← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 111

Sashe 1

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 1

Wani irin abu ya dinga jin yana bin jijiyoyin jikinsa ,zuciyarsa kuwa banda bugawa da matsanancin karfin babu abinda take tmkr zata fasa qirjinsa ta fito waje haka ya dinga ji ,"tabbas wannan fuskar fuskar yarinyar mafarkinsa ce tsaye a gabansa ."suna cikin wannan halin some ta turo kofar office din ta shigo cikin tsananin tashin hankali, muryarta na rawa ta soma magana cike da tsoro "me yasa kike da matsala? "maryama hussein mai ya shigo dake cikin  office din nan bayan na fad'a miki mai gida baya da bukatar ganinki?"  "sir please kayi hakuri ban san lokacin data shigo ba "ya d'ago idanunshi wad'an da suka rikid'e zuwa ja ya saukesu akan some dake rawar murya da jiki "kayi hakuri sir yarinyar ce tana da taurin kai na fad'a mata baka da bukatar ganinta am very sorry sir." "malama ki gyara kalamanki dan suna sani jin wani iri acikin kwakwaluwata ,na shigo ko aka shigo dani ?" Idanunshi dake kan some ya dauke ya maidasu kan maryama  caraf sukayi 4 eyes da ata ido cikin ido suke kallon juna wani irin zirrrr ya soma ji a gbdy sansar jikinsa ,wani irin kallo mai tafiyar da ruhi ya dinga mata , a zuciyarta tace" ko me yasa yake min irin wannan kallon kamar zai cinyeni ?saurin cire kwayar idanunta cikin nashi sakamakon bugawar da zuciyarta ta fara yi ."

Sosai ya sakankace a kallonta har sai da some ta soma zargin wani abu akan mai gidan nata dan bata ta'ba ganin macen da yayiwa irin kallon da yake mata ba hasalima shi mutun ne da bai fiyye son kallon mata ba , ta juya ta kalli salim dake tsaye shima ata yake kallo fuskarsa d'auke da tarin damuwa,sautin muryarta ce ta dawo dasu natsuwarsu ," kisani ko nace kusani gabd'aynku maryama tafi karfin wulakanci sannan tafi karfin tayi aiki akarkashin mutane irinku marasa mutunci da tausayi ."gaban ATA yayi wani irin  mummunar fad'uwar da bai ta'ba jin irinsa ba sai a yau din nan ."yay mugun  tsura mata kwayar idanunshi yana kallonta nan take yaji maganarta tayi balain d'aga masa hankali 'yayi taku biyu zuwa inda take tsaye jikinta na kyarma sai dai ya kasa cewa komai dan koma yace zai yi magana a halin da yake ciki bakinsa bazai iya furta komai ba "an fi karfina ne yasa kuka sake ganin qafafuwana acikin kamfaniku dan wlh a karon kaina bazan ta'ba turo maku sakon neman aiki ba tunda nasan halinku bare har na tako domin yin aiki ".tana gama fad'ar haka kan ATA yayi wani irin  tsarawa tare da sauke wani zazzafan numfashi ya kai tattausan tafin hannunsa daidai saitin zuciyarsa da  ke mugun bugawa da sauri sauri dan tun data soma magana qirjinsa yake bugawa fiyye da kaida "kisani ko nace  kusani  maryama tafi karfin wulakanci sannan tafi karfin tayi aiki akarkashin mutane irinku marasa mutunci da tausayi shine maganar da yake ta yiwa ata yawo acikin kwakwaluwarsa ."

maryama ta sauke idanunta da suke a rine tsabar tashin hankalin da take ciki akan ATA dake tsaye wanda ya tsareta da tsumammun idanunshi masu firgitarwa hakan yasa ta kawar da fuskarta gefe sannan ta fara fad'ar abinda take son fad'a "karo na  biyu kenan kana ci min mutunci laifin me nayi maka ?" ta tambayesa tare da d'ago fuskarta ta zuba masa tana mai danne kwalla dake qoqarin zubo mata "baka son ganina arayuwarka ko  "?ta fad'a tana sheshekar kuka " wallahi ban san me yasa na yarda na kawo kaina inda zaa tozartani ba ."subhallah !ata ya furta a kasan ransa yana jin kamar ya qara taku biyu din da yayi saura a tsakaninsu ya fixgota yayi mata kyakkyawan riko tare da mata masauki a faffad'an qirjinsa "what the hell is going on?me yasa kike fad'awa mai gida haka instead ki bada hakuri ko zai taimaka ya d'aukeki aiki sannan ki gyara kuskurenki shine zaki zauna kina fad'awa mutane magana I can't tolerate that "saboda me zan bada hakuri ?"laifin me nayi da zan bada hakuri ?Ko kuma kuskuren me zan gyara idan kina wasa ne to ki daina dan babu hakurin da zan bayar dan kawai nayi aiki daku  "cike da tashin hankali ata ya fixgar da   numfashi sannan ya motsa labbansa  a hankali ya soma magana "some !"

jikin some  na kyamar ta amsa da "yes sir! leave.."!
"Okay sir am sorry  !ta juya da sauri ta nufi kofar fita hakan da maryama taji yasa ta biyo ta bayansa  ta  ra'ba ta gefensa zata fita har tana zozon jikinsa wani abu yaji mai kama da wutar lantarji ya ziyarci gabad'aya ilahirin jikinsa  ,fuskarsa dake a murtuke ya tsaida akanta yayinda da sauri salim ya biyota ya  sha gabanta yana cewa "dan Allah maryama ki tsaya ki natsu ki kwantar da hankali duk abinda kike bukata acikin kamfanin nan a shirye muke zaa miki shi amman ki dan bamu  dama zamuyi magana mai mahimanci dake ."nan da nan 'bacin ran maryama ya sake nunnukuwa zuciyarta ta dinga tafarfasa bata ce masa komai ba sai dai ta balain had'e fuskarta sannan a  natse  ta ra'ba gefensa ya sake shan gabanta "a gaskiya raina ya fara 'baci da abinda kake min sannan zuciyata ta fara tafarfasa ,ni mace ce mai tsnanin hakuri  karka bari nayi maka abinda ban ta'ba yi wa wani mahaluki a duniyar nan ba ".
"me zaka fad'a min ko kuma nace me zaku me bayan wulakanci da tozarcin da kuka min ?nasani shima ATA daya aikata haka bai san ko ke.."enough please bana son jin komai matsa kawai ka bani hanya na wuce bana bukatar taimakonku."ta fad'a tana mai sake ra'bawa gefensa ya sake shan gabanta ai kuwa zuciya ta rufeta bata san sanda ta d'aga hannunta ba ji kake tas ..! ta sauke masa wani lafiyayyen mari   akan Kuncinsa a gigice ya dafe kuncinsa yana kallonta cike da tsananin tashin hankali. ta juya a matukar fusace tana kallon ATA dake tsaye tamkar wanda aka dasashi a wajen tsabar tashin hankali "ka fad'a masa ya fita rayuwata ya bani hanya na kama gabana". yadda ta tsura masa ido tana kallonsa cikin 'bacin rai haka shima ATA kallonta yake baya ko kifta idanunshi ga wani kalar tashin hankali dake shigarsa yana bin ilahirin jinin jikinsa ."bai ta'ba jin yayi laifi yayi nadama ba sai a yau ."

"Ka fad'a masa ya bani hanya na wuce na kama gabana."tayi maganar muryarta cike da rauni a hankali ya furzar da wani iskan mai zafi daga bakinsa cikin wani irin salon magana tmkr bashi da laka  yace "salim barta ta wuce !"yana gama fad'ar haka ya juya masu baya jin haka yasa salim ya matsa gefe ya bata hanya batare da ya sake cewa komai ba ,batare da 'bata lokaci ba maryama ta gyara zaman jakarta ta fice daga office din tana jan tsaki ,jiki a sanyaye maryama take taku tamkar bata son taka qasa."tasa hannu ta goge hawayen dake tsiyaya daga cikin kwarnin idanunta ta fita daga haraban ma'aikatan inda zuciyarta ke wani irin bugawa da karfin gaske ."tana tsaye a gefen  get din ma'aikatan jiran abun hawa sai ga motar ammar kallo d'aya yayi mata ya fahimci tana cikin damuwa nan take shima yaji damuwa ta shigesa umarni tsayuwa ya bawa direbansa tun kafin ya shigar da  kan motar ciki ." direba bai gama daidaita tsayuwarsa ba amar  ya fito ya tako ya sameta har inda take tsaye tana goge hawayen dake tsiyaya "maryama !ya kira sunanta ta d'ago da sauri ta tsura masa ido "lafiya kike tsaye a bakin titi kina kuka ?yayi mata tambayar cikin tsananin damuwa "ba wannan mara mutuncin mai kamfanin ATA creation din bane .."sai hawaye sharr suka zubo mata dan haka  ta kasa cigaba da magana "zo mu shiga daga ciki Kiyi min bayani abinda ya faru ".ta girgiza masa kai "har abada oga amar qafafuwana bazasu sake shiga cikin wannan ma'aikatar ba "tana gama fadar haka ta juya ta soma tafiya tana bin gefen titi da sauri ya biyota ya sha gabanta "fad'a min wanda ya 'bata miki rai ? yayi mata tmbyr ne domin ya tabbatar da abinda yake son sani "mai kamfanin da kanshi sai wani da bansan ko waye ba sun taru sun wulakantani sun tozartani "mai kamfanin ATA creation da kanshi ?ya sake tmbyrta cike da mamaki ta gyda masa kai alamun "eh! yana kallonta ta ra'ba gefensa ta wuce ta cigaba da tafiya da kallo ya bita dashi kafin ya juya da sauri ya nufi cikin ma'aikatan."

Cike da matsanancin tashin hankali ata ya zagaya ya koma mazauninsa yana sauke wani zazzafan numafshi sai dai ya kasa zama  ya d'auki wani  file da kwayar idanunshi ya kai garesa ya soma dubawa  cikin tsananin tashin hankali yake amman dake shi din nmjin  duniya  ne bazaka ta'ba iya gane hakan attare dashi ba sai dai acikin zuciyarsa kuka yake yi irin kukan da bashi da mafuta "me yasa rayuwarsa take shiga rud'ani?"me yasa abubuwa suke faruwa dashi ne ?"wannan wani irin tashin hankali ne mai sarkakkiya?yarinyar nan itace yarinyar da kasa aka kora  a sakonni da suka gabata  "I know? ATA ya fad'a atakaice ya na mai ajiye file din hannunsa ya sake zagayowa ya tsaya cak  a tsakiyar office din ya zira hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa yana jin wani irin tashin hankali mara misaltuwa na kusanto rayuwarsa ga ciwon da kansa yake yaki dainawa sai ma cigaba da sarawa yake  ." salim ya tsaya sororo yana kallonsa  tamkar mai shirin yin kuka "kace ka sani ?"yes of course na sani amman  a yanzu  kenan bayan nasa an koreta naga kana magana hankalinka kwance yarinyar mafarkinka ce fa ?"I know! salim ya girgiza kai yana kallonsa ."
Chapter 1 · 0% Book details