← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 111

Sashe 58

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“kuma nagartarsa yasa kake son had’a aurensa da hindu .”da lokacin da yace bai sonta ka hakura da yanzu komai yana tafiya daidai daka tsira da mutuncinka ,sannan diyarmu tana tare damu amman ka dinga biye mata kana karfafa mata gwiwa har tayi yunkurin kashe maryama wanda hakan yasa aka samu damar daura mata laifin da ba nata ba yanzu wa gari ya waya ?”wallahi mu dinga cire son zuciya muna fadawa kanmu gasky ka duba lamarin nuzla da mahaifinta ya biye mata da yanzu an ta’ba daya goma bata gyaru ba amamn kai ka dinga biyewa hindu so hauka ne da zatai yunkurin kashe yar mutane ?”ai duk sharrin daaka bita dashi daidai ne ni na wuce amamn ka zauan kayi nazarin maganata da kyau wannna tashin hankalin babu abinda zai haifar sai qarin kiyayya wallahi sam bakayi wa mahaifin adam adalci ba dan nasa kwaya daya zaka maidashi makiyinka abinda shi bazai ta’ba yi maka ba kenan .”tana gama fadar hk ta juya ta kama gabanta baba qarami yabi bayanta da kallo ” daman ita haka zuciyarta take sam bata goyon bayan karya koda kuwa akan kanta ne kuma tabbas yasan gsky ta fad'a masa sai dai me zai yi yanzu ?” ya cigaba da zama a wajen yana tunani maganganunta."

Mmn Sudais💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 27

Gabad'ayansu a tsaye suke acikin office dinsu  fuskarsu d'auke da murnar samun nasarar da sukai
a jiya inda madam some ta zagayo ta tsaya kusa da maryama  tare da dafa kafad'anta tace "duk wannan cigaba mun samu ne saboda ke . maryama ta saki kyakkyawan murmushi wanda yayi matuqar bayana kyawunta sannan tace " karki ce saboda ni ,nasarar gabadayanmu ce, kuma kowa acikinmu  tayi kokari .
"kowance daga cikinmu ta cancacin yabo na mussa man tunda tare mukayi, wannan cigabanmu ne gbdy. ". sukai murmushin jin dadi suna sake yaba mata "amman fa duk da haka kin cancanci a miki ban girma ,kuma kinsan wani abu ?maryama ta girgiza mata kai tana cizan lip's dinta na qasa . "yanzu gbdy a kamfaninmu kece sama da kowa kuma  kece wacce tafi kowa iya tsara zane mai d'aukar hankali you're the best maryama ."
"maryama ta sake yin  murmushi batare da tace uffan ba ."sultana dake zaune tunda suka  soma maganar  bata ce komai ba sakamakon jin haushin babu ita ciki presentation din , sai dai aranta  tace "in sha allahu wannan dariyar da kike yi  sai tazame miki damuwa  arayuwarki .

Ahankali yusura tayi taku ta nufo inda maryama take tsaye rungume da hannuwanta duka a qirji  tace "ai sani ne bakuyi ba wannan nasarar ba komai bace a wajen maryama ,ai nasara a koda yaushe tana biye daita ,duk abinda tasa gaba sai tayi nasara, ba akan aiki  ba kawai , ko akan karatu  haka take akwaita da kwakwaluwa ko lokacin da muke karatu first class  take d'auka ita din yar baiwa ce "karki manta ni din marainiya ce ta gaskiya tun da na bud'e idanuna na ganni acikin maraicin  kinsani mahaifina ya  rasu tun ina yarinya kakata data rungumi maraicinmu da kyau take nuna mana qauna muraran sai dai itama bamuyi tsawon rayuwa daita ba ta rasu kinga babu yadda zanyi dole na  jajirce nayi karatu "duk da haka maryama ke din yar baiwa ce ,"kunga mu bar mgnr haka muyi aikin dake gabanmu  kafin mr ata ya shigo ya fara rikita mana lissafi ". inji cewar maryama ."gabad'ayansu sukai  dariya tare koma mazauninsu kowacce ta soma aikin dake gabanta .”

Alamun kira ne ya shigo wayar maryama  adaidai lokacin da take qoqarin zama ta kai kallonta ga wayar tana duba number dake yawo a screen din wayar "number da ake yawon kiranta dashi ne wanda ta d'auka ko sultan ne sai dai daga baya ta fahimci bashi bane "dan ta nemi numbersa taga ba iri daya bace, ta d'aga kiran tare da yin shiru daga can bangaren ma shiru akayi ana sauke mata numfashi acikin kunnenta dan tana jin sautin saukarsu ahankali ta fara taku ta nufi  kofar fita daga  cikin office din yayinda sultana ta zuba ma bayanta  ido ganin yadda take bada step tana rausaya abun burgewa yarinyar tana da shep na d'aukar hankali ,ba lallai kowani nmj ya ganta ya iya hadiye miyonsa akanta ba".maryama ta numfashi kana ta cire wayar a kunneta ta  duba har lokacin mai shi yana kan layi sai dai babu alamun wannan saukar numfashi muryarta can kasan makoshi tace "hello !sai dai shiru taji babu amsa .

"hello wake magana? "ta sake yin mgn still dai shiru ne ya biyo baya kusan second biyar babu alamun zaayi magana  dan haka tayi disconnecting  din kiran ta nufo office  tana tunanin kiranta daakayi  mata kwanakin uku da suka wuce akace mata daga office ne  wai tazo da wuri bayan tazo din kuma taji shiru bata ga kowa ba sai mr ata wanda tayi imani ba muryarsa bane ,to  waye ya kirata ?"waye wannan da yake son dagula mata lissafi ?"ta furta a kasan ranta tare da samun guri ta zauna ta kasa aiwatar da komai tana sake zurfafa tunaninta lallai ya kamata ta nemi  mai wannan number da yake  kiranta taji dalilinsa na kira wayarta yana damun rayuwarta ."
Ahankali tai dealing number a qaramar wayarta ta shiga neman layin sai dai ba'a d'aga ba  tana cikin wannan halin mr ATA ya shigo office din yayinda kwayar idanunshi ke kanta sai dai  ganin hankalinta na kan wayarta yasa shi d'auke idanunshi akanta ya soma  mgn a natse  akan  qokarin da sukai jiya  "naji dadi sosai da qoqarinku na jiya na jinjiwa  kokarinku "sir ai ina tunanin maryama ce ta cancanci haka,dan  gsky ta cancanci jinjina har ma da  especially thanks ".inji cewar madam some "ta fad'a tana murmushin farinciki .”

asukwane ya kalli inda take zaune inda tayi busy  sosai wajen bincike layin daake damunta dashi a truecaller tana son taga da wani suna akayi registrater layin sai dai wani birkitaccen suna ta gani ."mr ata yayi shiru yana kallonta a tsanake yana nazarinta dan tunda ya shigo ya soma magana ya fahimci bata tare dashi,haka  hankalinta yana wani guri dabam ya cigaba da kallonta kafin a hankali yayi taku biyu ya dawo kusa daita sosai yana kallon cikin wayar dake rike a hannunta still dai bata maida hankalinta garesa ba." abinda yafi tsana kenan daga gareta ta ganshi amman tayi kamar bata gansa ba aranshi yace ko number wa take kira hk "?amman a zahiri muryarsa a kausashe yace "some ke kinfi kowa sani ina bawa wad'an da kad'ai suka d'auki aikinsu da mahimanci ne lokacina,yayinda  ita  wannan macece da bata bawa aikinta mahimanci any way kizo kisame a office akwai ayyukan da zamu yi magana akansu yana gama fadar hk  ya juya ya fice ."

Mr ata yana fita office dinsa ya koma ya zauna akan kujera yana juyi  sai dai hankalinsa da nastuwarsa suna gareta ." yayinda ita kuma tayi busy gurin son gano ko waye yake son damun rayuwarta yana kallonta tasa wayarta  ta dafe goshinta  wanda daga gani ta rasa mafuta ne yasa tayi haka  "to me yasa ba'a d'aga  kiran ?"kuma idan ban kira ba bazan san kowaye ya kirani  a akwanakin baya da km daren shekaranjiya har ma da yau din nan lallai ya kamata nasan kowaye daga cikin ma'aikatan kanfanin nan  sosai mr ATA yake son yasan  damuwarta." yana zaune a office dinsa amman kwayar idanunshi na kanta har sanda sultana ta shigo office din tana kiran sunansa wani irin mugun  kallo ya jefa mata wanda yasa tayi saurin cewa”oh sorry sir congratulations sir duk da dai  ni baa sakani ciki presentation ba wanda bansan ni laifin me nayi ba daaba sakani ba “wani irin matsefaffen haushinta yaji ya taso masa tun daga  kahon zuciyarsa har zuwa kan fuskarsa sai dai bai yi magana ba ya cigaba da juyi akan kujera yana sake maida hankalinsa ga sarauniyarsa ."

ta sauke naunayen ajiyar zuciya kana ta cigaba da magana tana kallonsa "ko zan iya sanin dalili  da yasa ni baa sakani ba bayan nima maaikaciyar kamfani ce kamar sauran ma'aikatan kamfani ?"irin Kallon da yake mata ne  yasa gabanta ya dinga faduwa "I think  kinzo office dan Kiyi aiki ne ?ta gyad'a masa kanta cike da rauni "okay pls kije kiyi aikinki ."wai dan Allah mai yasa ya Adam kake min hk Kmr ni ba jininka bace ?komai nayi sai ka nuna ni din ba kowa bace agurinka ,kasani wannan ba daidai bane this is not right ya Adam ko dan kaga na damu da kai ?"shiru yayi tare saisaita kanshi “kana yi kamar baka san me nake nufi ba alhalin kasani
“ka kuwa san  irin son da nake maka ?"saboda kai na .." "actually get out ". ya fad'a a matukar fusace yana nuna mata hanyar fita da yatsan hannunsa d’aya tare da kiranta da  nonsense."ranta a matukar bace  ta fito da sauri tana goge hawayenta ta wuce maryama tsaye wacce kusan duk  taji wasu daga cikin maganganunta ."
Chapter 58 · 0% Book details