← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 111

Sashe 55

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bangaren maryama har qarfe d'aya na dare idanuta sun kasa runtsawa ta yunkura ta tashi ta zauna sosai a tsakiyar katifarta ta janyo pillow ta rungume tsam a qirjinta tana going over maganganun mr ata tana son ta gano wata gaskiya da yake qoqarin boye mata ,wani bangaren na zuciyarta sai taji tana so ta yarda a cikin yanayinsa akwai alamun soyayya amma kuma acikin maganganunsa kwata kwata babu wata alama ,acikin kwayar idanunshi ma zaa iya tabbatar da akwai wani abu acikin zuciyarsa .”shiru tana tana tariyo irin kallon da yake mata domin son gano wani abu .”girgiza kai tayi tace “wad'an mugayen idanuwan nashi babu komai acikinsu sai tarin firgici "Idan kin san baki tashi aure ba a yanzu kar na qara ganin kin kula sultan magana ma ta fatar baki kar ya qara shiga tsakaninku dashi maganarsa kusan ta qarshe kenan to me yake nufi da hakan shi bai ce yana sonta ba sannan kuma zai ce karta kula wanda ya nuna yana sonta ."

Kwakwalwa maryama ta bude sosai  duk abinda mr ata ya fada sun samu kyakkwan mazauni acikin
zuciyarta ta rufe shayayyun idanunta ta jingina bayanta da jikin gado ta sake rungume pillown dake makale a qirjinta tana jujjuya maganganunsa tana kuma yin filla filla da su tana so ta fito da komai daga rami daya shige ya   fake a ciki, ta sake tariyo hirarsu da sultan  a kanta ta kuma hada da maganar sa, ta so ta  fahimci abubuwa da dama a kansa amma wani abu guda daya yafi komai girma, he is smart duk abinda yake yana yinsa da gogewa idan ba mugun karantarshi kayi ba bazaka ta'ba gane inda ya dosa ba , maganar sultan kuma  wannan ba wani abun damuwa bane a wajenta  saboda a yanzu ba soyayya bace a gabanta kamar yadda ta sheidawa mr ata bare tayi tunanin aure a nan kusa , abu daya yake tsaye a cikin zuciyarta wanda yasa  kwakwalwata ya kasa samun kwanciya shine yaya sadam dinta da take jin har yau cewar yana raye ."

Washegari maryama bata samu zuwa office da wuri ba sai wajajen karfe goma da wasu mintuna dan tuni duk wani maaikacin dake aiki a qarshin AGC yana cikin kuma yana kan aiki jiki a sanyaye ta shigo office dinsu bakinta d'auke da sallama ta gaishesu ta cire jakarta sannan ta samu waje ta zauna tare da yin shiru tana kallon sauran abokan aikinta da suka dukufa suna kan aiki madam some ta shigo tace "sai yanzu maryama ?me yasa baki d'aukar aikinki da mahimanci ai shikenan daman idan kana jin mugunta bakayi wa kanka ba ai baka cika mugu ba. "maryama ta kalleta a kaikaice sannan tace "madam please me haka yake nufi ?"ina nufin duk ranar da sir ya gaji da halinki ya dakatar dake kinga ai kanki kika cuta ,"maryama ta numfasa sannan tace "duk abinda Allah ya hukunto akaina daidai ne "ai shi kenan kuma daman muslim’s din nan haka kuke da taurin kai ,ga aikinki gobe zaa kar'ba idan kuma kingama shi a yau mrs ata zai ji dadi maryama tasa hannu ta kar'ba tana cewa me zaa zana? ahankali madam some ta soma mata bayani tana gama mata bayani ta fita ."

Maryama ta mike ta dauki jakarta ta fice daga office din ta koma qasa  office din da'aka maida ema.
yayi matukar mamakin ganinta amman dake bai san zuciyar mr ata bace kawai ya sakar mata murmushi yana murnar ganinta wunin ranar  tana tare da ema inda mr ata bai sanyata acikin kwayar idanunshi ba amman dai ance masa tazo kuma har an bata aiki  sai dai bai nemeta ba duk da kwayar idanunshi ita suke son  gani amman ya danne saboda kar ya bada kofar da wasu zasu fahimci halin da yake ciki ."
karfe shida daidai maryama ta hawo sama ta ajiye aikinta a gaban madam some dake zaune tayi mata sallama tace zata  wuce gida tana gama fadar hk ta juya bayanta ya hango daga inda take zaune tana rausaya kmr ba daga wacan jagwal gwalaliyar unguwar take fitowa ba komai mata tsab tsab kuma a natse . ya hard'e qafafuwansa waje d'aya yana cigaba da kallon yadda take juya sansar jikinta anya kuwa bazata koma saka asalin kamilalliyar suturarta ba ? dan irin wannan tafiyar ai sai wani yayi masa ganganci  ,haka ma the next day a kasa  tayi aikinta tare da ema duk yadda mr ata yaso  ya ganta taki yarda su had'u aranta tace "aiki take masa ba jikinta ta kawo masa ya dinga ta'bawa ba yana yin yadda yaga dama ita ba ."

Tsawon kwanaki biyu  kenan bai sanyata acikin idanunshi ba sai dai ya hangeta daga nesa ta shigo ko ta sauka hankalinta ma gabad'aya baya Kanshi tsabgar gabanta kawai take, yana zaune akan kujera sanye da riga da wondo blue sai yar cikinta light blue yayinda nick tied dinsa ya kasance brown colou hannunsa rike da wani nicktie din brown yana nadewa ahankali har ya gama ya soka cikin aljihun gaban rigarsa yana kallonta ta shigo office din some . gata ga office dinsa amman ko d'aga ido tayi ta kalli office dinsa batayi ba haka yana kallonta ta juya yaga ta nufi qasa wani zazzafan numfashi ya sauke sannan ya yunkura ya mike ya fito ya biyo bayanta  tana zaune  tare da ema da wasu ma'aikatan  takalmansa ya shigo office din  ,kamshin sanyayyen turarensa daya ziyarci hancinta da kuma bugun da zuciyata yayi ne  ya tabbatar mata da shine ya shigo "good morning sir "!!! duk ma'aikatan dake cikin office din sai daya  gaishesa illa ita qoqarin juyowa take ta gaishesa taji sautin muryarsa a zafafe "ke me kike yi anan ? cikin tsananin firgita, da tsinkewar zuciya da tsoro, tare da kyarman jiki, ta qarasa  juyowa  ta fuskanci inda yake tsaye sanye da suit  yayi matukar kyau kamar wani matashi dan shekara talatin” just  one second na baki ki tattara ki koma inda aka ajiyeki. tamkar gilmawar walkiya yaga ta zabura ta mike ta rungume  jakarta da kayan aikinta gam-gam cikin tsuma da karkarwa ta bace .

wani irin masifeffen dariya ne ya taso masa tun daga kasan zuciyarshi har zuwa kan lips dinshi amman dole ya taune lip din shi na kasa kana  ya gimtse ya murtuke fuska cikin tsare gida yace.ema "! yes sir ya fad’a cike da girmamawa “da alamun kagaji da aiki damu ko ?"no sir wallahi babu ruwana sir bance .."
“enough! ya d’aga masa hannu “to be your last warning. iya abinda ya fad’a kenan ya juya ya koma office dinsa sai lokacin hankalinsa  ya dawo gangar jikinsa  duk lalacewa ko wani abu bazai had'asu ba gara tana sama yana kallon duk abinda take ."ranar kusan tare ma sukai aiki akan presentation dinsu dake motsawa ,yadda bata sakar masa fuska ba haka shima wanda daman shi kusan fuskarsa a daure take .”aiko ta gane bata da wayo dan ya lafta mata aiki kamar me dan haka a matukar gajiya ta qarasa gida tayi wanka tayi magriba da isha’i saboda tsananin gajiya ma bata ci abinci ba ta kwanta.”

******

Yau ne ya kama zaa gabatar da presentation zaune mr ata yake tare da client dinsa mutun uku a gidan mami   tun daga sama yasa akayi decoration har zuwa kasa surayya ce ta fara fitowa sanye cikin riga da siket na suit tayi juyi kamar yadda yan fashions desings keyi sannan ta koma gefe ta tsaya sannan  yusura ma ta fito tayi Kmr yadda surayya tayi mutun na uku some ce sai wasu maikata guda biyu sai maryama wacce ta sauko cikin doguwar riga ta rike gefen rigar kad'an tana rausaya tamkr wata fure wani murmushin ne mai daukar hankali kwance akan fuskarta wanda ya bayyana wushiriyarta da dimples dinta ,tayi matukar kyau sosai  mr ata ya gyara zama yana kallonta tun daga samanta har qaraso saukowa kwayar idanunshi na kanta .”
Mutane da suka zo ganin new design dinsu suaki tafi yayinda mutun daya acikinsu yace "wooo gsky naji dadin ganin representation dinku yayi min kyau sosai thank you so much mr ATA "wannan desings din ya bambamta da sauran desing daka saba kazo da wani salo dabam daman kuma ina da yakinin AGC company ne kawai zatayi min abinda zai kwanta min arai akan kowani kamfani dan haka akan wannan suprisse din zanyi double din order kaya."

" that's great mr ATA ya fada tare da mikewa tsaye yace "just a second !yasa hannuwansa a aljihun wondon suit dinsa ya qarasa inda yammatan suke tsaye "sannuku da kokari aikinku yayi kyau "thank you sir suka hada baki gurin fadar haka" sir ko zamu iya zuwa mu canza ?yes of course" ya fad'a yana kallon cikin kwayar idanun maryama tayi kyau matuka itace ta fara yin hanyar sama yabi bayanta da wani shu'uminn kallo tare da yin taku a hankali yabi bayanta da kallo ,jikinta a sanyaye ta dan juyo dan kallon bayanta ai kuwa ta zame tayi baya luuuu zata fadi kan tayis aiko da wani irin sauri mr ata yasa hannuwansa duka ya tarota bayanta ta fado jikinsa ."

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 26
Chapter 55 · 0% Book details