← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 111

Sashe 45

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mr ata na zagaya parlour’nsa mami ta turo kofar parlour’n ahankali ta shigo tare da mai aikinta tabawa wacce ke d’auke da madaidaicin tray mai d’auke da kular abinci da flak’s sai qaramin cup da spoon nacin abinci dana shan tea, ahankali ta ajiye tray din akan qaramin stood, cak mr ata ya tsaya daga zagaya parlour’n da yake sakamakon shigo warsu,ya tsura ma mami tsumammun idanunshi yayinda ta’bawa ta juya ta bud’e kofa ahankali ta fita, idanunshi na kan mami har sanda tayi taku uku ta qaraso inda yake tsaye zuciyarsa cunkushe da haushin baba qarami “tsayuwar me kake yi ?tayi maganar cike da tausasawa bai ce mata uhm ba bare uhm “kamata yayi ka zauna.“sweetheart bazan iya zama ba saboda wani irin zafi da suya zuciyata ke yi min “shiyasa nace ka zauna domin ba’a son mutun yana tsaye tattare da fushi dan komai zai iya faruwa dashi “madadin ya zauna kamar yadda mami ta ce masa sai ya cigaba da magana cikin zafin zuciya “sweetheart baba qarami yana son yaga kalar nawa rashin mutunci ,so yake na murje idanuna nayi masa rashin kunya fiyye da nashi “ban yarda ba kuma ban amince maka ba kada naji kuma kada na gani ina mai umartarka daka kiyaye harshenka akanshi .”

“Sai data numfasa kana ta cigaba da magana atsanake “bazan daina fad’a maka ba, baba qarami uba ne agareka, indai zaka iya masa rashin mutunci tabbas zaka iyawa tariq mahaifinka da yana raye “.da sauri ya shiga girgiza mata kai yana mai runtse idanunshi gam dan jin zafi da ciwon abinda ta fad’a ya d’auki mintuna goma idanunshi na runtse sannan ahankali ya bud’e tsumammun idanunshi ya tsurawa mami dake tsaye a gabansa tana faman fad’a masa mahimanci baba qarami agaresa “sweetheart nasan mahaifina “ mahaifina bazai ta’ba aibantani ba .”bazai ta’ba min irin abinda baba qarami yake min ba “ya qarasa maganar kwayar idanunshi na canza kala tamkar wanda aka watsa garwashin wuta acikinsu .”Shiru mami tayi tana dubansa a tsanake domin dai gaskiya ya fad’a amman kuma duk da hakan baba qarami yana da qarfi iko da mahimanci arayuwarsa
Numfasawa tayi irin nasu na manya sannan ta riko tafin hannunsa cikin nata tayi taku biyu tace “zauna ka samu natsuwa “!cike da zafin zuciya ya zauna yana dafe goshinsa da hannunsa d’aya “adamcy !”Mami ta kira sunansa “yana jinta amman bai amsa ba dan ko yace zai yi magana a halin da yake ciki maganar ba fitowa zatayi ba .”

“Adamcy ka qara hakuri da yan’uwan mahaifinka “ka cigaba da ganin girmansu sannan kayi masu biyayya albarkasu albarka mahaifinka ce .”sai lokacin ya samu damar sarrafa harshensa “sweet heart ki daina fad’ar haka ki daina bani umarnin most especially akan baba qarami dan bazan iya ba kuma ko yanzu darajanki yaci .“ya qarasa fad’ar haka yana cire hannunsa daga goshinsa ya cigaba da magana “aiki kuma da yake magana a kanshi wallahi wallahi sweetheart sai anyi aikin nan kuma kafin time din presentatoin day in yaso yayi duk abinda zai yi bazan bi umarninsa ba dan ba ubana bane kamar yadda ya fad’a nasan mahaifina shima yasan ya’yansa.” shiru mami tayi kawai tana kallonsa har sanda ya dasa aya sannan tace “da farko dai na gode daya ci darajata kuma naji dadin yadda kayi masa daman kullum mutun yana girma yana qara hankalina ne a duk sanda zai zo maka da fad’ansa na umarceka da kayi qoqari ka danne zuciyarka wata sai labari Allah kuma yayi maka albarka .”

“Sai magana ta biyu zan so ka hakura da aikin nan kai idan ma da hali ka bar masu kamfanin gbdy.” “a’a sweetheart karkiyi min haka dan girman allah ki cire bakinki acikin lamarin nan ki barni dashi tunda abayan ya’yansa yake mutane sai son zuciya kullum basa duba cigabanmu sai abinda zasu samu “.ya fad’a yana jan tsaki tare da fesar da iska mai zafi .”
“Nasani adamcy nasani baba qarami baya maka adalci akan ra’ayinsa dana ya’yansa amman duk da haka hakurin shi yafi ka bar masu ba dan komai ba sai dan a zauna lafiya ”hankalinsa amatukar tashe ya zamo jikinsa ya durkushe a gaban mami ya risinar da kanshi sosai yana cewa “sweetheart kiyi hakuri kiyi min fatan alkhairi in sha allahu wannan aikin shine aikin da zanyi na qarshe a AGC na tattara na bar masu kamfanin gabad’aya tunda haka kike so kike buqata ,daman wahalar abbana nake duba ba akan kamfanin nan ya sha matuqar wahala akanshi kuma mutanen dake amfana da kamfanin nan suna dayawa idan nã barshi baba qarami da ya’yansa zasuyi hamdame komai tare da yin babakeri amman tunda kince na hakura nayi amman dan allah ki barni nayi wannan aikin kawai nayi miki alqawarin zan bar masu “.

shiru mami tayi tana nazarinsa gabad’aya baya cikin natsuwarsa bare a yanzu da take qoqarin hanashi yin abinda yake so ,zata iya barinsa amman ita bata son abinda zai zama damuwa da tashin hankali a tsakaninsu “sweetheart ki amince nayi aikin nan na miki alqawarin wallahi zan bar masu kamfanin jin haka yasa jikin mami a sanyaye tace“to shikenan na barka Allah yasa albarka allah kuma yayiwa rayuwarka albarka “Ameen sweetheart na gode .”ya fad’a tare da yunkurawa ya mike ya zauna akan kujera yana sauke wani sanyayyen numfashi yasan tunda mami ta amince ta kuma sa masa albarka to fa kamar yayi nasara ne akan wannan aiki sai dai idan mutuwa zasuyi su mutu amamn sai yayi nasara mami ta mike tsaye tana cewa “zan koma qasa kaci abinci idan kuma akwai abinda kake bukata ka kirani “okay !”ya amsa tare da mata sallama .”ya runtse idanunshi “layin maryama ya soma nema domin ya fad’a mata tazo da new designs din da sukai gobe sai dai abu daya computer take fad’a masa “swcthoff “!me kuma ya samu layinta da har yanzu akashe yake .”bai san me yasa take kashe phone dinta ba yaja tsaki .”

Shiru maryama tayi zaune rungume da pillow akan kujera a parlour’n umma tare da zabga tagumi cikin
zullumi da rashin sanin madafa, tunaninta abu 'daya tasani yau ma ta tafka babban laifin wanda babu mai kwatarta a wajen mr ata sai allah daya haliccesa shiyasa ma zuciyarta take mata gargadin barin aiki akarkashinsa amman kuma tana tsananin qaunar aikinta a yadda aiki ke wahalar samu a kasar nan tace zata bar aikin nan ai ta cuci kanta kuma tayiwa rayuwarta mugunta kuma daman malam bahaushe yace “idan har baka yiwa kanka mugunta ba hakika baka cika mugu ba “amman Kinsan da haka kike wasa da aikinki bayan kinsani mai wannna kamafanin yafi mahaukaci iya hauka idan abunsa ya motsa ,gasky maryama bakya kyautawa kanki ba ya dai kamata kisan mahimanci aikinki kiyi abinda yake so ki bar wanda bai so shikenan sai ki zauna lafiya dashi ahankali zuciyarta ta dinga mata fad’a akan abinda tayi “me ma yasa kika baro office batare da wani dalili ba ?” baki bar office da mr ata ba sai dan wata sultana din banza “.

shiru tayi yayyinda ta koma ta kwanata akan doguwar kujerar numfashi take saukewa kamar wacce tayi gudun tsare kanta ya shiga ya mutsawa kafin ahankali ta soma sakin murmushi alokacin da take tunanin mr ata wanda ta rasa dalilin haka dan kusan yanzu yana yawon shigowa cikin tunaninta babu abinda zatayi da bazai shigo ba wani lokacin halinsa dariya yake naunayen ajiyar zuciya ta sauke alokacin da taji sautin muryar umma kusa daita tana kiran sunanta .”
“Maryama bacci kikeyi ne ?”a’a umma idanuna biyu ta fad’a tare da yunkurawa ta zauna tana kallon umma ,umma ta zauna kusa daita tana jin wata irin qaunarta kamar itace ta haifeta musamman a yanxu da take hango tarin soyayyarta mai tsanani a idanuwan maryama dinta”yau kin dawo aiki da wuri fatan dai lafiya “?maryama tayi murmushi har wushiyarta ta bayyana kana tace “babu komai umma “amman kuma sai naga kamar akwai abinda ke damunki dan duk jikinki ya sake maryama tayi shiru “karki boye min kinji yar ummanta “.

“uhm !ta furta akasan makoshinta sannna tace “gsky umma kamar koda yaushe dana saba fuskatar matslaa da mai kamfanin AGC yau ma hakan ce ta kasance “wallahi umma na fara gajiya da takurawar sa ,wani irin bahagon mutun ne da bai da fahimta ga shegen taurin kan tsiya gashi ya tsaneni kamar ni kad’ai ke aiki a qarqashinsa ,duk sanda nayi aiki sai ya kushe min ko yace bai masa ba,ko kiga yana disgani kuma fa umma acikin mutane nan dai ta dinga korowa ummah halin da take da mr ata har da abinda sultana tayi mata a yau din nan sai dai ta kasa fad’awa umma cewar d’an sigari ne haka nan taji maganar tayi mata nauyin da bazata iya fad’a mata ba .”umma tayi murmushi irin nasu na manya sannan tace” anya duk wannan tarin qiyayya da tsana tare da tsamgwamar mai tsanani da yake miki bazata juye qaunar ba kuwa ?.”

Maryama ta zaro idanu waje da sauri tana dafe qirjinta da hannuwanta duka “umma rufa min asiri da yardar Allah ma bazata kasance ba koda zata kasance ma zan rusheta tazama babbar kiyayya dariya umma ta kwashe dashi tana cewa “kai maryama ya kika firgita haka da sauri ?dole na firgita umma dan dai baki san shi bane halinsa fa yafi wanda na fad’a miki muni wallahi kullum ina tausayawa matar dake aurensa dan nasan ba qaramin hakuri take dashi ba “ai irinsu kuma a wajen mata sauki kai garesu”umma ba dai wannan mutumin ba ,karfa wata rana soyayya tasa kizo kina yabonsa”kai umma kin dai kasa fahimtar irinsu mr ata bama zai ta’ba cewa yana son irina ba wacece ni tukun ma ?” ko girman kanshi bazai bari ba bare ma ni yanzu babu wani budget din aure a gabana so nake na d’an tara albashina na wata shida na siya mana wani qaramin gida mu tattara mu bar gidan nan mu canza emvaroment”.
Chapter 45 · 0% Book details