← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 111

Sashe 69

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wannan yarinyar bazata fahimceni ba saboda soyayyar wannan mataccen mutumin yayi tasiri acikin zuciyarta sannan kuma akwai abinda nake gudar wa rayuwarta dan ga dukkanin alamun rayuwar datai abaya cike take da tashin hankali da qalubali banason na kawota cikin ahlina ta fuskanci wani tashin hankali , shiyasa nake son nabi komai ahankali kafin na killaceta agidan dan bazan yarda kowa ya takata ba haka zalika itama bazan yarda ta taka min yan’uwana ba ,sannu ahankali suna tautaunawa har suka kawo AGC ."bayan direba yayi parking atare suka fito suka tsaya ajikin mota "bayan kamar minti goma oga amar ya qarasa inda yayi parking din motarsa ya shiga ya wuce shi kuma ya nufi ciki ."maryama nã tsaye da madam some suna magana akan ciwon hannunta mr ata ya qaraso da sauri madam some tayi masa sannu da zuwa ya amsa aciki batare daya kalli inda maryama take ba ya nufi kofar office dinsa yana cewa madam some "kawo min coffee."cike da girmamawa tace "okay sir ta juya ta bar maryama tsaye tana kallon bayansa mutun kullum cikin zafin zuciya kamar bashi ne jiya ya gama narke mata cike da tausayawa ba sai gashi yau ko kallon inda take bai yi ba bare ma ya tambayi lafiyar hannuta taja "tsaki tana duban hannu mai ciwo ."

cikin kankanin lokaci madam some ta had'a masa coffe ta nufi office dinsa ta ajiye masa cup din a gabansa tana cewa "ga coffe din sir”.sannan ta ja ta tsaya a gefe guda ya d'ago tsumammun idanunshi ya kalleta yana tsuke bakinsa sannan ya motsa lip's dinsa kamar mai koyon magana yace "zaki iya wucewa ta juya a natse ta fara taku yace" ummm kice maryama tazo nan da 30 minutes "okay sir ta qarasa fita da sauri ."ya kai hannu ya d'auki cup din coffe ya kai bakinsa yana kur’ba ahankali yana lumlumshe tsumammun idanunshi kana yana nazarin abinda ya dace yayi ."mikewa yayi hannunsa rike da cup ya rasa abinda ke masa dadi dan ransa yayi matuqar baci da rashin amincewar baba gali ,sosai kwakwa
Luwarsa ta dinga tunanin neman mafuta dan dole yasan abun yi kafin wani yazo yayi masa shishigi da shigar sauri ,ahankali ya soma zagaya office din “adam dan dole ka nemawa kanka mafuta to mai zan yi yanzu ?”mai zanyi?” dole dai idan ina son mallaka
r maryama sai na sheida mata kamar yadda baba gali yace ,amman taya zan fuskanceta har na iya fad’a mata ina sonta da aure ?”ka bata umarni kawai kenan nace maryama kisoni ki aureni bisa dolenki ?“No no impossible hkn bai yi ba shiru yayi yayinda ya ajiye cup din hannunsa ya shiga d’aya daga cikin dakun nan dake cikin office dinsa ya zauna akan kujera yana sauke numfashi kamar wanda yayi gudun tsere .”

Jikin baba gali a matukar sanyaye ya shiga bangarensa inda zuciyarsa ke wani irin bugawa da qarfi,yayinda aunty salma dake tsaye tace " ba dai har bakin naka sun wuce ba?"ya gyad'a mata kai tare da cewa "sun wuce salam !.”ya fad'a tare da samun guri ya zauna yana jin kanshi na sarawa bai ta'ba jin wani abu na farinciki ya samu maryama wanda ya haddasawa zuciya da gangar jikinsa shiga rudani da tashin hankali ba sai wannan." ganin yanayinsa yasa jikin aunty salma yayi sanyi ,dan haka ta matsoshi tace "wasu irin baki ne suka zo wajenka ?"kuma me ya kawosu ?”dan naga jikinki yayi wani iri ?dafe goshinsa yayi da hannu d'aya yana ciza labbansa yana sake jin tashin hankalinsa na nunkuwa agaresa .aunty salma taje ta kawo masa ruwa mai sanyi ta mika masa "ka sha ko kadan ka ji sanyi kafin ka sheida min meke faruwa dan lallai akwai abinda ke faruwa dan ban ta'ba ganinka haka ba ,dan ko dakatar da kai da umman sadam tayi banga ka shiga damuwa da tashin hankali irin haka ba."bai mata mutsu ba yasa hannu ya karba ruwa mai sanyi ya sha kad'an ya ajiye kofin din a gabansa ita kuma ta zauna kusa dashi "ina jinka bani labari meke faruwa da kai ?"shiru yayi "dan allah ka fad'a min dan shirunka ya fara sakani jin tashin hankali ."

numfasawa baba gali yayi kana ya cire hannunsa daga goshinsa ya soma bata labarin halin da yake ciki ,suman zaune aunty salma tayi a wajen kamar wacce aka dasata tsabar tashin hankalin data shiga ai baba gali yana gama labarta mata komai tsoro da matsanancin firgici yaga ya bayyana akan fuskar aunty salma wanda babu tantama yasan na tsananin firgita ne daman kuma yasan zai iya ganin fiyye da haka atattare daita muddin taji ".cike da tsnanin tashin hankali ta fashe da kuka tana cewa "nashiga uku wannnan babban mutumin ne ke son auren maryma "?tabbas salma shine kuma wallahi ga dukkanin alamun mutumin nan yana mutuwar sonta ."wani irin bugawa zuciyar aunty salma tayi ta soma kuka wiwi baba gali ya matso kusa daita yana girgiza mata kanshi alamar kartayi kuka hannunsa yasa ya share mata hawaye kuka take sosai har numfashinta ya soma qoqarin tsayawa tace "to kai me kace masu ?"ajiyar zuciya baba gali ya sauke yace "me kuwa zan ce masu daya wuce ban yarda ba kuma ban amince ba, dan tarin dukiyar da zasu bani bazai rage min radadin bakinciki da nake ji ba . ban barsu sun wuce ba sai dana tabbatar masu bazan masu wannan alfarmar ba,amman ni tsorona kar yaje su daidaita kansu da maryama din.”dan wallahi naga gabad'aya yanayinsa ya sauya alokacin da yayi maganarsa ta qarshe kinga kuma idan yaje ga maryama ta amince bani da uzurin da zan sake basu ."

cikin tsananin tsoro aunty salma ta sauke numfashi tana cewa "dan ubanta bata isa ta amince ba wallahi kuma bata isa ta taka wannan matsayin ba,wallahi muddin kaga maryama tayi aure to bana raye acikin duniyar nan , amman muddin ina raye ya'yana ne zasu rigata taka kowani irin matsayi ,kuji min tsinanniyar yarinyar kamar ita kadai ta kawo kan arziki duniya daga wannan ya wuce sai wannan yazo ?”wallahi salma ni kaina na firgita matuka da jin wannan alamarin da mun sani tun farko kin bar malam yahuza ya aureta mun huta da ganin wannan bakinciki .aunty salma ta share hawayenta tana dubansa karka shiga damusa in dai akan wannan matsalar ne ,ka yarda dani zan sa ayi aikin da duk duniya babu wanda ya isa yaga maryama yace yana sonta bare ma ya aureta, shi kuwa wannan mutumin sai ya dawo yana nuna mata zallar qiyayya daga yau bazai sake takowa zuwa wajenka da wannan zance ba ."aunty salma ta fad'a idanuwanta na kan baba gali dan murmushi yayi wanda yafi na kuka ciwo yace" na yarda dake salma, kiyi duk yadda zakiyi ya manta daita, me malamin nan yace miki akan yusif?"bar dan barouban yaron nan shima da kayan takaici sai aiki yayi kamar zai cisa sai kuma ya karkace ko da yake malam yace “bashi da laifi uwarsa ce take tsaye akansa da addua amman mu zuba ido muna zaune zai kawo kanshi” to to shikenan Allah ya taimakemu maganr dai suka cigaba da tautaunawa a tsakninsu ."

Cikin nutuwarta ta ko yaushe  ta tsaya a gaban kofar office dinsa sai dai bata hangosa ba bare ta nemi izinin shiga dan haka ta juya ta koma office dinsu inda ta baro madam some tace "madam naje banga mr ata acikin office din ba, may be ko ya sake fita ne "no no !! bai fita ba ,ki shiga ki jirasa zai fiyye miki akan ya ganki anan “maryama bata mata mutsu ba ta sake juyawa ta tura qofar office din ta shiga da siririyar sallama tana  hadiye wani yawu sannan  tana gogarin daidaita numfashinta da nutsuwarta dan wani irin qamshin turarensa office din yake mai bugar da zuciya .kusan mintuna shabiyar tana tsaye babu shi babu alamunsa dan haka  ta nufi wata qofar  data gani a bude dan tayi tunanin yana ciki  tayi knocking ahankali sbd sanin bayason hayaniya. Jin shiru yasa ta sake knocking din amma shiru dan haka ta juya ta tsaya tana cigaba da jiransa tare da sunkuyar da kanta qasa tana wasa da yatsun hannunta ,kusan minti biyar tana tsaye bai shigo
ba kuma bata ji alamun yana ciki daya daga cikin  dakunan dake cikin office din ba , kai tsaye tayi tunanin qila baya nan ne dan haka ta  harzata
juyawa da zumar barin office din sai taji motsin bude qofar  ta juyo da sauri , ya qarasa fitowa hannunsa d’aya rike da qugunsa yayinda gaban  rigarsa ke bude har tana iya hango fara singlet din da yake sanye ajikinsa .”

a matukar tsorace take kallonsa kwayar  idanuwan
ta ya shiga cikin nasa da sauri ta juya masa baya sakamakon cin karo da tai da qirjinsa duk ilahirin jikinta da muryarta na rawa tace  "madam some wai kana son ganina.” ta qarasa maganar tana duban hannunta mai ciwo bai ce daita  komai ba har lokacin kallonta yake yana jin wani irin zazzafar sonta na fixgarsa ya mugun tsura mata idanunshi yana kallon yadda numfashinta ke fita da garfi .” kujerarsa  ya nufa ya zauna tare da gyara hannun  longsleev din dake sanye ajikinsa  tai shiru tana duban duk abinda yakeyi komai yayi kyau yake masa tana kallonsa ya janyo wayoyinsa guda biyu dake kashe ya  kunna sanin yadda yanayinsa yake tamkar mai  jinin sarauta haka  yake yasa ta matso gabansa a natse tace "sir ko akwai aikin da zanyi maka ?"no !” ya fad'a atakaice yana danna bell ,cikin second biyar madam some ta shigo "miko min ruwa mara sanyi "okay sir !”ta qarasa ta bude fridge ta dauko ruwa marasa sanyi sosai tazo ta ajiye masa "you can leave
Chapter 69 · 0% Book details