← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 111

Sashe 30

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maryama na kwance ta soma jin qarar wayarta wanda shine ya dawo daita daga tunanin da take,ta mika hannu ta daga ta kara a kunnenta ba tare data damu da duba mai kiran ba"Assalamu alaikum warahmatullah" muryar nan nata mai daraja da qima a wajensa, muryar nan da yake bawa girma muryar nan da babu tamkarta acikin zuciyarsa
itace ta ratsa dodon kunnensa ji yayi tamkar an cire masa duk wata laka dake jikinsa ta cire wayar a kunnenta ta duba ganin sunansa sai da qirjinta ya buga ta sauke numfashi ta maida wayar ta sake yin wata sallamar tare da yin shiru tana jiran taji yanayin da zai amsa mata sallamarta .sai dai madadin taji ya dawo mata fatan amincin data masa sai taji maganarsa cike da gadara ”ke ni ne na zama abun wulakantawa wajenki ?”

Da sauri ta mike zaune tana cewa no !no sir !! ba haka bane wallalhi bana cikin natsuwa ne shekaranjiya kayi hakuri sir “ba hakuri na kira ki bani “mai ya hanaki zuwa aiki yau ?”shiru tayi zuciyarta cike da tsoro “kaji mutumin da bai je aiki ba ko ina ruwansa da rashin zuwanta ?”am talking to you?”amm uhm “sai kuma tayi shiru ta kasa cewa komai “saboda kin rainani shiyasa kike yin abinda kika ga dama “?ta sake kwantar da muryar da ladabi tamkar tana gabanshi tace “sir ba haka bane ai tsakanina da kai babu raini yau din ne na tashi da matsanancin ciwon kai ko kwayar idanuna bana iya budewa amman kayi hakuri” ta qarasa maganar cikin muryar kasaka kwalla na cika mata idanunta alamun kuka.”

nan take yaji zuciyarsa ta karye idanunshi ya lumshe sannan yace “Allah ya baki lafiya karki manta da sauran aikin dana baki gobe ne za’a zo kar’ba kiyi qoqari kiyi da kyau karki bari a samu wata matsala ko kuskure.” tace “in sha allahu sir gobe karfe tara daidai dashi zaka soma cin karo a office dinka ta fad’a “kiyi make sure bakiyi bacci ba dan ki gama komai kafin 5:30 “ok sir zanyi duk yadda kace “ very good .”wani farinciki ya mamayeta cike da jin dadi tace “thank sir …”yayi shiru yana jin yadda take farinciki wanda yayi sanadiyyar shima ya tsinci kanshi cikin farinciki ya maida jikinsa ya jingina da abun gado ya janyo pillow ya matse a faffad’an qirjinsa yana jin tamkar itace rungume a qirjinsa “.“mr ata !ta kirasa cikin kasalalliyar muryarta mai tsananin kashe jiki da zuciya “tasan bazai amsa mata ba dan haka ta cigaba da magana “nayi maka sallama irin ta addinin muslinci har sau biyu amman baka amsa ba “still shiru yayi mata yana sauke mata numfashinsa a kunnenta “.

“dan allah ka amsa min nima kamin fatan amincin Allah ya tabbata agareni shiru ne ya sake biyowa baya har na tsawon second biyar har ta fitar da rai zai ce wani abu sai ta jiyo sautin sanyayyar muryarsa “wa alaikumussala wa rahmatullah “.ya amsa mata bayan ya sauke ajiyar zuciya. idanunta ta lumshe daga can yana duban kanshi a madubi sai yaga gabadaya ya sauya tamkar bashi ba dan shi kansa ya san baya abubuwa irin na mutane “na gode mr ata na gode da kamin fatan samun amincin Allah agare…” jiya tayi ya katse kiran tun bai ji mai zata qarasa cewa ba .”numfashi ta sauke tana godewa allah daya d’aurata akanshi dan bata d’auka zai sauko haka ba bama ta d’auka zai nemeta ba ta d’auka shikenan sai dai taji an koreta daga aiki .” ta ajiye wayarta akan gado, nan da nan ta duro ta d’auko wata katuwar takardar zane tana dubawa ahankali ta soma aiki har kusan karfe biyun dare tana aikinta .”

yadda batayi bacci ba haka shima bai runtsa ba bini bini zai kirata yaji ko idanunta biyu .”gyangyadi tasoma na alamun bacci da sauri ta dawo haiyacinta “kai bacci ka barni bazanyi ka ba har sai na kammala da ayyukan gabana babu abinda take sai Hamma , bacci ne sosai acikin kwayar idanunta amman haka ta cigaba da zane amman bacci ba’a cin bashinsa sai daya d’auketa bata farka ba sai karfe uku da rabi na dare agigice ta kai idanunta kan agogo ta sauke numfashi tana hamma “wallahi bacci nake ji ta furta cikin muryar bacci tana lumshe kwayar idanunta sannan ta bud’e tana kallon tarin takardun data baje akan gadonta ,dole sai na gama aikin nan kafin na kwanta idan ba haka ba zan had’u da tashin hankali gobe.”

ta mike ta tattara kayan aikinta ta dawo parlour’ ta d’auki remut ta kunna tv wai dan kar bacci ya d’auketa ta cigaba da aikinta amman ina bacci fa yace bai san hakuri ba ai kuwa ya kwasheta akan kujera batare data qarasa aikin ba.”shima bangaren mr ATA kwana yayi yana aiki batare daya runtsa ba haka mami bata runtsa ba, ta shigo ta kawo masa coffee ya amsa batare daya ce komai ba ta juya ta fita ya kai bakinsa yana kur’ba a hankali ya d’auki wayarsa yana neman layinta sai dai wayar na ringing baa d’auka wanda maryama na can tayi nisa cikin baccinta ganin haka ya mike tsaye ya ture system din gabanshi ya shiga zariya hannunsa daya cikin aljihunsa yayinda kunnensa ke manne da waya yana neman layinta “maryama ki d’aga wayar mana amman shiru bata d’auka ba allah dai yasa ba bacci yarinyar nan tayi ba.”?

Tana tsaka da baccinta taga yaya sadam sanye da riga baki yana tafiya a hankali ,yayinda hannunsa daya ke rike da waya dayan hannunsa kuma rike da wata kyakkyawar budurwa suna tafiya cike da annashuwa da farinciki har suka qaraso farm center dake ikeja a long suka tsaya daidai wajen wani katanfarin gidan abinci wanda babu abinda babu naci acikinsa budurwa ta kwanto jikinsa sosai tana zuba masa shagwaba tana nuna masa restaurant kai tsaye suka shiga suka samu waje a vip suka zauna inda ma’aikatan wajen suka qaraso suka mika masu wata takarda da jerin abinci da suke dashi yake zane acikinsa budurwa nan tayi shiru tana kallon hadin salad wanda yaji nama da cocomba ta sake kwantowa jikin yaya sadam ta nuna masa abinda take bukata murmushi ya sakar mata tare da shafa gefen fuskarta ya nunawa maaikacin dake tsaye nan ya tambayesu zasu ci anan ne ko zasu yi takeway .”

Ya sadam ya kalleta tace “zasu wuce dashi dan haha maaikacin ya juya cikin lokacin kankani ya dawo rike da farar leda ya ajiye masu akan table din gabansu yaya sadam ya ciro kudi agaban aljihunsa ya mikawa mutumin sannan ya kalli budurwa da yake tare daita ya kai bakinsa daidai nata zai yi kissing dinta nan maryama ta farka a matukar gigice tana kiran sunansa wanda hakan yasa umma ta farka daga nata baccin ta fito da sauri ta nufi d’akinta sai dai bata ganta ba dan haka ta fito zuwa falo tana kiran sunanta “maryama! maryama !! Kukanta yasa ta qaraso da sauri ta rungumeta tsam ajikinta tana cewa “lafiyaki meke faruwa?”ummah mafarki nayi da yaya sadam tare da wata budurwa allah umma ina ji ajikina yaya sadam bai mutu ba yana raye .”

Umma ta kwantar da kanta a jikinta tana cewa “ idan bai mutu ba maryama mai zai hanashi dawowa gida ?idan bai dawo danke ba ai ya dawo saboda ni mahaifiyarsa dana rage masa a duniya ki cire wannan tunanin cewar bai mutu ba aranki d’an mutuwa kam sadam ya mutu sai dai muyi masa fatan allah ya hada fuskokinmu a aljanna .”shiru maryama tayi tana nazarin maganarta da kuma tunanin yarinyar data zo jiya a matsayin abokiyar aikinsa sannan kuma da sautin muryar dataji irin nasa anya kuwa sadam ya mutu kamar yadda mutane suke tunani?” ita dai tana ji ajikinta bai mutu ba amman zatayi kokari taje farm center gobe .”maza tashi muje ki kwanta ki bar aikin nan haka kya qarasa gobe idan allah ya kai mu mikewa tayi jikinta a matukar sanyaye umma ta tattara duk kayan aikinta suka nufi dakinta ta kwantar daita akan gado itama ta hau ta kwanta tana shafa sumar kanta .”

kasa komawa bacci tayi saboda da zarar ta runtsa idanunta sadam dinta take gani har asuba babu wani baccin daya dauketa .”Kiraye kirayen sallah ta soma ji daga masalatai mabam bamta dan hk ta sauko daga kan gado ta shiga bayi ta dauro alwala ta fito ta isa inda sallaya yake ta d’auka ta shimfida ta soma gabatar da nafil fili haka ma umma washegari qarfe takwas daidai ta shirya cikin doguwar riga yellow ta fito ta bar gida kai tsaye farm certer ta nufa inda ta shiga gidan sai da abincin data gani ta samu waje ta tsaya tana dube dube komai da ta gani a mafarkinta haka tagani azahiri sai dai wurin babu mutane sosai tana tsaye har karfe tara tana zagaya wurin ko Allah zai sa ta gansa sai dai babu shi .”

Jiki a sanyaye ta fito tana dube dube duk inda taga gidan abinci sai ta tsaya ta nuna hotonsa ko sun gansa a wurin jiya sai dai har karfe goma bata samu wanda yace mata yaga koda mai kama dashi ba amman haka ta cigaba da nemansa yayinda mr ATA ke faman kiranta a waya tana danna masa rejecting .”tsaye yake a office yana zariya domin kuwa dai lokacin da masu kar’ban zane yayi kusa gabadaya an gama arrangement din komai maryama kawai ake jira ya sake kiranta adaidai lokacin data nunawa wani mutun hoton sadam yace “zaki dauki kiran ne ko zaki bari naga hoton da kyau ?”sorry please ta fad’a tana saka wayar a flay mood ta mika masa wayar.”

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
   MAR'ADAMS
   💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

       Page 14
Chapter 30 · 0% Book details