Sashe 20
Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ashe maryama akwai damuwar da zaki kasa fad'a min ?tayi shiru tana kuka kafin ahankali taji shigowar sako wayarta nan jikinta ya sake daukar rawa ta sake tabbatarwa kanta sakon dakatarwa ce "shikenan na rasa aikina ".shine kawai abinda ta dinga maimatawa a fili cikin kankanin sakanni idanunta suka kada suka koma jazur ta dinga fidda huci " wani bala'in tausayin maryama din ya mamaye umma , "me kikayi har aka dakatar dake aiki ?shiru maryama ba magana sai kuka "ni daman tun da kika dawo na fahimci kina tattare da damuwa amman kikace babu komai kinfi son kiyita boye damuwa a zuciyarki tana cutar dake kina tunanin boye damuwar shi zai miki maganin halin da kike cikine?"
cikin murayar kuka ta shiga fad'awa umma abinda ya faru shiru umma tayi tana sauraronta har ta dasa aya umma tace "maryama baki kyuata ba ya dace kisan yadda zaki masa magana duk da nasan kureki yayi ."wallahi umma kureni yayi sam mr ata bai da mutunci ni bansan sanda yana fad'a ina fad'a ba "amamn tunda a qarqashin ikonsa kike dole sai kinbi dokarsa sannan zaki zauna lafiya nan dai umma tayi mata fada sosai tare da kwantar mata da hankali dan bata son tana yawan shiga damuwa da tunani saboda ba wai ta gama dawowa normal bane da kyar ta samu maryama tayi shiru ta share hawayenta tace ta bata wayar ta duba taga sakon daaka turo mata."
"A'a umma karki bude kawai ni nasan babu abinda zai saka mr ata kirana adaidai wannan lokacin ko ganin sakon madam some sai dan dakatar dani "ni umma miko min charbinki kawai na fara ja ko
tunani da damuwa zasu barni ta qarasa mgnr tana sake furta kalmar "Inna lillahi wa inna ilaihir raji un, tana hadawa da salatin Annabi da istigifar "maryama ki natsu in sha allahu ba abinda kike tunani bane Allah yana sane dake kuma zai kawo miki dauki bani wayar na duba jiki a sanyaye ta mikawa umma wayar ta amsa ta shiga inbox dinta umma ta fara karanta sokon a fili "ki tabbatar da kin zo da aikin da muka baki Gobe karfe tara daidai wani irin juyowa maryama tayi ta fuskanci umma hawaye na bin kuncinta ."
Kallon kallo suka shiga yiwa juna "kingani ba duk da abinda kikayi masa amman har yanzu suna bukatarki a ma'aikatan su lumshe seyx eyes dinta tayi tana godewa allah da ba dakatar daita sukayi ba sako na farko umma ta karanta "ki dauki kiran mr ata magana ce akan desing's din daaka baki aiki shine sakon some dayafi komai daga mata hankali naunayen ajiyar zuciya ta sauke " yanzu sai ki tashi kije ki fara abinda ake bukata daga gareki "wallahi ni yanzu duk jikina a sanyayye yake akan aikin baa wa mr ata gwaninta komai kayi baka iya ba komai bai masa ba wallahi umma bansan ta ina zan fara ba ."
" haka zaki karfafa zuciyarki ki tashi kije ki fara sosai umma ta dinga karfafa mata gwiwa har ta samu natsuwa da jin zata iya masa fiyye da abinda yake bukata daga gareta ."ahankali ta mike ta shiga dakinta taja kujera ta zauan ta fito da kayan aikinta d'auki farar takardar data fara zanen tana duba zanen da yace bai masa ba zanen yayi kyau sosai tana cikin tunanin yadda zata kawo wani sauyi akan zanen ya sake kiranta jiki a sanyaye ta d'aga cike da sanyi muryar tace " barka da dare sir ?you are very stupid dake da gaisuwarki".shiru tayi hankalinta na sake tashi "ni zaki katsewa kira ?muryata nã rawa ta soma bashi hakuri ai kuwa hakan ya bawa mr ata damar zuba mata ruwan matseefa."
Aiko hanakalinta yay mugun mugun tashi gabanta ya dinga dukan tara tara cike da jin tashin hankali tace "nifa sir bana son fad'a kabi komai ahankali tunda kace tara ka bari taran gobe tayi mana idan banyi abinda kake bukata ba sai ka dauki mataki akai ".daga can inda yake zaune ya gyara zama tare da motsa bakinsa da niyyar sake mata wani sabon rashin mutunci tunin maryama ta kashe wayarta gabad'aya ta zuba tagumi da hannuwanta duka tana mai runtse idanunta wayar ya cire a kunnensa yaga dip alamun ta kashe ya sake kira yaji swichoff
Tsaki yaja yasan zata rina ga rashin kunya ga tsoro wanda shine abinda yafi bukata tagani atattare daita
Ata nã zaune yana tunanin had'uwarsu da maryama Gobe kamar ance ya d'ago kwayar idashin kawai yaga fitowar mutun daga kitchen ."
Tsumammun idanunshi ya ware akanta maryam ce da ritsetsen cikinta da yayi girma sosai tana d'aga kafafuwanta da kyar yayi mugun tsura mata ido yana kallota nan take yaji qirjinsa na wani irin bugawa da qarfi "duk da cikin jikinta yayi girma sosai sai dai cikin bai sa tayi wata kiba ba sai uban fari data qara da gajarcewa yayinda hannunta ke rike da plet wanda bai san ko meye aciki ba ,ahankali ta cigaba da tafiya da kyar irin tafiyar masu ciki ta samu waje opposite dinsa ta zauna tana danne damuwarta dan ita kad'ai tasan irin damuwar da zuciyarta take ciki akanshi ,dan ta dauka kiyayyar da yake mata zata tsaya ne a iya kanta a she har da cikin jikinta kiyayyar zata shafa ta sunkuyar da kanta kasa tana danne hawayen daya cika kwarnin idanunta ta soma cin d'anwake wanda shi har lokacin bai san ko meye acikin plet din ba sakamakon tazarar dake tsakaninsu tsumammun idanunshi kawai ya zuba mata yana kallonta da cikin jikinta ."
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 9
Yadda mr ata ya tsurawa maryam kwayar idanunshi yana kallonta zaka d’auka zuciyarsa ta d’an saduda ne akanta ,sai dai azahirin gaskiya ba haka bane kawai tsabar mamaki ne cunkushe a zuciyarsa” wai d’ansa ko ‘yarsa ne kwance acikin matar da yake jin duk duniya bashi da abinda ya tsana sama daita tunda ta bar rayuwarsa ya d’an samu natsuwa da kwanciyar Allah a yanzu idan yace yaji dadin ganin fuskarta yayiwa Allah karya haka zalika ganin girman cikinta bai saka zuciyarsa jin komai aransa ba ko jin digon tausayinta ba sai ma jin haushi da bakinciki ganinta ne ke nunkuwa a kasan zuciyarsa yayinda zuciyarsa ke zafi da suya.” dogon tsaki yaja wanda yasa maryam tabar cin abinci da take ta d’ago kanta ta zuba masa ido dan ko bai fad’a ba tasan saboda ita yaja tsaki .”shiru tayi kawai tana faman sauke ajiyar zuciya .”fuskarshi babu walwala ya sauke kwayar idanunshi akanta alokacin da kiran gaggawa ya shigo wayarsa ya kai dubansa ga wayar ,d’aya daga cikin abokan kasuwan cinsa ne daga haka ya mike tsaye, a natse ya nufi hanyar fita waje dan gara tun wuri ya qara gaba kafin sweet heart tazo masa da batun yarinyar dan yasan dole zata masa maganarta wanda shi kuma abinda yafi tsana kenan .”
Mikewarsa ya daidai da sake jefa zuciyar maryam cikin gagarumin tashin hankali juyawa tayi tabi bayansa da ido tana kallon yadda yake d’aga qafafunsa tamkar baya son taka qasa .” kallo d’aya zaka mata ka tabbatar da cewar bata cikin natsuwa da walwala da kwanciyar hankalinta dan tunda ta sauka hankalinta da natsuwar da kwayar idanunta babu abinda suke da muradin gani tamkarsa so take taga yadda reactions dinsa zai yi idan ya ganta d’auke da cikinsa ,sai dai kash a ganin farko yayi buris daita da cikin jikinta tamkar bai gansu ba ,ita kuwa burinta ta ganshi hakazalika babynsu taji dumin jikin mahaifinta duk da tasan abu ne mai matukar wahala ya basu wannan damar .” bata san tsananin qaunar da take masa ya zarta dukkanin tunaninta ba sai data d’aura kwayar idanunta akanshi yanzu .
“ tunda taganshi taji komai ya dawo mata sabo ji tayi tamkar ada can bata ta’ba són shi ba a yanzu ne take son shi . numfashinta ya shiga sauka da sauri sauri sai ga hawaye sharr sun shiga turereniyar zubowa daga cikin kwarnin idanunta saboda rashin kulawar daya nuna mata ita da cikinsa ,gabad’aya taji gwaiwarta tayi sanyi wanda hakan ya sake tabbatar mata babu abinda zai canzasa daga ra’aayinsa ita da babynsa baza su ta’ba samun kulawa da soyayyarsa ba “me yasa bazata ciresa aranta ba tunda har qiyayyar ta kai haka ?”me yasa take son shi haka ?meye laifinta dan taso shi fiyye da komai a duniya ?”babban tashin hankalinta yanzu cikin jikinta wanda likitanta ya tabbatar mata bazata iya haifa da kanta ba ,yanzu shikenan idan ta rasa ranta wajen haifa masa baby bashi da asara babyn ce kawai zatayi rashin mahaifiya ya kamata maryama ki qarfafa zuciyarki ,ki manta dashi ki rayu ko dan abinda yake cikinki domin Ita kad’ai ce gantaki itace zata zama abokiyar adawa ga rayuwar adamcy”
ko cikakken mintuna goma mr ata bai yi da fita ba sai ga mami ta fito da sauri ta qaraso inda take zaune tana kallon kofar fita had’e da kiran sunanta “maryam lafiya ?”meke damunki?”ta fad’a tare da zama kusa daita ta riko tafin hannunta cikin nata .”hawaye kawai take zubarwa saboda tasan me zai iya faruwa idan mami taji damuwarta ita kad’ai tasan yadda take jin cikin jikinta baqaramin tokare mata qirji da mara yayi ba “kiyi min magana maryam meke damunki ?still shiru tayi ta kasa cewa komai sai sheshekan kuka take “kun had’u da adamcy ne ?”ahankali ta gyad’a mata kai alamun “eh! “wani abu yayi miki ne kike kuka ?ta girgiza mata kai alamun babu “to kukan me kikeyi haka ?”still kai ta girgiza mata bugun zuciyarta na qaruwa .”