← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 65

Sashe 9

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin hakan ya sa na ce su dai ci-gaba da kula da ita ba bu abin da zai gagari ubangiji. Nan na koma ƙasar London na ɗora kan karatuna na, gaba ɗaya master's ɗina da degree tare da PhD duk a chan nayi. Bayan wasu shekaru masu yawa cikin ikon Allah na zama shahararren likita wanda a kaf faɗin ƙasar africa da ƙasar turawa sun san da zama na, yayin da ake gayyata ta kasashe da ban-da ban. A shekara ta Ashirin da na ɗauka a ƙasar London ina aiki wata rana aka bugo min waya cewar Mrs Lailah ta kama wata majinyaciya ƴar prison da aka kawo asibitin. Hakan ya sani cikin tsantsar mamaki. Nan na fara shirye-shiryen dawowa Nigeria. na daɗe sosai kafin na samu visa kasancewar a lokacin an shiga lockdown a chan hakan bai bani damar dawo wa da wuri ba, Lokacin da na dawo na ganki a kasuwa na ga kammaninki suna yanayi da Mrs Lailah saidai a lokacin ban kawo komai a raina ba. Sai bayan naje gida naga an shiga ɗakin da na saka wa maƙullin sirri bayan ganin hakan ya ni shiga tantama, da naji cewar kece ki ka buɗe ɗakin nayi mamaki sosai. Jin hakan da nayi ya sa na saka Umar ɗan gidan Gov. Musa ya wanda shi ne ya riga ni dawo wa daga London domin ya tayani neman yaran Mrs Lailah.

Kallon Juna Zahra da sauran suka yi sannan suka haɗa baki wajan faɗin. "Dama kun san juna?".

Murmushi Umar ya yi ya ce. "Ƙwarai kuwa da gaske mun san juna tun a ƙasar London domin University ɗaya muka yi saidai kowa department ɗin sa da ban, na san shi ne kasancewar mun zauna a gida ɗaya da shi. Kuma mun ɗaukar wa juna alƙawarin cewa ba za mu taɓa nuna wa mun san juna ba a Nigeria sai dai idan muna ƙasar London. Dalilin hakan ne ma ya sa ku ka ga a lokacin da muka haɗu da shi da su Zahra ba mu nuna wa juna mun san juna ba".

Kallon Umar Amrah ta yi ta ce. "Kenen saboda neman yaran Mrs Lailah ya sa ku ka zo dajin mu ku ma kashe dabobbin ciki sannan ku ka sa aka harbe ni?". Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "No Amrah wannan ba ni na saka aka yi hakan ba, mahaifina ne".

Maida kallonsa Umar ya yi kan Sooraj ya ce. "Aboki ya kamata ka ɗora musu labarin fa domin ba nan ba ne ƙarshen.

Gyaran murya Sooraj ya yi ya ce. "Bayan na saka Umar ya na taimaka min. Nan Mrs Lailah ta fara samun sauƙi yayin da ta fara faɗa min dukkanin sirrukanta tun daga abin da ya faru har izuwa ƙarshe sakamakon yarda da ni da ta yi, domin tun lokacin da wannan abun ya faru da ita bata ƙara yarda da wani ɗan adam ba sai ni. Hakan ya sa na cigaba da bibiyar yara Mrs Lailah tare da hujjojin da zan kare Mrs Lailah amma duk ban samu ba. Nan ta bani wani bayani dangane da wani dukiyarta da ke cikin daji a Kano lokacin shekarun baya nan take zuwa ta ajiye dukiyarta domin yaran da zata haifa. Sannan kuma a cikin wannan dukiyar nata akwai hujjar da zai fitar da ita dangane da sharrin da aka yi mata. Hakan ya sa na ce a ina ne zan samu wannan dajin?.

Sai ta ce min iya ƴaƴan ta ne kawai ta yarda suje wannan guri domin su nemo inda dukiya da kuma hujjojin suke. Babu wani wanda zai iya zuwa kuma ya shiga inda dukiyar suke in ba yaranta ba domin hatsarin da ke cikin daji iya yaranta ne za su iya fuskantar sa. Hakan ya sa na shiga cikin mamaki naji cewa tabbas akwai lauje cikin naɗi. baya ga hakan na cigaba da bibiyar inda zan same ku. A lokacin da na haɗu da Mk a asibiti ya ce min akwai ƴar Mrs Lailah a masarautar mu ban yarda ba domin idan ma tana masarautar ta ina zan fara neman ta saboda mutanen cikin masarauta suna da matuƙar yawa ba zai yiwu na iya gane wace ce ƴar Mrs Lailah ba. Na fara tantama kan Zahra na cewa ko dai ita ce ƴar Mrs Lailah. Ban yarda ba sai lokacin da Mk ya zo lokacin da Gimbiya Talatu da Saratu suka ce Zahra ta saci gold. Ganin yadda Mk ke zayyano bayanai dangane mahaifiyar Zahra na cewar tana da mugun kuɗi hakan ya sa na fara tantama a kan cewa ko dai ita ce wacce aka ce Mrs Lailah ta riƙe hannunta ƴar prison lokacin ina London. Nan na ƙara tabbatar da cewa tabbas Zahra ita ce ƴar Mrs Lailah.

Wannan dai shi ne takaitaccen labari da na sani dangane da Mrs Lailah.

Ajiyan zuciya kowanen su ya sauke!. Sannan Aliyu ya ce. "Kenen tana tare da kai tsawon waɗan nan shekaru?, ashe tana raye, Allah sarki nayi matuƙar kewarta, na san idan Grandpa ya sani cewa tana raye zai yi farin ciki kuma idan ya san ba ta aikata laifukan da aka tuhume ta da shi ba zai nemi gafarar ta cikin dana sani. Sannan ahalin gaba ɗaya za su haɗu su koma yadda suke cikin farin ciki kamar yadda yake a da".

Kallon Sooraj Amrah ta yi ta ce. "Ta ya ya za mu san inda dajin yake muje mu ɗauko dukiyar mu da kuma hujjojin?". Kallon Amrah Sooraj ya yi ya ce. "Ta bani wani maƙulli da kuma wani ƙaramin littafi ta ce a cikin dajin ne za'a dinga buɗe littafin sannan kuma shi littafin ne zai dinga nuna muku direction ɗin inda za ku dinga nufa har ya kai ku ga inda dukiyar suke, sannan a bangon littafin kamar akwai photon dajin a jiki bara naje gida na ɗauko su".

Ya faɗa yana mai shiga cikin motar sa da Mk ya tawo da shi sannan ya nufi hanyar gida. Saida ya kwashe fiye da mintuna talatin kafin ya isa gida.

Ɓangaren Gov. Musa kuwa bayan an kamashi aka nufi cell da shi yayin da aka fara bincike a kan case ɗin ɗansa da ya yi ƙoƙarin sace wa tare da matan da yake safaransu izuwa kasashen waje.

_______
"Wai ni kam har yanzu ba'a ji bayanan inda Aliyu da Safira suke ba". Mom ta faɗa hawaye na sauka bisa ƙuncinta.

"Ki kwantar da hankalinki Zainab, in sha Allahu babu abin da zai same su, ba kuka ne ya kama ce ki ba yanzu, addu'a ya kamata ki dinga yi domin babu abinda ya kai ƙarfin addu'a tasiri".Cewar Daddy.

Ajiyan zuciya Grandma ta sauke ta ce. "Wai a ce yara an neme su sama da ƙasa an rasa kuma a kasa samun bayanan inda suke sai kace almara, ya kamata a sanar da ƴan sanda domin ba zai yu mu cigaba da zuba musu ido ba". Kallon Daddy da Abba Grandma ta yi ta ce. "Habib da Yusuf maza kuje ku bincika inda jikokin nan nawa suke domin hankali na ya ƙi kwanciya zuciyata ya gaya min cewa wani mummunan abu na shirin faruwa da su".

Kalllonta grandpa ya yi ya ce. "Babu inda za su je, da kafafuwan da suka fita da shi, da wannan ƙafafun za su dawo cikin gidan nan, babu wanda zai fita neman su domin babu wanda suka ajiye. Idan kuma naga wani a cikin ya fita domin yaranku ne saina saɓa muku albarka. Zan gani ku kuka haife ni ko ni na haife ku". Ya ƙarashe maganar yana mai tura wheel chair ɗin da yake zaune ya bar parlour ɗin gaba ɗaya. Binsa suka yi da kallo baki sake, suna mai yin mamakin halin mahaifin na su.

________
"Yaya Usman ka na ganin abin da muka yi ya da ce kuwa?, shi ɗin fa mahaifin mu ne kuma muka miƙa shi wa ƴan sanda". Cewar Khairiya.

Tsaki Usman ya ja ya ce. "Baki da hankali wannan fa maganar justice ake ba wai injustice ba, ke baki ga yara mata da ya lalata wa rayuwa ba?, baki san hadadin rayukan ahalin da ya ɓata ba?, Su matan da ya lalata wa rayuwa aka gaya miki cewa su basu da iyaye ne?, ko kuwa an ce miki su iyayen naki basua ƙaunar ƴaƴan su?. Duk hukuncin da aka yanke masa dai-dai ne a waje na domin ni saina fi yin farin ciki ma idan na ga an yake masa hukunci, domin shi bai ji tausayin kowa ba mu ma a kan me za mu ji tausayin sa dama kuma a gidan marayu ya ɗauko mu idan kun manta ni na tuna muku".

Sauke ajiyan zuciya Ramlat da Khairiya suka yi sannan Ramlat ta ce. "Aka ne, ya yi abandoning ɗin mu da mahaifiyar mu sannan ya ci amanar mahaifiyar Yahya Umar daga baya ya zo ya ɗauke mu a gidan marayu ya kawo mu nan matsayin ƙannen yahya Umar".

____________
Kallon Zahra Dpo ya yi ya ce. "Ni zan tafi tun da na riga na ba ki littafin babu buƙatar cigaba da tsayuwa a nan, ina son ni da Mk mu tafi cigaba mu sa a dawo da case ɗin Mrs Lailah sannan a fara gabatar da shariya da kuma bayyana hujjoji na gaskiya dangane da abinda ya faru".

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Wannan shawara ce mai kyau amma ta ya ya za'a yarda cewar ita ɗin ba ta aikata abin da ake zargin ta da shi ba?".

Murmushi Mk ya sakar mata sannan ya ce. "Muna da hujja guda ɗaya mana wanda shi ma zai tsaya muku a kotu".

"Wa kenen?". Cewar Zahra. Amsa Mk ya ba ta da cewa. "Mahaifin ku shi ne wanda zai tsaya mata, domin kuwa wannan ranar kaɗai yake jira wanda zai iya zuwa da confidence ya tsaya a gaban kotu".

Bayan ya gama faɗin hakan shi da dpo suka shiga mota sannan suka bar wajan. Nan ya rage su biyar a wajan.

Sooraj Pov.
Chapter 9 · 0% Book details