← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 111

Sashe 79

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“nadiya ya gani tsaye rungume da hannuwanta duka a qirji tana dubansa,da wani irin sauri ya riko hunnunta ya sanyata ajikinsa ya rungumeta tsam tsam yana sauke numfashi da ajiyar zuciya atare . bayan kamar second goma ya janyeta zuwa gefensa domin ya samu damar maida kofar ya rufe.”cike da tsananin son juna suka tsurawa junansu ido suna kallon juna kafin ahankali suka tsakarwa juna murmushi,sadam na cewa “banyi expecting zaki dawo lafiya ba , na d’auka shiri ne aka shirya miki dan a gano wani abu akanmu “nadiya ta sauke numfashi kana tace “sosai kuwa my heart shiri ne kamar yadda kayi expecting sai dai na nuna masu kwarewa domin kuwa na d’aurasu a wani bagire da bazasu ta’ba fahimtar Komai akanmu ba ,domin kuwa na shirya masu bayanan qarya kuma sun yarda da hakan kuma sun amince dani .”tana gama fad’ar haka suka samu waje suka zauna cike da kulawa sadam ya turawa nadiya tiran kayan marmari nan na gabansa sannan ya nufi fridge ya kawo mata maltina da ruwa mai sanyi" tare da tsura mata idanunshi .”

“Uhm fad’a min wani irin bayanan qarya kika fad’a masu ?”nan take nadiya ta shiga zayyano masa qaryar data fad’a masu tun daga farko har qarshe sannan ta qara da cewa ko kasan cewar maryama baqaramin tashin hankali ta shiga ba sakamakon jin cewar ni da kai masoya ne ?”ta fad’a tana wata irin dariya mai sauti ,”na tabbatar mata kai din nawa ne alokacin baya, amman kuma data lura alokacin da nake mata bayanin soyayyarmu,data fahimci har a yanzu ma kai din nawa ne amman dake wannan yarinyar mahauka ciya ce sai kuka take mai tattare da jimamin rashinka .”my heart sosai fa yarinyar nan ta kamu da sonka anya kuwa my heart wani abu bai shiga tsakaninku ba ?”domin kuwa a irin kallon da nayi mata da tawa fahimtar ta d’an dani dadin ka ne yasa ta damu da rashinka ?”fad’a min menene gaskiyar magana ka kusanceta ko .”?ta qarasa maganar fuskarta tana nuna alamun damuwa da kishi.”

Yaya sadam yayi shiru kawai yana kallonta da sauraronta cike da Jin haushin maganar haka ma zuciyarsa sam taji babu dadi kiran maryama da mahaukaciya datai .” karta ga ya guji kowa akanta ta nemi ta dinga ci masa fuska duk fa lalacewa maryama tashi ce kuma jininsa ce kuma har zuwa yanzu tana nan amatsayin matarsa “kin sha furta min wannan kalmar atsakanina da maryama ko mun d’an d’ani dadin juna ne yasa na kasa furta kalmar saki agareta,wannan kalmar baya damuna kamar kalmar haukan da kike danganta maryama dashi ,”karki manta dangan takata da maryama ,ni daita dagin juna ne da suke da tsananin shakuwa amman ina son daga yau wannan kalmar ta zamo qaro na qarshe da zai sake fitowa daga bakinki shiru tayi tana kallonsa da bayanannen mamaki “yes karki sake dangatata dashi banason dan zamu iya samun gagarumin matsala dake.” ya qarasa maganar yana had’e fuska “numfashi ta sauke sannan tace “okay shikenan naji kayi hakuri “.ta fada tare da kamo hannunsa cikin nata a natse bai ce daita qala ba ta cigaba da magana “kayi magana mana kayi shiru kana kallon wani gefe dabam huci ya furzar yana Kai hannunsa goshinsa “na fa baka hakuri duk da ni nasan ba wai laifi nayi ba.”

“Saboda me to zaki bada hakuri tunda kinsan bakiyi laifi ba?”ya fad’a a fusace yana qoqarin zare hannunsa cikin nata tayi saurin rikewa tana shagwabe masa “yanzu akan maryama zaka canza min “.ba akanta bane akan kalmar hauka ne banason kina kiranta da kalmar hauka domin ke kanki kinsan babu alamar haka a attare daita “naji kayi hakuri bazan sake ba shiru yayi mata yaki cewa komai “haba mana my heart ka saki ranka mana wallahi idan kana nuna min haka sai naji kamar kana sonta ne “ta qarasa mgnr tana kwanto masa ajiki numfashi ya sauke tare da cewa “shikenan naji naji !! ta dan dago daga jiknsa tana kallonsa “to kayi min murmushi .”
murmushin takaici yayi itama dai murmushin tayi kana ta cigaba da magana “ga dukkanin alamu company ata sun nuna zan samu aiki da company dan nasan tunda suka d’aukeni dole zaa sake nemana still dai shiru sadam yayi sannan yayi kicin kicin da fuskarsa “my heart!”ta kirasa bai amsa mata ba amma hakan bai sa ta damu ba ta cigaba da maganarta “da zarar na samu aiki kudi zasu samu kenan ,da zarar mun samu kudi zamu bar wannan wajen ko ba haka ba ?”shiru dai yayi mata .”

ta numfasa tare da gyara zamanta “what’s our next plan my heart ?”stil dai shiru yayi dan shi baya jin zai wani barta tayi aiki da wannan kamafanin “my heart kamin magana mana ?”tai maganar tana kai hannunta sansar jikinsa “ba batun samun kudi bane damuwatq dan banason Kiyi aiki a wannan kamfanin ,domin ina son muyi nisa da nan ne mu qara gaba muje inda babu wanda zai ganmu ko wanda ya sanmu far away from everyone “.and far away from maryama ba ..”ta fad’a tana tsarke yatsun hannunsu tare da rungumesa ajikinta” amman kuma duk wannan abun daka lissafa suna bukatar kudi “karki damu zamu samu kudi qasar ma zamu bari gbdy dan haka kar na sake jin batun zakiyi aiki da wannan kamfanin matsawar kina son ki cigaba da ganina a tare dake ko kuma yuwar aurenmu dan kina sake tada maganar aiki da wannan kamfani wallahi na fasa aurenki .”sake rungumeshi tayi tsam ajikinta tana shakar qamshin jikinsa.”shikenan naji duk abinda kace shi zanyi.”

*****

Qarfe takwas da wasu ‘yan mintuna motar mr ata ta qaraso titin capitor sakamakon hoodop din da suka iske akan hanyarsu ahankali suka shigo unguwarsu maryama ,direba ya samu waje a gefen titi yayi parking ya fito daga cikin motar ya rufe murfin mota yayi gaba kad’an abunsa inda mr ata ya maida kwayar idanunshi kan maryama still yana rike da yatsunta hannunta muryarsa a kasalance ya kira sunanta “maryama .”!
bata amsa ba sai dai ta waigo inda yake zaune tana kallonsa tana kallon yadda yake ciza lips dinsa ,gefe guda kuma tana jin sauyi a sansar jikinta sakamakon hannunta dake cikin nashi sosai ya sanya kwayar idanunshi cikin nata duk da babu wani wadataccen haske acikin motar amman tana jin kwayar idanunshi ajikinta ta Lumshe idanunta hasken wayarsa ya kunna ya haska fuskarta ya tsurawa fusakr ido yaga yadda idanunta suka kumbura sukai wani irin girma fuskarta tayi jajir .”cikin wani irin yanayi yake kureta da kallonshi kafin yaja ajiyar zuciya ya sauke sosai ya kwantar da muryarsa“ya kike jin zuciyarki yanzu ?”kina jin damuwa har yanzu ?yayi mata tambayar ajere sai data had’iye wani abu daya tsaya mata a makoshi kana ta soma magana a natse “ban ta’ba tunani cewar cikin lokacin kankani irin wannan zai sa naji damuwata ta wattanni sun gushe ba ,ta qarasa magana muryarta da alamun son yin kuka “wallahi naji relief sosai amman hakan bazai sa na iya mantawa da d’anuwana ba “ta qarasa maganar tana runtse idanunta “maryama wannan duk mai sauki ne akan ki cigaba da rainon soyayyar matace acikin zuciyarki ,sannan rage damuwar zai sa ki cigaba da rayuwarki cikin salama kamar kowa ,forget your past and leave your present “ko kin fahimci abinda nake nufi.”

“naji zanyi duk abinda kace kuma naji dadin gudumuwar daka bani dan ka taimakeni kuma naji dadi sosai “maryama kin yarda sosai da wannan mutumin kuma ina ji a zuciyata har yanzu akwai wani space da kika bashi acikin zuciyarki “wannan haka ne ban ta’ba jin na yarda da wani halitta kamar yaya sadam ba amman ta yaya kasan har yanzu sadam yana da sauran space acikin zucyta?”shiru yayi kawai yana kallonta yana jin wani iri acikin ranshi “sir !”mai yasa kayi shiru kana kallona ?still dai shiru ya cigaba dayi yana cigaba da kallonta zuciyarsa cike da zallar kishi “sir me kake tunani ?bai ce mata komai ba illa ya runtse idanushi “amman nace sir yaakayi kasan cewar idan nayi kuka irin na yau zanji relief ?”ya sake damke yatsunta da karfi tare da sake runtse idanunshi gam “sir ko kai ma ka ta’ba tsintar kanka cikin irin yanayin dana tsinci kaina ne ?”shiru yayi kawai yana tunanin irin rayuwar wahalar da yayi akanta wacce bazai ta’ba mantawa ba “bazai iya kirga sau adadi nawa ya sha giya akan zafin rashinta ba sigari kam ma baa maganarta bare kuma zubar hawayensa “.

“sir !sir !! ta sake kira sunansa ahankali har sau biyu ajere sakamakon ganin moond dinsa ya canza “sir me kake tunani ne ko maganata ta ’bata maka rai ne ?”no !”ya fad’a atakaice bata bata min rai ba amman abinda nake baqata dake ki goge wannan soyayyar dake binne a zuciyarki domin bawa wata soyayyar dama shiga rayuwarki yana gama fad’ar haka yace muje ko “.ta kasa fita daga cikin motar ta tsura masa idanunta tana tunanin abinda ya bata masa rai ganin ta kasa tuno wace kalma ce tai sanadiyyar canza masa mood dinsa taga gara kawai ta bashi hakuri sosai tayi kasa da muryarta “kayi hakuri .”!
“ba hakurinki nake bukata ba ki goge wannan banzar soyayyar shine abinda nafi buqata “naji zanyi qoqarin yin abinda ka buqata duk da hakan ba abu ne mai sauki agareni ba bayan halaccin ya sadam agareni umma ma abar dubawa ce taso ni ada baya can kuma har a yanzu tana qauna ,ta bani dukkanin wani gata da kulawa tun ina qarama har zuwa girmana ,bata son damuwata yanzu haka tana can zaman jirana bata bacci matsawar bata ga shigowata ba tana girmamani kuma tana tsananin sona zatai iya yin komai akaina “the most special thing in this world to me is my special mumy wato umma wannan yana daga cikin dalilin da yasa cire ya sadam araina zai yi matukar wahala agareni dan umma bazata iya ciresa a rayuwarta ba amman zanyi qoqarin ragewa da fatan bazaka damu da jin haka ba ?”ta qarasa maganar tana kallon yatsun hannunsu dake tsake cikin juna.”
Chapter 79 · 0% Book details