← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 111

Sashe 67

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Khadija ki daina cewa haka ya d’aukeku abakin komai mana adamcy fa yana matukar qaunarku duk sanda kuka ga yayi maku haka kuyi masa uzuri ni wacece a wajensa ?”ta tambayesu tana dubansu “nifa na kawosa duniya amman a duk sanda halinsa ya motsa nima yi min yake yanzu ku duba bayan gaisuwa mai ya had’ani dashi ?”amman kuma ya zan masa baa canzawa mutun d’abiarsa da nayi dan haka duk kuyi hakuri idan da sabo mun rigada mun saba da halinsa fatan mu Allah ya canza mana shi inji cewar mami "nima shine abinda na gani tunda halinsa ne mai zai sa mu damu kanmu ni dai idan ba tautaunawarmu yaji ba ai da sauki zabiba ta fad’a tana kallonsu shiru sukayi babu wacce ta sake cewa uffan "maryam kam tunda ta d’aura goshinta akan hannu kujera bata sake d’agowa ba hatta maganar da suke akan ata ta daina fahimtar komai sai hawaye ne ke fito daga cikin kwarnin idanunta suna bin gefen idonta har sanda aunty shahida tai mata magana “maryam tashi mu wuce gida lokaci na tafiya da kyar maryam ta yunkura ta mike tsaye mami da sauran jama’ar dake wajen sukai ta mata sannu “to mami mu zamu wuce gida sai an kwana biyu kuma “to shikenan allah ya tsare haka ma aunty khadija da zabiba sukai mike tare da yiwa mami sallama suka kama gabansu gidan ya saura daga mami sai auta.”

********

Mr ata yana shiga bangarensa takalman qafafunsa kawai ya cire da safa ya fad’a bathroom yayi alwal ya fito ya gabatar da sallahr magarib da isha’i bayan ya idar ya d’aga hannuwansa sama ya soma addua yana mai kaskantar da kanshi a wajen Allah ,allahumma as aluka bi anna lakal hamda laila ailla anta wahdaka lasharika laka ,al mannan ya badi’us-samawati wal ardi, ya hayyu ya qayyum ya zal jalalu wal ikram inni as alukal janna wa auzubika minan nar, Allahu
al wahid ,al ahad ,Allahu assamad, wa ilahukum ilahun wahid ,laila a illahuwar rahmanur rahim “. a qarshe ya fad’i bukatarsa a wajen Allah wadan nan sunayen sune sirrin sunayen allah matukar mutun ya iya fadanci da wadan nan sunayen babu abinda zaka roki allah dasu bai baka ba in dai alkhairi ne . dan a yanzu ya gane yayi sakaci sosai arayuwarsa ta baya shiyasa yayita samun matsala .”bayan ya gama adduar ya mike tsaye ya cire kayan jikinsa ya shiga wanka ya dan jima ya fito ya goge jikinsa sannan yabi jikinsa da turaraku masu sanyi kamshi sannan ya sanya vest da boxer ya zauna a tsakiyar katifarsa ahankali ya janyo system dinsa da hannu d’aya ya kunna kai tsaye inda na’urorin sadarwar camerorin saman office dinsa suke ya shiga yayi rewarning ya soma duba abinda ya faru a tsakanin nadia da maryama ba komai yasa yayi haka ba sai dan yana son ya gano wani abu .”

Ahankali ya natsu tare da tsurawa screen din laptop din ido ,abinda ya d’aga masa hankali shine mutumin nan mai spray control daya gani tare da nadiya tsaye suna musayar magana har a qarshe ya mika mata wayarta ya fita da sauri ita kuma jin motsinsa yasa ta buya a qarqashin kujera “waye shi din ?”ya tambayi kanshi “yana sake zoomin din fuskarsa mutumin duk yadda yaso yaga fuskarsa ya kasa sakamakon babu inda ya bari a bude dan gabad’aya ilahirin jikinsa a rufe suke haka fuskarsa hatta kwayar idanunshi wani katon glass ne d’an tsiririn hancinsa ne a waje shima bai gama bayyana ba amman dai yasan babu wanda zai kawo masa wannan mutumin sai nadiya lallai shima yana son yasan ko waye shi .kwakwaluwarsa na cikin wannan tunanin mami ta turo kofar bedroom dinsa ta shigo kai tsaye zama tayi a gefensa tare da tsura masa ido “barka da dare sweetheart “barkanmu adamcy ya kake fatan kana lafiya?”lafiya sweetheart"!ya fad’a yana sauke numfashi tare da kashe laptop din gabansa ya rufe ya tsura mata tsumammun idanunshi, sai da mami ta gama nazarinsa tsab sannan tace “mai yasa kake yiwa yan’uwanka haka bayan kasan duk duniya baka da kamarsu suma haka .”

“Mai sukace nayi masu sweetheart ?”basu ce ba amman kai a ganinka abinda kayi masu daka shigo daidai ne ?”kallon arziki baka masu bare ka gaishesu kannenka kuma sun gaisheka suna ka wulakantan su .numfashi ya sauke yana shafa sumar kanshi “mami shigowa nayi naji suna zagina “.zagi kuma adamcy ?”ya d’age mata girarsa daya “alamun “eh !”taya zasu zageka adamcy ?”sweetheart ki tambayesu idan ma zagina zasuyi sai su zauna sunayi dani a gaban wannan yarinyar haba sweet heart “mami ta girgiza kai tana cewa “adamcy rigimar duniya ni dai wannan qiyayya taka da maryam allah ya kusan kawo min qarahenta ,aranshi yace “in sha allahu allah bazai kawo qarshensa ba .ta kamo hannunsa cikin nashi kana ta cigaba da magana “yaushe zaka kawo min yarinyar maryama ?”ya kalli mami yana nazarin maganarta kafin ahankali ya motsa lip’s dinsa yace “maryama kuma ?”ta lumshe masa ido ina son ganinta ka kawo min ita “okay !”ya fad’a atakaice “when zaka kawo min ita “sweetheart may be zuwa next week Insha Allah"Toh Allah ya kaimu next week din sannan sai abu na gaba “ka dinga hakuri da komai adamcy yanzu girma kake yi gashi zaka zama uba "Allah yayi wa rayuwa albarka
"Ameen" ya amsa mata yana tsuke fuska baya son tana masa batun cikin yarinyar, mami ta mike tare da shafa sumar kanshi “akawo maka coffe ko tea ?”kowanne ya samu sweetheart “abinci fa ?”dan qaramin tsaki yaja kana ya girgiza mata kai alamun baya bukata , ta fice tana fita ya dawo parlour’n tare da danna wayar yaronsa ahmed ya kira ya kai sau uku bai dauka ba .”ahankali cike da natsuwa mr ata ya ajiye wayar ya kwanta flat akan kujera tare da rungume hannuwansa ya soma tunani maryama .”

Dare yayi dare amman maryam ta kasa runtsawa juyi kawai take akan gado a qarshe dai ta yunkura ta tashi ta zauan tare da ruqunqume hannuwanta duka a qirji tana tunani ,sosai tayi zurfi cikin tunani mai zai faru idan har yarinyar ta tabbata gaskiya ne ?”maryam !" taji sautin muryar aunty shahida ta kiran sunanta,da sauri maryam ta maida hankalita zuwa bakin kofar shigowa tana amsawa da raunanniyar murya "meke damunki?”tayi shiru kawai zuciyarta na wani irin harbawa da sauri, aunty shahida tayi taku zuwa inda take zaune ta zauan a gefenta tare da dafata tace fad’a min damuwarki maryam “Allah aunty shahida na kasa bacci labarin d’azu da sister ta gaya mana ya hana zuciyata sukuni daren yayi min tsawo sai nake ganin kamar gari bazai wayewa ba ,zuciyata zafi take haka kwakwaluwata ,na rasa natsuwar komai aunty “kada ki damu kanki da maganar yarinyar nan kinji,sannna ki rabu da adamcy zamuyi miki maganinsa da izinin allah yadda ya dasawa zuciyarki ciwo ya hanaki sukuni da kwanciyar hankali muma zamu dasawa zuciyarsa ciwo domin kuwa ciwon 'ya mace na 'ya maca ne, kina wannan halin na yau lafiya gobe babu amman ya hana zuciyarki hutawa wanda a daidai wannan gabar zaki iya rasa rayuwarki .”

Maryam numsafa kawai tana jin wani irin zafi a zuciyarta tare da kai idanunta sama tana kallon dakin d’akin tana sake zurfafa tunaninta “ki daina tunanin maryama ki jajurce da addua domin baki da mataimaki sai Allah “ina addau aunty addua nake amman kullum alamarin sake tsamari yake ni har nagaji da addaur aunty , na rasa me zanyi zuciyata kullum muradinsa take ni bama kaina nake ji ba a halin yanzu abinda ke cikina nake tunanin halin da zata shiga idan tazo duniya “ ta qarasa maganar hawaye na gangaro mata akan kuncinta .”wannan kuma ki qyaleshi ko yaki ko yaso abinda yake cikinki nashi ne kuma jininsa ne idan ya ga dama karya amsa mu dai mun amsa kuma muna so .”sannan duk fushi da zai yi na banza ne zai ma sauko ne ni nasan bazai iya cigaba da fushi da abinda ke cikinki ba sai dai idan bata zo duniya ba " maganar aunty tayi mata dadi ke dai ki dage da addua allah yace zai amsawa bayinsa matukar bai kosa ba ki daina cewa adduar kike kinji shiru baa cewa allah anji shiru maryam ki cigaba da yin addua,allah yana jinki kuma yana ganinki kuma zai amsa miki saboda kina da yakinin allah ya ganmu yasan mu kuma yana jinmu ,bawa zai dade yana addua amman yaji shiru har ma yaji tamkar allah bai amsa ba Aa wani lokacin abun ba alkhairi bane wani lokacin kuma Allah yana jaraba bawansa ne .”maryam tayi qasa da kanta tana amsawa da to aunty na gode in sha allahu zan sake jajurcewa ta fad’a haka a fili sai dai abani zuciyarta ta kasa samun nutsuwa .”

Washegarin da misalin qarfe 11 :00 daidai kira ya shigo wayar oga amar alokacin yana zaune a office dinsa ya janyo wayar tare da dubawa ganin wanda ya kiransa ne yasa ya d’aga da hanzari “hello !”daga can bangaren mr ata yace “amar idan kana da time kazo zuwa anjima muje gurin kanin mahaifin maryama shiru oga amar yayi kafin daga baya yace “yanzu kana ganin wannan tsarin da zaka bi daidai ne ?”ko daidai ne ko ba daidai bane ni dai kazo muje kawai “amman jiya jiya nan kace next week ?”na canza shawara .”ya fad’a yana cizan lip’s dinsa na kasa “to shikenna zan zo zuwa anjima yana gama jin abinda ya fad’a ya katse kiran ya cigaba da juyi akan kujera qarfe daya da rabi oga amar ya shigo AGC sai dai bai hau sama ba ya kira mr ata cewar yazo amman zai shiga massalaci yayi sallah “okay nima yanzu nake shirin saukowa .”daga masallaci suka wuce unguwarsu maryama shi da oga amar bayan sun kira baba gali cewar suna son ganinsa suna tafe suna tautaunawa har suka qaraso gidan su maryama lokacin da suka qaraso har baba gali ya gama shinfida ,a bangaren da suke sauke tarbon baki .”
Chapter 67 · 0% Book details