← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 111

Sashe 7

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

numfashi ta sauke da karfi sannan ta numfasa ta riko hannunsa ta zaunar dashi a gefenta kana ta fara magana cikin salon hikima irin nasu na manya “kowani bawa dake rayuwa acikin duniyar nan yana da matsala ,mutane mabam bamta amman akwai wasu matsalarsu bata kai ta wasu ba dole duk wanda zakayi muamula dashi sai kayi hakurin zama dashi saboda duk dan Adam yana tattare da matsala kawai na wani ne yafi na wani ,dan haka shi mai wannan fikira idan kaji har acikin zuciyarka ya samu matsuguni karka damu da matsalarsa dan matsala bata qarewa arayuwar d’an adam hakuri zakayi ka janyosa ajiki ka bashi kulawa idan akayi sa’a sakamakon hkn sai kaga matsalarsa ta ragu sannan km ka amfana da fikirarsa kaga anan ma ka samu riba biyu ka sanyashi ya samu natsuwa sannan ka amfana dashi na baka amsar tmbyrka ko nima zan iya tambayarka ?”tsura mata tsumammun idanunshi yayi yana kallonta haka nan yaji zuciyarsa ta gargadesa da kar ya yarda tai masa nata tmbyr dan haka ya girgiza mata kai alamun a’a “ok mr ATA muje kaci abinci ammi ta kwalla ma tabawa kira har sau biyu .”

cikin kankanin lokaci ta bayyana sanye cikin doguwar riga tace “mami gani !“muje kiyi serving din Adamcy abinci cewar mami kai kuma muje ko ? “no sweetheart barni kawai anan “shikenan bari akawo maka abincin nan bai yi mgn ba ya runtse idanunshi shi kad’ai yasan me yake ji a gangar jikinsa damuwarsa ta ninku fiyye da can baya “mami ta janyo qaramin table gabansa “adaidai lokacin da mai aiki ta qarasa da d’an hanzarin gudun karta tafi da sauri ta sha zagi a gurinsa mami ta mike tabi bayanta .”a natse take komai duk bai motsa ba ta wuce taje ta tsaya kusa da mami “mami !naam !”wani abinci zan zuba masa ? Kinsan shi yafi son shimkafa ki zuba masa kiyi masa plet din salad dabam ta amsa da to ta yi Kmr yadda mami tace ta d’auka ta kai Kan table din gabansa ta ajiye har ta juya tayi taku biyu taji sautin muryarsa a dake “Ke!ta tsaya cak hantar cikinta na wani irin kad’awa yayinda jikinta ma ya d’auki rawa ta fara sauke numfashi da karfi tana addua allah yasa ba wani laifi tayi masa ba “ba dake nake mgn ba ?ta juyo da wani irin sauri ta tsura masa ido abun mamaki idanunshi a runtse suke cikin hanzari mami ta qaraso wajen tana cewa “Lafiya Adamcy ? numfashi ya sauke yana bud’e idanunshi akan mami “kiyi tafiyar ki sweetheart tace “to ! ta kama gabanta sai dai duk hankalinta na kansa ya kalli mai aiki cikin isa da kamewa “ meye aciki ?muryarta cike da tsoronsa tace “rice and stew “.daukesu bana bukata?” shiru tayi can tayi karfin hali ta kwantar da murya tace “yalla’bai to me zakaci ai sai a dafa maka komai ka kake so ?ware idanunshi yayi sosai “waye zai ci jagwalgwalonku I think you’re cray.”

tace “to yau kuma abun ya motsa ta koma da baya ta kame tana cigaba da addau acikin ranta allah yasa maganarta bata hassalasa ba yaje ya koreta ta shiga ukunta bai qara magana ba ya tashi ya canza wurin zama ta kwashe komai ta maida kitchen tana yiwa mami bayani “barni dashi bari naje na samesa dan da alamun yau rigima yake ji “Adamcy nah ya’akayi kuma kace baza ci abincin ba ?yatsina face dinsa yayi “am not feeling eating any…”haba Adam ka dinga qoqarin bawa cikinka hakinsa ko na dafa maka kusku ne ?kamar yace “a’a !sai kawai yaji tausayin mahaifiyarsa ya kamashi tana matukar kula dashi da rayuwarsa dan haka ya gyad’a mata kanshi kawai tamark wani qaramin yaro.” ta juya ta koma kitchen da sauri tana kiran tabawa tazo ta tsaya kusa daita “ dauko min abubuwan da zamu had’a joluf din kuskus zan masa a natse mami take yin komai cikin kankanin lokacin ta dafa masa joluf din kusku wacce ta wadatu da korrot,green beans da kayan kamshi hanta da koda a madadin nama nan da nan kamshi curry da tyme ya soma tashi kusku din yayi kyau sosai sannan tace maza tabawa d’auko ki biyoni dashi “.

Turus mami tayi tsaye sakamakon rashin ganin ata a inda ta barshi “ina kuma yayi ?tayiwa kanta tambayar “kardai fita yayi ?Aa bazai fita adaidai wannan lokacin ba sai dai idan dakinsa ya koma kai tsaye hanyar step ta nufa inda mai aiki tace “mami na biyoki da abincin ne ?”eh tabawa biyo dashi da hanzari mami ta tura kofar parlour’nsa tare da sallama taga baya nan wani yawu tayi qoqrin hadiyewa sannna ta dakatar da tabawa da cewa ajiye tray kiyi tafiyarki ta nufi d’akinsa nan ma baya nan ta sake fitowa da sauri ta shiga d’ayan bedroom dinsa tsaye ta gansa ya rungume hannuwansa duka a saman faffad’an qirjinsa ya tsurawa zanen hoton maryama ido a tsorace take kallon bayansa inda shi kuwa yayi zurfin cikin tsananin tunaninta “bazai iya hakura daita ba tabbas soyayyarta tana da matukar tasiri a rayuwarsa ,ji yayi kamar da ba sonta yayi ba a yanzu ne ma ya fara sonta yayi shiru tare da runtse idanuwansa sosai yana kiran sunan Allah zuciyarsa na sake nitso acikin tafkin qaunarta ” a hankali ya bud'e idanuwanashi wanda suka kad'a sukayi ja saboda wannan qaddarar tafi komai yi masa ciwo acikin rayuwarsa a fili kuma cewa yayi "adam ka hakura daita karka kuskura ka shiga hurumin Allah ballantana ka bayyana mata  soyayyarka bare ma kasan yarinyar nan bazata soka ba sakamakon abinda kayi mata. bugu da qari kuma matar wani ce Ya qarasa maganar wasu hawaye masu zafi suna saukan masa akan kumatunshi “wace yarinyar ce matar wani ?yaji saukar muryar mami ?daga sama cikin sauri ya share hawayensa dan kar mami ta gane halin da yake ciki a dan tsorace yace “amm ..” sai kuma sai yayi shiru yana tunanin abinda zai fad’a mata dan bai iya karya ba duk abinda zai fito daga bakinsa to gsky ne “.

mami ta tsura masa ido jikinta ya kama rawa numfashinsa ta hango yana fita da karfi saboda zubar hawayensa “kayi min bayani wai meke damunka ne kake zubar da hawaye?ko dai har yanzu matsalar yarinyar nan ce ?shiru yayi ya kasa cewa komai dan bazai iya mata karya ba kuma bazai iya fad’a mata cewar ya ganta amatsayin matar wani ba .”mami batayi mamakin shurin da yayi mata ba domin tasan halinsa a duk lokacin da yayi shiru haka baya son fad’ar gsky abinda ke cikin ransa ne tana kallonsa ya nufi kofar fita jiki a sanyaye ta biyo bayansa alokacin da ya samu waje ya zauna akan kujera ya d’aura kafarsa d’aya akan d’aya yana kallon saman parlour’n yana cizan lips dinsa dan shi ne kawai abinda yake ganin zai iya yi a halin damuwar da yake ciki dan zuciyarsa tafarfasa take ta sake nitso acikin tafikin qaunar maryama .”ahankali ta zauna a gefensa “adamcy ga abincin kaci kar yayi sanyi lumshe tsumammun idanunshi yayi ,shi dai baya jin zai iya sakawa cikinsa komai bashi da wannan kuzarin ,bashi da wannna natsuwar ,bashi da wannna ‘yancin tun da ya rasata yasan ya rasa komai nashi bazai sake morewa ba ko kuma yace rayuwarsa tazo qarshe dan idan babu ita cikin rayuwarsa shima babu shi .”

sunkuyar da kanshi yayi kasa yana kallon zara zaran yatsun qafafunsa masu kyau da haske “shikenan wahalar bazan nayi adamcy bazakaci komai ba ?shiru yayi batare da yace mata qala ba “sanin halin yanayinsa tamkar mai nasaba da jinin sarauta yasa ta matso da table din da tabawa ta daura tray abinci akai gabansa tana cewa “yau dai da alamun miskilanci ya motsa?” ta fad’a tana bude masa kula abinci tana zolayarsa sannna ta mike ta qarasa inda fridge dinsa yake ta bude ta dauko ruwa mara sanyi sosai tazo ta ajiye masa kallonta yayi cike da tausayawa yana wahalar da mahaifiyarsa over “kiyi hakuri sweet heart .” dakayi me adamcy ?ina wahalar dake dayawa “babu komai Allah yayi maka albarka ni dai fatana da adduata Allah ya yaye maka tunanin yarinyar nan dan idan akwai abinda ke cin raina bai wuce naga ka zauna kana bata lokacinka akan tunaninta ba .”numfashi ya sauke kawai batare da yace komai ba “nifa banga abun so a wajen wannna aljanar yarinyar ba bai san ya akayi ba murmushin ya bayyana akan fuskarsa yana cewa aljana kuma sweetheart?sosai ma kuwa aljana ce mana shiyasa kullum nake nemar maka tsari daita domin tana cikin ta bada gudunmuwar rabuwarka da matarka da har yanzu baka waiwayi inda take ba, ga tsohon ciki haihuwa yau ko gobe ina ganin ma kusan tare zasu haihu da auta “rayuwar maryam na matukar bani tausayi adamcy domin nasan duk abinda tayi ba da son ranta bane tursasata akayi bugu da qari soyayyarka ..”

Lumshe idanunshi yayi na second biyu sannan ya bud’e yana kallonta a tsanake dan shifa sam ya manta da wani labarin wata maryam arayuwarsa dauke da ciki sai yanzu da tayi maganarta “sweetheart !ya kira sunanta “na’am adamcy ka tausayawa maryam tana bukatar tausayawarka “dan Allah sweetheart ki bar maganr wannna yarinyar ta rigada ta zama tarihi arayuwata ita kuma aljanar da kike magna akanta itama an bar tunaninta kai na ma cireta arayuwata sai yanzu na fahimci cutar da nayiwa kaina akanta na ‘bata tsawon shekaru akan abinda ba samu zanyi ba yayi maganar cike da raunin zuciya “alhamdulillah Allah na gode maka kai gsky ka wanke min zuciyata yau “yanzu dai ka fara cin abinci!babu mutsu ya fara cin abinci a natse ficewa Mami tayi daga dakin ta sauko zuciyarta cike da farinciki shi kuwa bayan fitarta kasa cigaba da cin abinci yayi ya kai tafin hannunsa ya shafa sumar kanshi zuwa fuskarsa ya had’a tagumi yana tunani .”
duk inda ya motsa yarinyar yake ji acikin ransa ji yake tmkr ransa zai bar gangar jikinsa ranar dai kwana ata yayi yana juyi da tunanin maryama sai yayi kamar ya saita tunaninsa yayi amfani da karfinsa sai ya sake shawara saboda jin tsoron allah duk yadda ya kai ga sonta bazai iya taka dokar Allah ba .”
Chapter 7 · 0% Book details