwan muamula da mutane mutun ne mara girman kai da sanin kimar mutane mutun ne mai…”ai kafin ta qarasa mganrta sai Jin saukar mari tayi akan kuncinta sosai ta firgita ta dafe kuncinta ta tsura masa ido shima ita yake kallo ranshi a matukar’bace hawaye ya zubo mata akan fuska yace “kina hauka ne ko kuma kin fara shaye shaye ne ?”a gabana kike yabon wani katon banza har kike kuranta shi ?bayan ya gama maganar sai kuma yayi shiru ya juya mata baya yana fesar da iska yana duban hannunsa da ya mareta dashi “oh my god why adam ?”me yasa ka mareta?”yana cikin wannan halin yaji motsin takalmanta alamun zata bar office din juyowa yayi da sauri ya rungumeta tsam tsam ajikinsa gabansa na fad’uwa nan take jikinta ya d’auki kyarma amman ta kasa kwacewa yadda yake ji ajikinsa haka take ji ajikinta kamar an jona mata wutar lantarki cikin sanyi murya yake magana “ki fahimceni maryama banason ki aure wani ,ba wai Ina nufin karki yi aure bane a’a banason ki auri wanda bakya so ne .”

Wani haushi da bakinciki ya dinga shigarta yana mamaye ilahirin jikinta domin alokacin tayi tunanin zai ce mata shi yana sonta ne dan tafi son ya furta mata cewar yana sonta ba wai ta auresa batare da tasan matsa yinta ba kuma tayi Imani idan ta auresa a haka duk ranar data bata masa rai kai tsaye zai wulaqantata .wani haushi ya sake kamata sbd bai ce yana sonta ba ya wani rungumeta yana faman sauke ajiyar zuciya tamkar jinjirin daya kwana uku batare daya sha nono ba tana fama da radadin marin da yayi mata da rashin furta mata yana sonta bare ta samu damar aurensa ,ya wani rungumeta yana mata maganar banzar ko ina ruwan shi da zata auri wanda bata so oho ?”

ahankali ta soma mutsu mutsun kwacewa ya juyo daita suka fuskanci juna ya sake matseta yayi mata kyakkywan riko yana cewa“haba maryama me yasa kike jin cewar zaki iya auren wani ki bar ni “zan fi samun natsuwa da kwanciyar hankali ta bashi amsa da haka tana sheshekar kuka “bazaki samu ba maryama bazaki iya rayuwa da wani ba ke har yanzu baki fara Jin alamun cewar kina son adam ba ?”wannan kam gakiya ne ta fara Jin son shi har ma tana jin cewar bazata iya kwanaki dayawa batare datayi magana dashi ba domin duk yadda yake mata kallon tana son shi ashe abun da gaske ne lallai zuciyarta ta tafka mata babban kuskure domin dai son shine kuskure na farko da zatayi arayuwarta.”

“Ya zareta ajikinsa ya riko hannunta cikin nashi yana murzawa ahankali yace “maryama me yasa bakya tausayawa kanki ?”tayi saurin zare hannunta daga nashi tana yarfarwa kamar wanda wuta ta kona saboda wani blood rush da taji ya taso mata daga hannunsa zuwa nata cikin second d’aya ya zagaye duk ilahirin jikinta cikin tsarke war murya tace “me ya sameni da zanji tausayin kaina?”sannan dan nace zan auri wani ne yasa ka mareni ?”ya lumshe mata idanunshi ya bud’e yana kallon yadda take yarfe hannunta tace to “nasan kana da komai da duk wata mace zata so aurenka amman ni maryama bazan aurenka kuma kome zakayi gara na auri wani akan dai na auri mutun irinka “ bai san sanda dariya ya subuce masa ba, ..ya mugun tsareta da ido sannan yace “kamar zaki iya!” ta d’an tsaya tana kallonsa Tana assessing maganarsa yana kallonta with a broad smile akan fuskashi ta d’auke kanta tana lissafi “kamar fa ya gane ta fara son shi idan kuma bai gane ba tabbas cigaba da tsuyuwarta a wajen zai iya tona asirin zuciyarta bugu da qari ga tsayuwa na neman gagararta dan haka ta juya ahankali zata bar masa offie din taji ya riko tsintsiyar hannunta tare da fixgota zuwa jikinsa ya rungumeta yana jin wata irin tsantsar soyayyarta na ratsashi “
Chapter 103 · 0% Book details