Sashe 71
Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da sauri ta mike tsaye tana cewa "sir ni zan wuce gida "karki damu yanzu zamu wuce ."yanzu zamu wuce kuma ?"ta maimaita a fili zuciyarta na luguden bugu "eh zamu kai ki gida ne ko bakya so?" tayi shiru tana tunanin tare da nazarinsa "kin yi shiru ya fad'a yana dawowa gabanta ya tsaya yana kallonta ta d'an d'ago ahankali idanunta sukaci karo da sarkan zinarin wuyansa dake kwance a qirjinsa wani sabon tsoro ya kara dirar mata a zuciya wadda yasa tai saurin sunkuyar da kanta tana runtse idanunta gam "ko kin fi so ki shiga motar hanya kuna gogayya da maza ?"numfashi kawai ta sauke batare da tace masa komai ba ."ahankali ya juya yana maida maballin rigarsa ya kwashe wayoyinsa ya nufi kofar fita tana tsaye kawai taji alamun baya gabanta dan haka tayi qoqarin bud'e idanunta taga har ya kusan ficewa daga cikin office din, tabi bayansa da kallo tana maida numfashi bata san me take ji adaidai wannan nan lokacin akansa ba .”idan tace tasan abinda take ji ko tasan abinda shi yake tattare dashi tayiwa kanta karya ta dai tasan a duk lokacin da tayi arba dashi ya kan gusar mata da hankalinta bazata ce so bane dan bazata jefa rayuwarta cikin matseefa ba dan ko soyayya ne sai tayi duk yadda tayi takicesa aranta bare ma bashi bane .”
Bazata ta’ba wannan ganganci ba shi kuma tasan yafi qarfin ya sota sai dai idan wata manufa garesa akanta idan ba haka ba ina ita ina shi hanyar jirgi dabam ta mota dabam ta sake numfasawa tana tunanin binsa ,ta bishi ne ko kuwa ta kama gaban ta ?" abu daya ne zai sa ta bishi saboda taimakon da zai mata akan nadiya if not bazata sake ganganci binsa ba kuma tasan halinsa muddin taki baqaramin aikinsa bane yace ya fasa taimakonta ."ta kusan mintuna a haka bata motsa daga inda take ba kafin ahankali ta soma taku ta fito ta shiga office dinsu inda kusan kowa ya watse ,wasu tsirarrun maakatan sultan ne suke kai kawo ,ta kai hannunta ta d'auki jakarta dake ajiye akan table ta rataya a kafad'anta tana qoqarin fitowa daga office din wayarta ta shiga qara mara sauti,nan take ta tsaya ta ciro wayar daga cikin jakarta tana duba screen din wayar suannsa ta gani yana yawo ahankali ta sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ta d’aga "hello sir !"dan Allah malama ki fito karki ‘bata min lokaci .""O.."okay sir.."kafin ta rufe bakinta har ya katse kiran.”
jiki a sanyaye ta qarasa fitowa daga office din tana d'aga qafafuwanta da kyar, a tsaye ta ganshi ajikin had’addiyar motarsa bmw fara sol hannayensa duka suna cikin aljuhun won dashi , ganinta yasa ya bud'e mata murfin kofar baya sannan yayi mata alama ta shiga da kwayar idanuwansa,wani yrrr taji a gaba d'aya ilahirin jikinta ahankali zuciyarta ya dinga bugawa da sauri sauri "wannan shine karo na biyu da yayi mata haka ,kuma a gaban masu tsaronsa da direbansa ,ba ita ba hatta masu tsaronsa da direban sa a ruwa sun dasa ayar tambaya akanshi dan duk tsawon lokacin da suka d’auka tare dashi suna masa aiki babu wanda ya samu wannan matsayin bayan mahaifiyarsa gashi karo na biyu kenan yana bud’e mata murfin mota .”ahankali maryama tayi kasa da kanta tana d’ora hannunta d’aya akan d’aya tana d’an jujjuya jikinta alokacin da yake sake mata alamar ta shiga, tai tsam da zuciyarta dake tsinkewa tana sake nazarinsa da kyau."
alamunsa da abubuwan da yake mata suna nuna mata kamar só ne saboda duk yadda mutun yake sonta tana ganewa amman kuma shi nashi salon ne yazo dabam shi yasa ta kasa fahimtarsa da kyau
Idan yayi wani abu kamar só sai kuma yayi wani abu kamar sha'wa ,za dai tafi ajiye abun a matsayin shaawa dan ina mutun kamar shi zai sota ?" "me mutun kamarsa zai yi daita ?"wace ce ita ?"waye ubanta a duk fadin kasar nan da har zai sota ita data kasance jinin talakawa ,me yasa zai sota?"kai wanan ma ba abune mai yuwu ba, akwai dai abinda yake nema a wajenta wanda ba sai ta tsaya wahalar da kanta ba tuni tasan me yake so atare daita gara ta kama mutuncin kanta zai fiyye mata alkhairi kuma har abada bazata yarda ta banzatar da budurcinta ba duk wuya duk runtsi tana tare da abunta .”cike da natsuwa ta shiga ta zauna bangaren daya bud’e mata tana mai ra'be jikinta tare da kamkame kayan jiknta tana kallon bangaren da take zaune tana jinsa ya shigo ya zauna a kusa daita bai ra’beta ba sai dai taji idanunshi ajikinta suna yawo wanda ke qara saka zuciyarta tsinkewa tare da mummunar bugu .”
ahkl mota biyu suka fara fita sai motar da suke ciki tabi bayansu sai kuma mota biyu dake biye dasu a natse direba ke jansu, motar tayi shiru yadda bai ce mata qalla ba itama bata waigo inda yake ba bare ma ita bata da abinda zata ce masa ,dan kusan shi ke takalota da magana har suka isa titin Liverpool bai ce uffan ba , anan taga motocin gabansu sun d’auki wata hanya haka ma motocin bayansu yayinda motarsu ta sauka zuwa kasan bridge din Liverpool ahankali direban ke jansu ,tukinsa bai yi slow ba hakazalika ba mugun gudu yake shararawa ba a haka har suka shigo unguwarsu still babu wanda ya cewa danuwansa wani abu ,a ruwa yayi parking a inda yayi jiya yana cewa “ranka ya dade mun qaraso mr ata bai ce masa qala ba illa ya rankwafo zuwa jikinta yana qoqarin bud'e mata murfin motar daga cikin “ya rabbi ta furta tana saisaita numfashinta sakamakon abinda taji ya tsarga mata ai yana barin jikinta tayi wuf ta fito daga mota adaidai lokacin daake kiran sallahr isha'i kafin tayi tattaki ta tsallaka ta karya kwanar da zata shigar daita dogon layinsu taga ya fito bata tsaya ba ta soma tafiya.”
ahankali ya biyo bayanta, idanuwanshi na kanta haka ya dinga binta yana bin duk wani takunta da kwayar idanunshi tamkar wacce ke rangaji haka take ajiye takunta a nutse duk ilahirin jikinta na juyawa ,duk jin kan maryam daya sani da nuna ita wa tace wajen iya gayu da sanyin murya tare da iya tafiya bai ta'ba ganin tayi irin salon maryama ba kai bai ma san mata nada irin wannan salon ba ko don bai kallon mata ne sai maryam din data zame masa dole kuma da ita kad’ai ya zauna bai sani ba , dan shi bai san komai da ya shafi shirgin mata ba tsakaninshi dasu a wajen aiki ne kuma tsakani da Allah shi baya kallon tafiyarsu ."
"Wait" ! Kunnuwanta suka jiyo mata muryarsa mafi soyuwar sauti domin dai ko tana so ko bata só zuciyarta ta aminta yana da sanyin murya mai dadi da shiga jiki ,ta tsaya cak ta kasa juyowa zuwa garesa sakamakon abinda ke nukurkusan zuciyarta da ganganr jikinta a natse ya qaraso zuwa gareta ya tsaya a gefenta yana had'a kafad'anta danashi "ta d'an matsa kad’an aranta tace "matsalarsa kenan son jikin matseefa”.
ya motsa lip's dinsa ahankali "karki mata tambayar da nayi miki d'azu a office ,tana jinsa amman tayi shiru "zan baki lokacin nan da qarshen watan nan ina son ki natsu kiyi tunani akaina, bana son idan na tambayeki ki tsaya min inda inda ko kice baki fahimci komai ba ,ko kuma kizo min da wannan banzar kukan naki I can't take it "yana gama fad'ar haka yace zaki iya wucewa zuciyarta na bugawa da matsanancin qarfi ta soma d'aga qafafuwanta wanda take jin sun mata nauyi kamar yadda maganarsa suka mata nauyi acikin kwakwaluwarta ,tana tafiya amman still tana jin idanunshi na biye daita a duk inda tasa qafarta sai dai ta kasa juyowa taga halin da yake ciki a haka ta shige gidansu bazata iya cewa ga adadin lokacin daya d'auka a kofar gidansu ba ."kai tsaye bangaren umma ta shiga kamar koda yaushe Sai dai duk jikinta yayi wani iri umma ta hango zaune ita kad’ai a parlour’n hannunta rike da casbaha da alamun idar da sallarta kenan .”
assalamu alaikum “ta furta tana mai qoqarin qarasawa inda take, umma ta amsa mata tana kallonta da kulawa “maryama kin dawo ?”na dawo umma sannu da gida .”yauwa !”ta amsa tana dubanta maryama tayi shiru tana jingina bayanta ajikin kujera har lokacin zuciyarta taki daina bugawa inda ita kuma so take ta saisaita ta dawo normal .”
“Lafiya kuwa maryama naga duk kinyi wani iri “?hawaye ya d’an gangaro a gefen idanunta amman tayi dabarar gogesa “haka fa jiya kika shigo min nayita tambayarki abinda ya samu hannunki kika
yi ta wasa da hankalina batare da kin fad’a min ba yau ma gashi kin shigo min wani iri anya kuwa maryama kina son kwanciyar hankalina “?nafi kowa son kwanciyar hankalinki ,babu komai ne yasa yau na gaji ne sannan jiya yankewa nayi yasa kika ganni wani iri “naji kin gaji ne yau shi yanka garin yaya ne ta faru ?”maryama taso sheida mata komai amman dai tayi tunanin ta bari har mr ata yagama mata binciken da yace zai yi mata ta gyara zamanta tana duban umma “ki kwantar da hankalinki babu komai kawai dai sausayi ne numfashi umma ta sauke tace “naji sausauyi ne amman fa kisan bayanshi akwai abinda ke damunki menene shi ?”maryama tayi shiru suna kallon juna da umma tasani dole umma zata damu sakamakon jiya bata runtsa ba zariyar data dinga yi daga dakin zuwa parlour ma kad’ai ya isa ta gane tana da damuwa wacce baa akan kowa bane sai akan mr ata .”