← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 111

Sashe 82

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ahankali maryama ta mike ta nufi kofar office dinsa ta turo kofar ta shigo ta tsaya a gabansa tana gaishesa “good morning sir ?” a natse ya d’ago tsumammun idanunshi wad’an da suka wadatu da gashin ido dana gira ya zuba mata tare da yin shiru yana sauraronta itama shiru tai tana kallonsa tana wasa da yatsun hannunta ganin irin kallon da yake mata yasa babu shiri ta sunkuyar da kanta qasa ta cigaba da murza yatsun hannunta dake tsarke cikin juna ta sake d’agowa ahankali fuskarta d’auke da murmushi amman nan take murmushi ya d’auke a fuskarta sakamakon ganin fuskarsa a had’e tamkar yadda ya shigo ,kwatakwata fuskar nan babu alamun fara’a bare annuri akan fuskarsa ,dole tasa ta shanye dukkanin wani farinciki da take tattare dashi .”

shiru tayi tana zazzare idanu kusan mintuna shabiyar bai ce mata kala ba itama bata iya ce masa komai ba tana dai tsaye a gabansa tana kallonsa ya mike tsaye ya zagayo ya wuceta tsaye ya shige d’aya daga cikin dakun nan dake cikin office din .”qirjin maryama na wani irin dokawa ta juyo da sauri tabi shi da kallon mamaki tamkar bashi ne jiya ya dinga bata kulawa ba “karfa yayi tunanin wani abu akanta alhalin ita tazo ne dan yi masa godiyar taimakon da yayi mata ,yayinda sultana wacce idanunta ke kansu tai murmushin jin dadi yadda yayi mata wulakaci “kad’an ma kika gani dan dole yayi miki wulakanci tunda ya rigada ya gama more miki albarka jiki ,amman kuma sultana ki natsu da kyau zai iya zamowa pretending yayi dan kwayar idanunshi kad’ai idan kika kalla kinsan akwai zazzafar soyayyar yarinyar acikinsu sai dai ga dukkanin alamun bai sheida mata ba ,kamata yayi ki bari maryama tasan irin son da kike masa ta haka ne kawai zata janye jikinta daga nashi .”

Wani irin wahalallen numfashi maryama ta sauke ta soma magana da zuciyarta“ki sharesa kawai ba sai kin masa godiya ba ,no no hakan bazai yuwu ba ga mutumin daya tayaka jin pains dinka ,mutumin da yayi qoqarin cire maka damuwar dake cikin zuciyarka ai ko babu komai ya cancanci kayi masa godiya koda kuwa bazai amsa ba.jiki a sanyaye ta fito daga office dinsa zuwa nasu ta tsaya dan gabad’aya ta kasa samun natsuwa bare ta zauna tunanin abinda zata kawai take “to ni yanzu me zanyi ? ” me zanyi “?yauwa nasan me zanyi !ta furta a fili lokacin data furta hakan sai da kowa dake zaune acikin office din ya kalleta .”da sauri ta dauki jakarta ta fita daga office din inda sultana ta mike da sauri tabi bayanta tana son taga inda zata.”ganin ta fita daga maaikatar gabadaya yasa ta dawo .”

Maryama bata d’auki wani lokaci ba ta dawo still dai ta kasa samun natsuwa dan ko aikin da madam some ta ajiye mata bata bi ta kansu ba babban burinta tai masa godiya sultana ta kalleta a tsanake “meke cikin zuciyar maryama yau kamar tana son furta wani abu mai mahimanci ga yaya adam I most find what’s the matter maryma ta sake kallonsa alokacin daya fito yana waya “ni na rasa ma me zanyi gabad’aya yanayinsa yau ya bani tsoro ta fad’a a zuciya inda sultana tazo ta tsaya a kusa daita tana cewa “lafiyarki kuwa maryama “?“me kika gani ?maryama ta tambayeta fuskarta babu yabo babu fallasa “abubuwa dayawa na gani !” “sultana abubuwa dayawa kuma ?”maryama ta tambayeta, ta gyada mata kai alamun eh “amman kuma babu komai ai,” amman me yasa kika kasa zaune kika kasa tsaye kike ta zariya office din d’anuwana bayan nasan babu aikin daya baki ?”am babu komai sultana kawai dai Ina son na gode masa ne saboda ya taimakeni.” tayaya akayi ya taimakeki ki fad’a min dan ina son sani “?mr ata yayi min taimakon mai girman da wani dan adam ya kasa min a jiya na d’auki tswon lokacin ina cikin damuwa sakamakon mutuwar mijina amman a jiya yayi silar yaye min wannan damuwar ya taimakeni wajen dawo min da farincikina shiyasa nake son ganinsa na gode masa .”

murmushi sultana tayi tana cewa “wannan bashi ne asalin gaskiyar abinda ke ranki ba akwai wani abu dabam acikin zuciyarki da kika boye .”ta fad’a tana kallon tsakiyar idanun maryama “no sultana babu komai acikin raina bayan wannan karki manta mr ata matsayin mai gidana ne kawai dai godiya zan masa bayan haka wallahi babu komai acikin zuciyata “lallai ya tsaya amatsyain babu komai sultana ta fad’a mata hk cike da gargadi har maryama zatai magana sai kuma tayi shiru ta fasa cewa komai ta zaro takardar zanenta tana mamakin maganr sultana ”lallai ya tsaya amatsayin babu komai ta sake maimaitawa kanta maganar sultana na qarshe tana mata wani irin kallo mamaki to me take nufi daita ?.”

can bangaren mr ata kuwa kawo qarshen wayar da yake yayi da cewa “okay zan duba thank you sannan ya ajiye wayar ya maida tsumammun idanunshi zuwa ga glass din office dinsu maryama ,ya d’an kalleta yana jin wani irin magadisun sonta na shigarsa ,kafin ahankali ya mike yasa hannunsa d’aya cikin aljihunsa ya bud’e kofar ya fito yana cewa madam some “ina mukalan motocin da’aka kawo “?gasu anan sir !”okay biyoni dasu “okay sir ta bud’e doruwar data ajiye ta kwaso “kai tsaye office dinsu maryama ya shiga ya tsaya yana cewa “guy’s!gabad’ayansu suna ganinsa duk suka natsu suka tattara hankalinsu garesa cike da girmamawa madam some ta tsaya kusa dashi inda hankalin maryama da idanunta suke kanshi tana qare masa kallo tsab tare da nazarinsa tana son gano wani abu atattare dashi cikin tunanin da take ta soma jiyo sautin zazzakar muryarsa mai bugar da zuciya tare da sanya natsuwa a zuciya “some ki fara raba masu”. d’aya bayan d’aya some take mika masu keyn din motar benz new model “lokacin data kawo kan maryama yace “bani nata !”babu musu ta mika masa ya jefa cikin aljihunsa hakan bai damu maryama ba kamar yadda taga yanayinsa mutum kamar hawainiya kamar bashine jiya yay silar cire mata damuwa ba .”wannan shine kyautarku na presentation din da kuka gabatar “.nan take office din ya kaure da hayaniyar godiya ,yayi saurin dakatar dasu ta hanyar d’aga masu hannu “bana bukatar godiyarku sannan bana son ganin kowa yau din nan a office dina duk wanda yake da wata bukata ya samu some yana gama fad’ar haka ya juya ya fita inda maryama ta mike ta biyosa da sauri tana cewa “sir !”go back to your office …”

cak ta tsaya qafafuwnata na d’aukar rawa “me ke faruwa dashi ne yau ?” tayiwa kanta tambayar tana mai jin wani irin tashin hankali mai tsanani yana shigarta “bayansa ta cigaba da kallo har sanda ya qarasa shigewa office dinsa ya zauna jikinta a sanyaye ta dawo ta zauna inda sauran abokan aikinta ke cike da tsannain murna.”yusura ta matso kusa daita ta dafa kafadarta tana cewa “lafiya maryma meke faruwa mr ata ya bawa kowa kyautar mota amman ya hanaki ?”I don’t know yusura ban san meke faruwa ba bansan dalilinsa ba but is like sir his not in good mood today ki natsu sosai maryama kiyi tunani baki yi masa laifin komai ba dan bazai yuwu ace ya bawa kowa kyautar mota ya hanaki ba ?”tai shiru kawai tana tunanin mutumin da suka wuni dashi jiya kuma lafiya lafiya suka rabu dashi babu wata matsala kawai dai tafi tunanin miskilancinsa ne ya motsa. numfashi ta sauke da qarfi tana cewa” yusura kije kiyi abinda ke gabanki ni ban damu da kyautar motar da ya baku ba dan ko bai bani ba inada niyyar zan siya lokaci kawai nake jira ta qarasa maganar tana hura hanci tare da runtse idanunta tana mai jin zafin abinda yayi mata.”

Yana zaune rike da file yana dubawa maryama ta shigo office dinsa batare data tsaya neman izininsa ba ta tsaya a gabansa tare da goya hannunwanta duka abaya yayinda kwayar idanunta ke kansa muryarta a sanyaye tace “sir !”ya d’ago tsumammun idanunshi ya zuba mata sai data ji wani irin mummunar fad’uwar gaba sannan taji wani abu ya caki zuciyarta sai dai tayi qoqarin danne abinda taji a zuciya da sansar jikinta ta motsa lip’s dinta ahankali ta soma magana a natse “thank you for yesterday sir .”daman shine dalilin zuwana d’azu office dinka ba wani bane kawai ina son na gode maka ne bisa qoqarinka akaina domin ka dawo min da farincikina” shiru yayi kawai yana kallon kyakkyawar fuskarta da qaramin bakinta da burinsa a yanzu ya jisa cikin bakinsa yana sarrafasa tana gama fad’ar haka ta juya a natse ta nufi kofar fita batare datai masa maganar keyn motarta ba .”

ya ajiye file din hannunsa yana ya cigaba da kallon bayanta yaji kamar ana zarar ranshi ne a zaune da yake ,idanunshi na kanta har ta shiga office dinsu ta samu waje ta zauna ta soma aikinta batare da wata damuwa ba ,can bayan wasu mintuna duk abokan aikinta suka fita zuwa break ,office din ya saura ita kad’ai, ta mike a natse taje inda aka tanada masu ruwan zafi ta tara cup ta tsiyaya ruwan zafi ta had’a shayi ta soma sha ahankali tana lumshe idanunta ahankali mr ata ya tashi daga mazauninsa ya fito har zai karya kwana sai ya hango bayanta tsaye shiru bata ko motsi dan haka ya shiga office dinsu har lokacin tana tsaye hannunta rike da cup qamshin daddaden turarensa ne yasa ta juyo da sauri aiko taji tayi karo da mutu tsaye a gabanta da sauri ta d’ago shi din ta gani tsaye yana dubanta da tsumammun idanunshi gashi har ruwan tea ya d’an ta’ba masa gaban rigarsa a rikice ta soma cewa so..” sorry sir ban..”bansan kana tahowa ba.”
Chapter 82 · 0% Book details