← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 111

Sashe 40

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsumammun danunsa ya ware sosai akansu yana cewa "mintuna goma kacal sun isa ku tattara duk wasu kalamanku masu mahimanci." sarai sun fahimci inda ya dosa dan haka suka taikaita maganarsu kamar yadda ya bugata suka kama gabansa tun kafin yace ya fasa halqallar kasuwanci dasu ."bayan tafiyar bakinsa ya mike tsam ya janyo kujera zuwa gabanta ya zauna tare da ware qafafunsa ,sunyi mugun yin daf da juna ta dan ja kujerar baya kad’an amman hakan bazai hana idan ya sauke numfashinsa taji ba. ganin yadda idanunshi ke yawo ajikinta yasa tayi saurin sunkuyar da kanta qasa natse alokacin daya soma magana a tsanake amamn idan mutun ya natsu sosai zai fahimci cikin tsananin fushi yake "anya kuwa kwakwaluwarki tana da cikakkiyar lafiya kuwa ?" ta d'ago kanta a gigice tana kallonsa "yes !dole na tambayeki dan kin wani tsareni da idanu "ya qarasa maganar yana lumshe mata ido .”

“Ko me ya gani atattare daita yasa zai had’a da wannan mummunar ciwo ?” tabi jikinta da kallo na second goma sannan ta d’ago ta zuba masa idanunta “me yasa zaki fad'a kan mutane ?" Muryarta na rawa tace “wallahi ban sani bane ni ma haka kawai naji jikina ya kama rawa.” taso ta fad'a masa idanunsu ne yayi mata yawa amman sai ta tsinci kanta da kasa fad'ar haka dan batasan me hakan zai haifar ba tunda ta rigada tasan halinsa abu kad’an ke hassalashi "idanun maza yayi miki yawa kina gani bai kamata kiyi aure anan kusa ki huta ba "?tayi shiru tana cigaba da kallonsa yayinda qararrawar zuciyarta na kad'awa da sauri sauri sakamakon kusancin da suka samu na haifar mata da shiga cikin wani yanayi "ya dai kamata kiyi tunani ko sanin cewar ke matar aure ce zai saukaka miki wasu abubuwan ."numafshi ta janyo ta sauke da kyar tana sake sunkuyar da kanta gabdaya ta sake neman natsuwarta ta rasa rawar da jikinta keyi ta qaru ".

“Maryama ki tsaida miji kiyi aure zai fiye miki kina aure kina aikinki , dan bai dace ki dinga kula kowani kare alade da jaki ba "idan dai kema din ba irin hallitarsu gareki ba ."ya qarasa mgnr yana jan tsaki tabi shi da wani irin kallo zuciyarta na tsinkewa idan ta fahimcesa da kyau" idan halittartata ba irin ta jaki kare da alade bace ta daina kula kowa kallonsa take fuskarta da bayananen mamaki “to shi da yake kulata take kulasa fa ?”kenan shima ya kasance d’aya daga cikin abinda ya lissafa kare da alade da jaki ne ?”tayi maganar a can kasan makoshinta ta yadda ko shi da yake zaune a gabanta bazai iya fahimtar komai .ya juya ya d'auki kwalin sigari ya bud’e ya zari d’aya ya kai bakinsa ya kai hannu ya dauki abun kunnawa tana ganin haka ta zabura ta mike ranta a matukar bace ta nufi kofar fita tana jan tsaki da kallo yabi bayanta yana ta'be fuska  "abinda zaki qarasa tsawon rayuwarki daita itace abar gudu ai gara ki fara sabawa daita sannna ya lumshe idanunshi lokacin guda kuma ya budesu yana cewa "ke dawo ki zauna ."!

Maryama taki tsayawa bare ta dawo kamar yadda ya bukata "idan kika  kuskura  kika bar office din nan ki tabbatarwa kanki  kin tafi kenan har abada bazaki  sake da aiki a AGC ba  ".cak taja qafafuwanta ta  tsaya tana sauke wani wahalallen numfashi daga inda yake zaune yana kallon yadda kafad’unta suke d’agawa sama alamun tana  kokuwa da numfashinta Ahankali ta juyo tare da sunkuyar da kanta  kasa dan bazata iya cigaba da kallonsa a yanayin da yake ba saboda yayi mugun tsareta da ido  yana kallonta tana takowa ahankali har sanda ta qaraso ta tsaya "set "! ya fad'a yana kunna sigarinsa muryarta sanyaye tace  "sir kayi hakuri ka kashe wannan abar bana son warinta "daga yau ki koyi son warinta set !ya sake maimaitawa" inna ilaihi ita kam ta shiga ukunta da wannan mutumin ta sake yin kasa da muryarta sosai kmr zatayi kuka "sir kada kamin haka dan Allah "me nayi miki  ?"ya tambayeta yana dage mata girarsa d’aya “sigari ce fa kawai ?meye illarta?"  set and don't let me repeat my seif again ".

babu yadda maryama ta iya da rayuwarta haka tayi shiru ta toshe hancinta da hannunta d'aya dayan hannun kuma taja kujerar baya kad'an  domin rage kusancinsu ta zauna sai dai duk a rud'e take .
tunda ta zauna bata d'ago kanta ba yayinda shi kuma kwayar idanunshi ke kanta yana zugar sigari yana zance zuci  "ta d'ara duk matan duniya a idanunsa ita kadai  zuciyarsa  take so ,kuma bazai ta'ba son wata bayanta  ba ,sai dai duk runtsi bazai d'auki raini daga gareta ba farar takadar ya janyo ya ajiye mata sannan ya janyo wata roba da kayan zane yake ciki shima ya ajiye mata "ki zanani ahaka .
"what ?" !
ta furta à matukar razane tare da d'ago fuskarta ta tsura masa yana rike da sigari yana zuga muryarta a raunane tace "sir kayi hakuri bazan iya zanaka kana shan sigari ba ka canza min da wani aikin na yarda "okay ! zana min mata da miji rungume da junansu suna kissing din juna a bakin kofa "oh my goodness god ya rabbi ka taimakeni akan wannan mutunin ta furta a can qasan makoshinta sannna ta sake tsura masa idanunta gbdy ta rasa natsuwarta ji take kamar zuciyarta zata buga haka ne ma yasa ta cigaba da kallonsa ko dai a buge yake ne ?sai dai tsaf yake abunsa idan ma baa a gabanka yake shan sigari ba bazaka ta'ba cewar shi din dan sigari bane dan babu abinda ya nuna ko ya sauya ajikinsa "Kina 'batawa kanki lokaci domin kuwa babu inda zaki har  sai kinyi abinda nake bukata."

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 19

Zuciyar maryama cunkushe da haushi had’e da takaicin mr ata ta zari pencil din zane ta soma aikin daya sakata wanda tai masa laqabi da aikin mugunta tana zane bakincikinsa na sake ninkuwa a kasan ranta, yayinda zuciyarta ke wani irin zafi da suya .
ina ma zata iya murje idanunta tare da cire d’an burbushin tsoronsa dake ranta ai wallahi data zage kunjinta ta zabga masa rashin mutunci fiyye da wanda ya iya .amman ina bazata iya ba ,bazata iya karawa da mr ata ba ,dan ko a yanzu ya gano wani abu daga cikin rauninta domin kuwa ya fahimci aikinta yana da matukar mahimanci arayuwarta.
cikin kankanin lokaci ta zana namiji sanye da kaya wondo da riga tare da jacket sannan ta zana mace tana rungume da namiji sanye da dogon riga kanta lullu’be da mayafi,ta gama amman tsabar ‘bacin ran sigarin da yaketa faman bankawa cikinsa yana busa mata hayaki ya hanata d’agowa ta kallesa bare ta sheida masa ta gama.”shi kuwa mr ata zuba mata ido yayi ganin yadda ta gama amman tana jin wani abu aranta yasa ya sake ware qafafuwansa ya kunna wani sigari a ransa yayi murmushi ,shi ko kwana zasuyi a hk daidai ne.”

“ ganin muddin bata yi managa ba zasu kwana a haka ba damuwarsa bane dan ta tabbrwa kanta miskilancisa da jin kansa bazai barshi yayi magana ba , dan haka cike da tsinkewar zuciya da kyarma jiki ta d’ago fuskarta inda yake karaf idanunsu ya tsarke cikin juna ,ganin haka yasa maryama sake had’e ranta tamau dan bata son ya kawo mata wani sabon rainin hankali ko rainin wayo tare da d’aga masa farar takardar hannunta tana nuna masa alamun ta gama .” kina son ki zamo matsalata?” yayi mata tambayar yana tsareta da tsumammun idanunshi ahankali ta girgiza masa kai tana cewa “bazan ta’ba son na zamo matsalar kowa ba ,abinda kasani kenan sir , kuma wannan shine iya abinda zan iya yi . shiru yayi kawai yana ajiye qarshen bakin sigari acikin wani dan qaramin kwanon tangaran .”sannan ya cigaba da dubanta tare da cewa “tsarin yanayi rungumar bai min ba kasancewar babu remotic .“
ta kalleshi da tarin mamaki akan fuskarta lip’s dinta take matsawa alamun magana take son tayi masa sai dai ta kasa furta komai dan zuwa yanzu gaba d’aya a firgice take dashi .”

Yanayin zamansa ,yanayin kallonsa ,yanayin maganarsa duk sun canza dan hatta kwayar idanunshi sun canza kala yayinda shirunta ya
bashi damar kallonta son ranshi dan ko son kifta
ido ba yayi ,ga wani kalar murmushi da yake wanda shi karon kanshi bai san yana yi ba sosai itama ta shagala da kallonsa amman ita kallo ne dake tattare da tashin hankali da tsoro ,ahankali ya matso kusa daita ya hura mata iskar bakinsa da sauri tayi kasa da kanta tana jin wata irin fargaba yayinda gabad’aya ilahirin jikinta rawa yake .zuciyarta ta cika fal da matsanancin tsoronsa ,jigun sukayi daga shi har ita barin maryama wacce komai ya tsaya mata cak ,yadda bai sake yin mgn ba itama bata ko motsa ba daga inda take zaune sai dai kowannen su da abinda zuciyarsa ke saqawa acikin zuciyarsa .”
zurfa goshinta ta share tana kallon mr ata tace “sir ko zan iya wucewa “?numfashi ya sauke da kyar yana soka yatsan hannunsa a gefen bakinsa.”
Chapter 40 · 0% Book details