← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 111

Sashe 4

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikin kankani lokaci sababbin ma'aikatan suka hallarar a cikin officer dinsa kowannensu rike da takardar zane ya yunkura ya mike da kyar ya zagayo daya bayan daya ya dinga amsa yana dubawa sai dai gabadaya babu wanda yayi masa acikin zanensu . yaja qaramin tsaki ya tsaya ya rike kugunsa yana aika masu da wani mugun kallo mai tattare da abu biyu ,abu na farko damuwar da yake ciki abu na biyu kuma takaicin basu yi masa abinda yake so ba "wannan shine iya kwarewarku?shiru sukai gaba dayansu zuciyarsu cike da matsanancin tsoro kallonsa kawai yana firgita da mutun bare kuma maganarsa cikin zafin rai ko waye kai sai kaji fargaba "ban d'aukeku aiki dan biyaku batare da kun iya komai ba ,na daukeku né saboda kunce kun iya wannan shine karshen iyawarku ?ya sake jefa masu tamabyar data sake gigitasu suka ji kamar su falla da gudu amman babu hali ."wallahi duk na daukeku né saboda best design not nonsense ya fad'a a matukar tsawace  ." sannan ya maida idanunshi Kan sactry" some can you see your self ina gwajin da kikace kinyi masu ?"sir duk angwadasu  "most of the...."

"Culmdown ata ! aka fada tare da turo kofar office din ,shiru yayi yana dago tsumammun idanunshi zuwa kofar shigowa ganin sultana yasa ransa ya qara baci ,ya lumshe idanunshi yana furzar d iska mai zafi  daga bakinsa fuskan natashi babu annuri ko daya sultana ta qaraso har gabansa hannuta rike da farar takarda "nazo da abinda kowa ya kasa kalli nan kaga" ta fada tana jujjuya masa jiki tare da kai takardar gabansa "kalli irin kwarewata nasan wannan ne exactly abinda kake bukata? shiru yayi zuciyarsa na wani irin tuttukin bakinciki "Listing !this is my last warnin karki kara shigo min office batare da kinyi knowking ba  sannan idan zaki kirani kisa girmamawa call me with sir ..."yana gama fad'ar hk ya juya  da sauri zai barta tai saurin cewa " okay sir !ta fad'a tana masa fari da idanu wanda ko kadan bai girgiza zuciyar ATA  ba sai ma qara tsanarta da yayi "my design ! ta furta cikin salon jan hankali tana duban farar takardar dake rike a hannunta a kaikaice ya juyo ya fixge takarda daga hannunta ya tsurawa zanen tsumammun idanunshi dake cike da tashin hankali yana karewa zanen kallo yayinda ta cigaba da juya  masa jikinta tana murmushi tana kallonsa sai dai gabanta banda dukan uku uku babu abind yake ."

Wani irin dariya ne yaso kufce masa saboda ganin abinda take takamar ta zana awajensa shi da  jagwal gwalo bashi da wani bambamci amman ya danne  dan dariya bata kamace masa ba a halin da yake ciki sai dai  kana kallon fuskarsa zaka fahimci abun yaso bashi dariya wani irin sanyin  dadi ne ya mamaye gabadaya ilahirin jikinta ta sake gyara tsayuwa tana kallonsa tana jiran taji me zaice ."a natse taga ya shiga matsé takardar har ya matseta  gabadaya yana  mata wani irin mugun kallo sannan ya kalli inda abun zuba shara yake ya cilla takardar aciki ."
sake fuskantata yayi cikin fushi yace "wa kike da suna sultana ko me ,wannan shine sakamakon abinda kike zana yana gama fadar haka ya juya ya soma tafiya zuwa mazauninsa wani irin numfashi ta sauke da karfin gaske tana kiran sunansa "ya Adam !a matukar tsawace yace "me zanyi miki ?wato burinka ka wulakantani a bayyanar  nasi ba ?ta sauke numfashi tana furta why ?Kina san kisan ina da ikon wulakantanki ko bani da ?tayi shiru tana dubansa "to ki daina shiga tsabgata ki kama kanki akan komai nawa ki tsaya iya inda aka ajiyeki stay a way from me sultana oya leave ..."ya fad'a yana nuna mata kofa  tare da zabga mata harara cike da in ina ta kira sunansa "ya..ya Adam"i saida leave ya sake nuna mata hanyar fita ."

"Some ai na rigada na fad'a miki ki dauki kwararrun masu zane ba muna zane ba gabadayan ni banga na dauka anan ba "ya fad'a yana jan dogon tsaki  "sir kayi hakuri kowannensu yana ta qoqarin yaga ya zana abinda zai burgeka "shiiii! "ya fad'a a tsawace "common design sun kasa abinda zai fi ki sallamesu kawai gabadayansu a nemo min wasu "kayi hakuri sir amman  me zai hana a nemi maryama hussein  nasan zata maka abinda kake ...,"stop ! ya tsadata  a tsawace just stop some karki qara kuskure ina wata magana dabam kina sako wannan yarinyar ko kin fahimceni ? tai saurin gyada masa kai "bana bukatar wannan yarinyar kuma bazata sake tako kafarta zuwa cikin wannan kamfanin ba ,bama wannan kafanin ba har kowani kafani da suna aiki ita da yin aiki har qarshen rayuwarta ."

Bayan ya gama mgn ya numfashi yana kallonsu daya bayan "ku saurarani da kyau zan sake baku lokaci "yarinyar ce zaune a lap cike da natsuwa idanunta na Kan farar takarda tana zana doguwar rigar amarya da riga da wondo na ango  sosai tayi concentration gaban doguwar rigar tana da shape daga gaba yayinda bayan rigar ta sauko wanda ya hade da dogon gashin mace yana bayani yana kallon maryama cikin kwayar idanunshi cike da matsanancin qaunarta ,lumshe lumtsatsun idanunsa yayi "wannan shine tsarin zanen da nake so ku dinga bin komai daki daki tare da tsare fatan kun fahimceni ?gabadaya suka hada baki "yes sir ."oya maza maza aje ayi daya daga cikinsu ya kallesa yace  " kayi hakuri sir inshaallahu zanyi maka abinda kake so "very good ya fad'a yana tare da komawa  mazauninsa ya zauna yana jujjuyawa akan kujera sannan ya dauko cup din glass cup dake cike da ruwa ya kai bakinsa ya kurba ya ajiye ya daura hannunsa akan hannun kujera yana cigaba da jujjuyawa."

Bangaren sultuna kuwa office dinsu ta koma ta cike da tsananin tashin hankali da takaicin abinda ATA yayi mata waya ne a kunnenta tana magana da Aunty abida "kinga wulakacin da yayi min kuwa aunty agaban ma'aikatansa bayan ya gama  wulakanta zanen dana sha wahala na zana a gaban kowa wallahi bazan dauka ba Aunty bazan jura wannan wulakanci ba" nasan halinsa shegen gaske ne  zai iya aikata abinda yafi wannan ki daina damuwa abinda ya kamata kiyi  kokarin shine ki fara daukar hankalinsa ...amman Aunty .."No ki tsaya kiji abinda nace Kiyi shi zakiyi karki min mutsu dan duk ina yin wannan abun ne saboda jin dadinki ...."

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 2

Sultana na gama wayar da take idanuwanta suka sauka akan zanen da maryama tayi akan table , shiru tayi rike da wayarta tana duban zanen zanen ne mai Shege kyau da d'aukar hankali. zanen mace ce sanye da kayan weeding gwan sosai maryama ta kwantar da hankali ta zanata had'e da zana gashin kanta har gadon bayanta tamkar dai mutun sak wani irin murmushin jin dadi ya bayyana akan fuskar sultana cike da jin dadi tasa hannu ta d'auka tana cigaba da kallon zanen "wannna ai irin zanen da ya adam yake bukata ne sak "tabbas idan yaga wannan zanen zai ji dadi sosai bari na kai masa nace ni na zana "ta juya da sauri ta nufi hanyar office dinsa alokacin da Kunnensa yake manne da waya yana magana da wani abokin kasuwansa ,yayinda hannuwansa duka ke aikin dadddana keyboard gefensa sectary dinsa ce tsaye rike da wani blue file tana dubawa ."

"Yes !muna da fiyye da abinda tunaninka ya baka ,eh !sosai kuwa akwai abubuwa masu mahimanci akan sakon dana tura maka kayi qoqari ka duba" ya fad'a yana cigaba da aiki can bayan kamar minti goma ya mike tsaye rike da system dinsa ya isa inda sectary dinsa take tsaye yana nuna mata wani sako tare da yi mata qarin bayani yadda yake son kasuwancin ya tafi bai gama rufe bakinsa ba yaji ana magana daga bakin kofa "tare da knowking " ko zan iya shigowa ?.Idanuwanshi dake manne da farin glas ya tsurawa kofar shigowa tare da yin shiru na second biyar sannan maganarsa ta biyo baya "yes !ahankali ta tura kofa ta shigo tana rausaya yana ganinta yaja tsaki ya koma kan kujera ya zauna ya dungule hannunsa duka waje d'aya ya d'aura akan table yana ciza lips dinsa na kasa wani irin numfashi ya furzar mai zafi daga bakinsa ya kawar da fuskarsa adaidai lokacin data garaso qefensa ta tsaya tare da ajiye masa farar takarda a gabansa "ko akwai abinda zaka ce akan wannan zanen ?ta gefen idonsa ya soma hango had'ad'd'en zanen ,a natse ya juyo gabad'aya idanuwan shi suka sauka akan zanen " kaga irin zanen sultuna ba?na sha fad'a maka ina da kwarewa sosai akan zane amman kullum gani kake ban iya komai ba to yanzu dai me zaka ce akan wannnan zanen sir ."?
Chapter 4 · 0% Book details