← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 111

Sashe 49

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

mr ATA bai  kalli inda sultana take tsaye tana kallonsu da mamaki ba ya bawa maryam umarnin kije ki cire kayan  "good morning sir “! amman me Ke faruwa haka ?ya lumshe mata tsumammun idsnunshi yana sauke numfashi sai maryama ce tayi mata bayani dan shi bashi da lokacinta "you could have called me ya Adam I can do more than this for you ,ita nayi raayi ta min any problem?amman me yasa sai ita bayan gani dana kasance jininka ?ya ma akayi kuka kasance tare adaidai wannan lokacin ko tare kuka zo ne? gaban maryama ta rikice ta dinga jin wani irin mummunar fad'uwa gaba yayinda jikinta ya dauki rawa ta kasa motsi bare taje ta cire kayan jikinta shi kuwa wani irin mugun kallo yayi ma sultana sannan ya wuceta zuwa mazauninsa batare daya ce mata komai ba dan bata isa ba.”

da sauri maryama ta shiga ta cire kayan ta fito zuwa office dinsa wanda zuwa lokacin mutane sun fara zuwa "good morning!!!ta furta tana zama sannan ta kallesu daya byn daya mr ATA fa ya amince da new desings din mu "me Kike qoqarin kice ya amince maryama cewar surayya maryama ta gyada masu kyau tana lumshe idanunta suna cikin haka sectray ta shigo "maryama !yes ma !gabadaya desings dinku sun kammala dan zaa fara shirin aiki akansa ?eh !ni dai nawa ya kammala har na shiga sabon aiki na sauran ne dai sauran kadan su qarasa madam some ta juya maryama tace “excuse me ma!” ta tsaya dan Allah idan zaa dinka kayan ayi kamar yadda na zana "okay ta fad'a tare da juyawa ta fita gabadaya kowa ya fuskanci aikinsa ."

******

Suna zaune mr ata ya shigo yana magana da some yayinda gabadayansu suna tsaye cike da girmamawa yana cikin magana wayar sultana ta dauki qara ya juyo ahankali yana mata kallon banza irin kallon da yake mata yasa taji jikinta ya dauki rawa qoqarin kashe wayar ta fara dan a dokarsa baa kiran mutun idan yana magana sannan mutun bai isa ya amsa kira ba ,ta dan saci kallonsa kamar yadda maryama tayi ,sultana ta aikata laifin amman gabadayansu zuciyarsu rawa take kallo daya zaka masu ka fahimci haka muryarta a hankali tace  sorry sir "lumshe lumtsatsun idanunshi yayi ya cigaba da magana zamuyi qoqarin mu gabatar da new desings din nan in sha allahu idan kunci saa zaa da.. .."wani kiran ya sake shigowa ya katse masa mgn wannan karon qarara ake iya hango bacin ransa yaji kamar ya kifa mata mari ita kuwa idanunta ta kai ga kallon screen din wayar sunan Aunty abida tagani yana yawo numfashi ta sauke "ko me zan mata adaidai wannan lokacin "me Ke damun tunaninki ne sultana “?me zai hana kisa wayar a silet me yasa bakya yin abinda dan Adam yake ?”kalli maryama kwararriya ce a gurin iya zane amman kin ta'ba ganin wayarta na qara . koda yaushe wayarta na silet nan take maryama ta sha jinin jikinta ta fara zazzare idanuwa” to be your last warning nonsense girl kawai da batasan komai ba sai zallar shirme “yana gama fadar haka Ya juya ya koma office dinsa yana fita maryama ta dubi surayya da sauran matan tace “kuyi ku qarasa aikinku kafin ya sake shigowa ."

Sultana na fita ta kira Aunty abida tana dauka ta hau magana cikin zafin rai  "me yasa kika daukar wayata ? taya zan dauka ina tare da ya Adam sister idan kinga abinda yayi min a gaban abokan aikina sai kin tausaya min” what akan me kenan “?nan ta shiga koro mata duk abinda ake ciki da new desings din da'a zaa gabatar batare da sanin kamfani ba na fad’awa sultan amman ban san me ye shirinsa ba dan har yanzu bai zo office ba bare naji yadda sukai da baba qarami .kice wannan yarinyar ta samu dama haka lallai akwai sabon aiki agabanmu shiyasa banason ayi aikin ba kuma wai dan banason cigaba yaya adam bane idan akayi nasara maryama ce nasara saboda ita ta kawo tsarin kinga dole zai Bata mahimanci arayuwarsa .”

“naji bari na kira Ibarahim naji ko yasan abinda Ke tafiya suna gama wayar ta kira yaya Ibrahim byn ya dauka tace "ka natsu da kyau akwai abinda zan fad'a maka very important sultana ta fad'a min tun last week a office anyi shirin gabatar da new desings batare da sanin kamfani ba” what”! ya furta da karfi yana mikewa tsaye cike da bacin rai me kike qoqarin fad'a min?” abinda muke gabatarwa duk qarshen wata me yasa zai shirya haka byn shine ya karfafa wannan dokar” wannan ba shirinsa bane shirin wannan tsinanniyar sabuwar maaikaciyar ce maryam ne sunanta ko maryama shiyasa nace nayi sauri na fad'a maka kayi duk yadda zakayi hakan bai tabbata ba ai wannan maganar dole sai baba yaji amman bari na bincika na gano gaskiya mgn yay discounting din kira.”

Mmn Sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 23

mr ata kam tunda ya gama yiwa ma'aikatansa bayani tsabgar gabansa kawai yake ya manta da yayiwa wata sultana rashin mutunci yana zaune akan kujera yana amsa waya da d’aya daga cikin wayoyinsa kiran yaya Ibrahim ya shigo ya d'auki wayar ya duba ganin sunansa ne, yayi shiru ya cigaba da magana cikin nishadi kamar zai d'aga ko tunanin me yayi sai ya share ya cigaba da wayarsa dan haka nan jikinsa ya bashi waya ce akan aikinsu shi kuma ko me zai faru sai dai ya faru amman sai ya cima burinsa yana son yaga me zai biyo baya idan yayi ."bangaren yaya Ibrahim kuwa layin mr ata yake nema sai dai kiran na shiga ba'a d'agawa ya kira layin ya kusan sau biyar amman the same thing ne.
ya shiga zagaya office dinsa tsabar tashin hankali kafin ahankali ya koma kiran layin sultan kira d'aya sultan ya d'aga."

Sultan yana d'agawa bai tsaya sun gaisa ba ya soma da tambayarsa halin da'ake ciki ,bangaren sultan yace "tabbas labarin daka ji haka ne sai dai baba ya takawa abun burki babu abinda zai yi "ka tabbatar sultan dan yanzu ina kiran layinsa yaki d'agawa ?"to ai ka rigada kasan halin wannan banzan mai banzar rayuwar ba lallai ya d'aga kiranka ba tunda an hanashi cima burinsa yana can yana bakinciki da bakin rai ,sannan mami ta tabbatarwa baba bazai yi ba ,bayan haka ma tace zai bar mana kamfani gabad'aya ,kaga ai mu gaba ta kai mu, ita kuma wannan yarinyar mai rawar kan zan san abinda zanyi akanta, duk yadda zanyi na rabata dashi dama aikin a qarqashinsa zanyi,dakata! dakata!! sultan ni fa ba batun wannan yarinyar bane agabana ,muyi magana mai bullewa kasani nasani kai kowa ma acikinmu ya san kasancewar ata acikin AGC yana da matukar amfani bazan so ata ya bar kamfani nan ba domin kasancewar sa tare damu akwai alkhairi .”

"wani alkhairi ne akwai ?"sultan ya fad'a haka a zafafe ta hanyar dakatar da yaya Ibrahim dan arayuwarsa yana bakinciki ace mr ata yana da wani qualities ko mahimanci,sai daya ja numfashi ya sauke sannan ya cigaba da mgn "mutumin da yayi mana handama da babakere,mutumin da yake qoqarin yaga bayanmu,mutumin da babu komai aransa sai zallar zalinci da .."dakata sultan ban kiraka dan kayita aibuntashi ba,tunda naji kan magana sai anjima yana gama fad'ar hk ya katse kiran yana sauke numfashi sannan ya soma magana a fili “bansan har sai zuwa yaushe sultan zaka dainawa ata bakinciki ba ,”kasa ganewa kayi amman ata ba sa’anka bane ,ba sa’an karawarka bane ya fad’a yana cigaba da lamuran gabansa da zumar idan ya koma gida zai nemi ata suyi magana ta fahimta dan shi bai yarda da tsarin barinsa kamfani ba "qarfe shida daidai yaya Ibrahim ya dawo gida wanda har lokacin mr ata bai dawo ba yana can zaune a office ."

Ahankali mr ata ya mike daga mazauninsa yana duba lokaci karfe shida da wasu mintuna ya kai kwayar idanunshi saitin office dinsu maryama yaga kowa dai bai gan ita da yusura ba,sauran ma’aikatan ma dake office din shirin tafiya gida suke dan haka yayi tunanin suma sun wuce gida.ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa ya soma shirin wucewa gida ya tattara duk abubuwansa masu amfani kira madam some ya mika mata ta fito ta nufi qasa sannan shima ya fito yana taku cikin isa da jin kai yayinda .”
tun daga nesa ya hangosu tsaye ajikin motar sultan tare da yusura wacce ke tsaye ajikin kofar baya da alamun jiran maryama take yayinda maryama ke tsaye a kusa da sultan rike da yatsun hannunta tana wasa dasu suna magana .nan take qirjinsa yayi wani irin bugawa da karfin gaske har sai da yayi qasa da tsumammun idanunshi ya kalli daidai saitin zuciyarsa sakamakon bugawar daya ji take dum dum!! .”
Chapter 49 · 0% Book details