Sashe 32
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shugabar cikin su ce ta ce. "Dole mu cece ta ko ta halin yaya ne domin ta kasance mai matuƙar amfani a gare mu, mahaifiyar ta mutuniyar kirki ce, bai kamata a ce ta rasa ranta ba domin tana da burin ganin mahaifiyarta. Dole mu cece ta".
Nan take suka haɗa hannaynesu guri ɗaya tare da saita hannayensu kanta. Take haske ya kauraye ɗakin, nan take hasken ya soma shiga jikin Zahra".
Daidai lokacin likitoci suka buɗe ƙofar ɗakin.
Nan take kowannensu ya zaro idanuwa waje.
LOW BATTERY. MANAGE PAGE
MU HAƊU A PAGE NA GABA🙏🙏🙏🙏
KADA KU MANTA DA LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏🙏🙏🙏🙏🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
بسم الله الرحمن الحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*BOOK 2 PAGE9️⃣2️⃣▶️9️⃣3️⃣
________________________
Babu abin da likitocin suka gani face ganin yadda gangar jikin Zahra yayi sama, ita ba'a sama ba kuma ba'a ƙasa ba.
Da sauri Sooraj ya ce. "Kada ku tayar da hankulanku, ita ɗin tana da aljanu ne bakomai ba". Kamar jira ake Sooraj ya yi magana nan suka ga gangar jikin nata ya soma koma wa ƙasa.
Da sauri Sooraj ya nufi inda take sa'anan ya soma duba yanayin numfashin ta. Da mamakin sa kuwa ya ga numfashinta ya dawo. Hamdala ya yi sannan ya ce. "Masha Allah, naga alamun yanzu ta samu bacci".
Nan ɗaya daga cikin likitan ya duba ta, ganin drip ɗin da haka saka mata ya ƙare ya sanya Sooraj ya ce a ƙara mata. Ganin har izuwa wannan lokaci ba ta buɗe idanunta ba ya sanya shi duban likitocin sannan ya ce. "Please ku kula da ita ni zan je gida na dawo".
Girgiza kai kawai likitocin suka yi yayin da daga bisani ya fice daga cikin wajan.
_____________________
"Ki yafe min Lailah, ban cika miki alƙawarin ki ba, Kasancewar mijina a lokacin baya so hakan ya sa ina ji ina gani ya saka ƴar ki cikin akwati ya kaita titi. Shima saboda zunubin abinda ya aikata yana kan hanyar dawo wa ne ya samu hatsarin mota ya mutu". Cewar nurse Nadiya
Shiru miss Lailah ta yi ta ce. "Aba nurse Nadiya kada ki bani haƙuri, domin kuwa yarinyar da na baki gata nan a gefe na".
Dubansu Safira ta yi, nan take ta kuma fashe wa da kuka. "Ashe da gaske sune yaranki da na gani a asibiti. Na gode wa Allah da ya nuna min wannan ranar".
Kallonta Aliyu ya yi ya ce. "Toh ki tashi zaune mana".
Kamar yadda Aliyu ya faɗa haka ta miƙe ta zauna. Kalllon su ta yi ta ce. "Naji an ce za'a dawo da shari'a sannan a bayyana hujjoji kuma a hukunta wanda yake da laifi".
Girgiza kai Aliyu ya yi ya ce. "Ƙwarai kuwa, dole a hukunta wanda ya yi laifi".
Kama hannun Amrah Safira ta yi ta ce. "Bara mu shiga kitchen mu dafo wani abu". Ta faɗa tare da shige wa cikin kitchen ita da Amrah.
_________________________
Babu inda John bai zaga ba amma bai ga Safira ba, gaba ɗaya ya bazama neman ta, amma bai ganta ba kasancewar sa a garin Lagos. Daga ƙarshe dai ya gano wasu information a kanta cewa tana garin Jigawa. Hakan ya sa ya je ya yi booking flight wanda zai zo garin Jigawa.
_____________________
Sooraj kuwa bai zarce ko ina ba, sai gida. Yana zuwa ya yi parking motan yayin da fadawa suka yi ta miƙa masa gaisuwa. Babu wanda ya amsa daga ciki, kai tsaye kawai cikin gida ya nufi.
Da sauri Yusrah da ke bakin window ta yi saurin nufar hanyar ɗakin su Gimbiya Saratu. Gudu take har tana tuntuɓe. Bangaje ƙofar ta yi. Da sauri su Talatu da su Samira suka ɗago tare da dubanta.
"Ke lafiya ki ka wani bankaɗo ƙofa kamar wacce haka biyo?".
Nishi Yusrah take tana mai faɗin. "Yanzun nan yahya Sooraj ya dawo".
Zumbur kowacce a cikin ta miƙe tare da kallon ta suka haɗa baki wajan faɗin. "Sooraj ya dawo!".
Girgiza kai Yusrah ta yi ta ce. "Eh, kuma ba tare da Zahra na ganshi b, shi kaɗai ne ya zo".
Jin hakan ya sa Gimbiya Saratu ta ce su je part ɗin Mami domin su san abin da ke faruwa.
Kamar yadda suka shawarta, haka suka ta fi saboda gulma na cin kowacce a cikin su, babu wacce ta hula balle hijabi.
"Sooraj kai ne ka dawo, ina Zahra take?". Cewar Mami.
Ajiyan zuciya Sooraj ya sauke!, sannan ya ce. "Mami yanzu haka Zahra tana gadon asibiti, please ina son kiyi min taimako, ki dafa mata ko tea ne, don babu abinda ta ci kuma jikinta ƙara weak yake yi".
"Aba Sooraj sai ma ka roƙe ni, kada ka damu. Bara na shiga kitchen. Yanzu ina son kaje wajen mai martaba ka nemi gafarar sa domin ranshi ya ɓaci da ka tafi baka tsaya an ɗaura maka aure da Zubaida ba, kayi masa kalamai wanda zai sa shi ya sanyaya".
Shiru Sooraj ya yi kana ya dubi Mami ya ce. "Shi ke nen, bara naje na same shi". Yana kaiwa nan ya nufi hanyar fita. Ganin Sooraj na ƙoƙarin fito wa ya sa su Saratu da ke laɓe suka yi saurin barin wajan.
Direct part ɗin mai martaba ya nufa sallama riƙe a bakin shi.
Durƙusawa ya yi kan gwiwowinsa yayin da hawaye ya ciko cikin idanunsa. tare da ƙasa da kansa ya ce . "Sarki mai sarauta, mai mulki ba tare da sandar hukunci ba, mai duba nesa da ido, mai gani a duhu kamar rana, mai yafe laifi kafin a karanto shi, sarkin da yafi ruwa tausayi, ya fi rana haske. Na zo gaban ka da gwiwa biyu a ƙasa, da zuciya mai rauni da ido mai cike da hawaye. Na san na sabawa maganarka, na taka layi, na bijire da ganganci. Amma kamar yadda ruwa ke shayar da bushashiyar ƙasa, ka yafe min kamar yadda rana ke daskare sanyi. Ka zama uba a gare ni, ba mai hukunci ba. Domin sarki mai afuwa, yafi sarki mai fushi daraja. Na roƙi gafara, na roƙi yafiya, domin domin zuciyarka tafi dutse laushi, tafi teku zurfi, ta fi sama girma. Afuwarka ita ce tazarar da ke tsakanin mutuwa da rai"
Ajiyan zuciya mai martaba ya sauke sannan ya dube shi ya ce. "Tashi ka zauna".
Kamar yadda sarki ya furta, haka Sooraj ya miƙe ya zauna. Dubansa mai martaba ya yi tare da sakin murmushi ya ce. "Ya ɗana, jinin jikina, jigon gadona, naji kuma na gani na fahimta.
Kuskure bai zama ƙarshe ba, fa ce darasi da za'a koya. Na yafe maka, ba don ka cancanta ba, amma don ni uba ne, kuma uba baya ana ɗansa inuwa. Na yafe maka daga dukan zuciyata, ka gyara tafiyarka, tunda ka gane kuskurenka to kana kan hanyar gaskiya".
Cikin farin ciki Sooraj ya ce. "Na gode mai martaba, kamar yadda ka faranta min, nima haka zan kokarta na faranta maka ta hanyar auran Zubaida".
Murmushi manya sarki ya yi sannan ya ce. "Shi ke nen ka shirya gobe za'a ɗaura muku aure".
Nan take annurin kan fuskar Sooraj ya gushe izuwa damuwa. Kallon mai martaba ya yi ya ce. "Afuwa mai martaba, dama yanzu Zahra tana asibiti bata da lafiya, idan babu damuwa a bani lokaci idan ta warke sai a ɗaura auren kuma idan babu damuwa ina son ita ma Zahra na aure ta domin yanzu katafaren nauyin ta a kaina yake, ina son a ɗaura mana aure da ita da Zubaida a rana ɗaya".
Shiru mai martaba na ɗan wasu lokuta kafin daga bisani ya ce. "Shi ke nen zan yi tunani a kai. Yanzu ya kamata kaje ka duba Zubaida domin ba ta a cikin yanayi na jin dad'i, tunda ka tafi take kuka, ya kamata kaje ka duba ta".
Girgiza kai kawai Sooraj ya yi kana daga bisani ya fice daga cikin ɗakin. Kai tsaye ɗakin da ya tabbatar nan Zubaida take ya nufa sannan ya shiga. Nan ya tarar da su Samira a cikin ɗakin. Kallonsu ya yi ya ce. "Ku fita ku bamu guri zamu yi magana".
Taɓe baki Fasma ta yi ta ce. "Ta ya zamu fita mu baku guri, kai da ba mijinta ba?, mu ka san me za ka aikata mata".
Kallonsu Zubaida ta yi ta ce. "Ku je kawai babu wani abu". Jin hakan ya sa su Samira suka miƙe tare da fi ce wa daga ɗakin".
Kallonsa Zubaida ta yi ta ce. "Me ya faru?, ka zo bani haƙuri ne a kan abin da kayi min".
Murmushi Sooraj ya yi tare da mata kallon baki da hankali sannan ya ce.
"Wai ke a tunanin ki zuwa nayi na baki haƙuri?, to ki saurara ki ji da kyau, ba zan taɓa baki haƙuri game da abin da nayi ba domin baki cancanta ba. Nayi kuskure da na taɓa ɗaukar ki da mahimmanci matsayin ƴar uwa. Halin ki bai da mutunci ba. Kuma kada ki taɓa tsammanin komai daga wurina. Zahra ce kawai macen da nake so a rai na ba ke ba".
Sannan ya ƙara da cewa. "Wannan ko mayya ce sai haka, samm baki da zuciya, nasha gaya miki baƙar magana domin ki rabi da ni, amma naga alamun kamar ƙara so na ma ki ke, sai ka ce ni kaɗai ne namiji a duniya".
Kallonsa ta yi a sa'inda hawaye suka fara bin kan ƙuncita. Cikin ƙunci ta ce.
"Na zaɓe ka daga cikin milyoyi, amma kai ko kallona baka yi, zuciyata tana bugawa da sonka amma kai baka san da hakan ba, ba gina mafarkina da kai, amma kai baka taɓa ganina a cikin naka ba. Ina son kafi yadda zan iya faɗi, amma kai baka jin hakan ko kaɗan, sona gare ka gaskiya ne, amma na gane ba kowa ne yake da sa'ar a so shi ba. Wanda zuciyata ta faɗa masa shi ne wanda baya jin komai a tattare da ni. Shin dan na ce ina sonka laifi ne?, ko kuwa ban cancanci a soni ba ne".