← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 111

Sashe 46

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Umma ta sakar mata murmushi Allah ya gani tana matukar qaunar maryama kuma taso hada zuri'a da wanna natsattsen yarinya kamarta mai kyakkyawar zuciyata da natsuwa tare da sanin ya kamata amma Allah bai nufa ba, ina ma ace tana da wani d’an bayan sadam , tabbas data sake nema masa aurenta amman haka Allah ya qaddara mata haihuwa d’aya zatayi arayuwarta ,amma ba komi zata cigaba da mata addu'a Allah ya bata miji na gari wanda yafi sadam komai .”sun dade suna tautaunawa har
Qarfe goma da minti goma sha biyu maryama ta mike tsaye tare da cewa “umma bari ma shiga ciki zan d’an yi aiki kafin na kwanta sai da safe “acikin duhun nan zaki yi aiki ?”to ya zanyi umma tunda sunki kawo wutar nan ? nafi tunanin wutar lalacewa tayi dan yinin yau basu kawota ba “inji cewar umma maryama tace “ai yan nepa na abinda ransu yake so Allah dai ya kyauta bari naje dan muddin ina son zaman lafiya da mutumin nan na qarasa masa aikinsa kawai na bashi “to shikenan Allah ya tashemu lafiya maryama ta nufi d’akinta itama umma batá dade ba ta mike ta shige ciki “.

Bangaren mr ata ruwan tea kawai ya sha ya shige bedroom dinsa inda ya soma ya cigaba da neman layin maryama sai dai har wannan lokacin kiran baya shiga hakan nan yaji damuwarsa ta ninku daren ranar haka ya zauna yana tunaninta duk juyin da zai yi tana makale da zuciyarsa da jikinsa sosai yake tsananin buqatar aurenta,domin a yanzu a matse yake tamkar yaci babu “yanzu kai adam kana ganin hanyar daka bullo daita mai bullewa ce agareka kayi aure a boye batare dasanin danginka ba ?ya kamata dai kayi nazari sosai kafin ka aikata haka .”yayi wani juyi ya sake kamkame pillow a qirjinsa yana jin tamkar maryama ce ajikinsa har wani shafa jikin pillow yake yana sake zurfafa tunaninsa .”sannu ahankali bacci yayi awon gaba dashi “yayinda maryama ta baje takardu masu yawa a tsakiyar gadonta ta soma aikinsa daya bata kusan awa biyu ta d’auka tana aiki kafin ahankali ta lalubo wayarta ta kunna tana gama kunnawa kira ya shigo tai shiru tana duba fuskar wayar gabanta na fad’uwa cike da karfin zuciyata ta d’aga tasa wayar a handsfree “kamar dai daren jiya akace “ko ina magana da maryama hussein ne ?”yes itace !”ta fad’a tana kai pencil din hannunta baki tana taunawa .”

“Okay daga kamfanin AGC ne jiya mun kiraki akan kizo da wuri kasancewar akwai aikin da zamu baki inda aka samu matsala jiya ban samu damar zuwa aiki ba sakamakon wani uzuri daya taso min amman in sha Allahu gobe kizo da wuri zan zo na sameki da kaina muyi magana .”wani naunauyen ajiyar zuciya ta sauke sai yanzu ta tuna da jiya an kirata shine ma dalilin zuwanta aiki da wuri da har mr ata ya samu damarta kuma sai yanzu ta fahimci mai kiran kamar muryar sultan ne “kafin tace wani abu dif idon taga ya d’auke”hello mr sultan ne ?hello !”jin shiru yasa ta danna gefen wayar ashe babu caji ne yasa ta mutu gbdy dogon tsaki taja tana dungurar daita akan katifar da take daman nasan haka zata iya faruwa shiysa naki hawa online tun dazu saboda rashin wutan nan da suke fama dashi a unguwarsu tayi yawa .”ahankali ta cigaba da aikinta

Qarfe biyu saura ta kammala komai ta tattara aikin ta zuba acikin jakar aikinta tayi addua ta shafa a gabad’aya ilahirin jikinta ta kwanta kasancewar akwai bacci a idanunta nan take bacci yayi awon gaba daita .”sadaf sadaf ya shigo ta kofar baya d’akin maryama ya fara lekawa ya ganta kwance ta kamkame jikinta waje d’aya tana bacci ahankali ya janyo kofar ya rufe ya nufi d’akin ummanshi ya tura kofar ahankali ya rabe daga wajen d’akinta,kai tsaye hannunsa ya kai inda makunnin wutan d’akinta yake ya kunna bayan haske ya gama haskaka d’akin ya turo kanshi kad’an ya leka tana kwance tana bacci abunta hannunwanta rungume da fream wanda ko bai duba ba yasan hotonsa ne .”gefenta kuma tulin uniform dinsa ne tun daga kan primary har zuwa secondary har ma dana islamiyyar sa .”wani irin bugawa zuciyarsa tayi da mugun qarfi ya soma d’aga qafafuwansa ya shigo d’akin cikin sand’a ya qara taku biyu ya iso zuwa inda take kwance ya tsaya akanta yana kallonta ya sani bai kyauta mata ba hakika mahaifiyarsa bata cancaci haka daga garesa ba ,yayi mata butulci yayi mata muguwar sakayya da wani ido zai kalleta dashi aranar da zai bayyana mata kanshi.”?

zazzafan numfashi ya sauke ya soma tafiya cikin sand’a ya isa durowarta inda yafi tunanin anan zai ga sauran documents din da yake nema dan jiya dayazo ya duba koina a d’akinsa bai gani ba wanda nadia ta kawo masa ba iyasu kawai yake bukata ba akwai wasu masu mahimanci.kafin ya kai hannu ya bud’e sai daya waiga ya sake kallonta tana sauke numfashi ahankali tana sake kwakume hotonsa ajikinsa nan take idanunshi ya ciko da ruwan hawaye cike da qaunar mahaifiyarsa ya d’auke idanunshi akanta ya maida kan durowar ya bud’e ya soma duba abinda ya kawo shi hawaye nabin kuncinsa ‘hawaye ne kawai yake zuba daga cikin idanunshi alokacin da yake tunanin irin qauna da soyayyarta da ummansa ta nuna masa tun yana qaraminsa har zuwa girmansa da irin rayuwar da sukai idan taci yaci zata iya hakura da komai akanshi duk son da take ma abu muddin bai so to itama in sha allahu yafi ranta kallonta ya sake yi ita kadai ce fa ta rage masa a nan gidan duniya gashi ya barta akan wani dalili mara tushe .”

bai wani ‘bata lokaci ba ya ga document din daya kawoshi ya d’auka tare da maida durowar ya rufe ahankali ya dawo gabanta ya tsugunna yana furta “umma nah ina tsananin sonki ,daidai da minti d’aya tunaninki da soyayyarki basu ta’ba barin zuciyata ta huta ba ki ya fé min umma nah Kiyi hakuri umma nah..”ya fad’a yana shafa gefen fuskarta inda ta motsa yayi saurin cire hannunsa ya mike da sauri ya fice yana fita ta bud’e idanunta ta kira sunansa da karfi “sadam ..” gabanta na wani irin fad’uwa .”d’akin ta dinga bi da kallo kafin ahankali tace “ashe mafarki ne”. ta furta tana kallon fuskar fream din hannunta tana shafawa Allah ya jikanka sadam ,allah yasa ruhinka yana aljanna ina tsananin sonka dana amman Allah daya bani kai ya fini bukatarka tana gama fadar haka ta fashe da wani rikitaccen kuka hade kamkame hotonsa tun sanda umma ta farka da sunan sadam abakinta maryama tayi zumbur ta farka daga baccinta.”

da sauri ta shiga kokuwar saukowa daga kan gado ta fito ta banko d’akin umma in da ta iske umma zaune kwakume da hoton sadam tana kuka tana zuba sambatun “ya Allah bana bakinciki da wannan rayuwa, bana bakinciki da hukuncinKa Allah .”
Allah kabani ikon cinye jarabawar wannnan da sauri jikin maryama na kyrma ta zauna kusa daita hawaye na zuba a idanunta ,maryama kuka ummah kuka umma ta kamo hannunta ta damke cikin nata tace “maryama mafarkin sadam nayi maryama ina matuqar qaunar sadam amamn ma rasahi “umma ki daina kuka ki dinga tuna cewar kina dani wallahi zan zame miki tamakar yaya sadam bazan ta’ba juya miki baya ba, nasani maryama “Allah yayi miki albarka a rayuwarki Allah ya baki miji na gari “amen ummah ki bar kukan haka banason kina daga hankalinki in sha allahu sai kinyi alfahari dani bazan tabayi nisa dake ba zan kasance tare dake dan Allah ki daina damuwa kinji, Allah yayi miki albarka data yayan da zaki haifa in sha allahu bazaki dangwama a haka ba ,Allah zai saukaka .”

“Allah zai hadaki da miji na gari mijin da zai rikeki amana mijin da zai qaunace da dukkanin rayuwarsa
ta qarasa maganar tana zubar da hawaye baccin da umma da maryma basu koma ba kenan umma ta mike ta ajiye fream din hannunta a inda yake akan durowarta sannan ta soma tattara uniform din sadam tana hawaye maryama tayi sauri ta kar’ba a hannunta ta maidasu inda suke sannan tace “umma kije kiyi alwala kizo Kiyi sallah in sha allahu zuciyarki zatayi sanyi kai kawai umma ta iya gyda mata sannna ta shige bayi ta dauro alwala koda ta fito ta iske maryama ta shimfida sallaya tazo ta shiga gabatar da nafilflii inda maryama ta fito ta shiga kitchen ta daura mata ruwan zafi shiru tayi tsaye rungume da hannunwanta a qirji kwakwaluwarta na tunani mai zurfi “ita fa data shiga d’akin umma taji kamshin turaren yaya sadam daman idan akayi mafarki da mutun har kamshin mutun zaa iya ji ?”
Sosai kwakwaluwarta ta shiga cajin tunanin jiki a sanyaye ta had’awa umma tea ta kai mata alokacin ummah ta sallame tana zaune tana nemawa d’anta rahma a wajen allah ”

“Umma ga tea ki sha “sannu maryama na gode Kwarai Allah ya shiga cikin lamarinki “Ameen ummah ,cike da tsinkewar zuciya umma ta kar’bi cup din bakinta maryama ta dawo gabanta tana mammatsa mata qafa umma tayi murmushi “kije ki kwanta kinji maryama .ta girgiza mata kai alamun “a’a ni dai dan allah umma ki kwantar da hankalinki kice fa kike bani kwarin gwiwa idan ina ganinki haka walalhi nima zaki rasani da sauri umma ta girgiza mata kai “allah bazai sa naga mugun abu ba in sha allahu sai naga aurenki da ya’yanki sai nã goya ya’yanki da wannnan bayan nawa maryama tai murmushi kawai tana mai sake jin qaunar umm aranta wanda ta dade dasanin qaunarsu daga Allah ne “jin an fara kiran sallah farko yasa maryama mikewa tace “umma bari nasoma aikina dan yau ma ina ganin da wuri zan fita to shikenan Allah ya taimaka ta fice tana janyo mata kofa .”

********
Chapter 46 · 0% Book details