← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 65

Sashe 16

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎

*BOOK 2*
PAGE 7️⃣5️⃣▶️7️⃣6️⃣

_________________________
Nan wannan muryar ta fara magana kamar aka. "Ina ku ke tunanin za ku tafi?, ai tunda ku ka shigo ba za ku fita ba har sai kun nemo wannan dukiyar da hujjojin nata sannan za ku iya fita".

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Mun gamo ita ɗin ba mahaifiyar mu bace ba domin ba zai yu mahaifiyar mu ta kawo komai nata nan dajin ba tunda dai ita ba aljana bace ko mayya".

Dariya muryar ya kuma kwashe wa da shi a karo na mara adadi aka ce. "Tabbas ita ɗin mahaifiyar ku ce, dan aka tunda ku ka riga ku ka fara wannan tafiyar ba za ku taɓa koma wa ba sai kun kai ƙarshen ta.

Yana kaiwa nan suka ji dajin ya yi shiru.

"Shi ke nen ta mu ta ƙare, yanzu kenen ɗora tafiyar za mu yi?". Cewar Safira.

"Toh ya za mu yi dole mu cigaba tun da sun ce ba za mu iya fita ba".

Zahra ta faɗa tana mai ɗaukar littafin sannan ta shiga karanta wa. Man suka cigaba da tafiya yayin da suka fara cin karo da shukoki wanda suna ɗauke da nau'in alama na rubutu mai ban mamaki.

Nan take suka fara ganin idanuwa masu haske suna kallonsu. Cigaba da tafiya suka yi ba tare da dakata wa ba.

************
Mami na fita daga ɗakin mai martaba ta nufi part ɗin Sooraj da sallama ta shiga tare da samun guri ta zauna.

Ganin fuskar Mami ɗauke da damuwa ya sa hankalin Sooraj ya tashi, da sauri ya nufi inda mahaifiyar sa ke zaune ya ce. "Mami mene ne abun da ya faru?, shin kishiyoyin ki sun sake yi miki wani abun ne?".

Girgiza kai Mami ta yi ta ce. "A'a Sooraj babu abin da suka yi min".,

"Mami karki ɓoye min, please ki gaya min mene abin da ke faruwa, kin san bana iya jurar ganin ki cikin irin wannan yanayin". Cewar Sooraj yayin da damuwa ke ɗauke kan fuskarsa.

Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Mami ta sakarwa Sooraj kana ta ce. "Ka san inda a ce akwai wani abin zan sanar da kai. Ina son nayi maka wata tambaya".

Kallonta ya yi ya ce. "Ina jin ki Mami".

Tattaro nutsuwar ta Mami ta yi ta ce. "Shin kana da wacce ka ke so a ranka?".

Shiru Sooraj ya yi na ɗan wasu lokacin kana daga bisani ya ba ta martani da cewa. "A'a Mami bani da wacce nake so".

"To me ya sa baka son auran Zubaida?, na san dai Zubaida yarinyar kirki ce kuma tana da hankali ga sanin ya kamata, shin mene ne aibunta?". Cewar Mami wacce ta kafa idanunta kan Sooraj.

Nannauyan ajiyan zuciya ya sauke!, sannan ya ce. "Mami bawai bana sonta matsayinta ƴar kawuna kuma ƙanwa ta, ina sonta a matsayin hakan, amma so na soyayya wanda zai haɗa da aure bana so. Domin kuwa ban taɓa jin ƙaunar ta a raina ba, bana son na aure ta kuma ta dinga fuskantar kalubale daga waje na, shi ya sa kawai na ce ta yi addu'a Allah ya kawo mata na gari wanda ya fini".

Kallonsa Mami ta yi ta ce. "Tunda baka sonta, sai ka koya wa kanka sonta tunda naga kai kaɗai take so kuma take muradi, bana tunanin idan ba ta same ka ba za ta iya yin aure domin gaba ɗaya naga idanuwanta sun rufe a kan soyayyar ka. Bawai tursasa maka nake ka aure ta, ina yin hakan ne saboda kawun ka Sadiq kada ya ji babu dad'i yarsa ta buƙaci abu mun kasa cika mata".

"Mami nayi ƙoƙarin koya wa kaina sonta amma na kasa, bana son na bata wahala idan munyi aure domin ba za ta samu fuskana ba, saboda wasu ƙiyayyar basua taɓa zama soyayya"., Cewar Sooraj.

Haɗa hannayenta guri guda Mami ta yi ta ce. "Dan Allah Sooraj na roƙe ka, ka amince da auren Zubaida ba dan ni ba please".

Dafe kansa Sooraj ya yi ya ce. "Wayyo Mami mene ne aka, ta ya ya za ki dinga roƙo na matsayin ki na mahaifiyata. Kina da ikon yin duk abinda ki ke so a kaina, ba saikin roƙe ni ba. Tunda abinda ki ke so kenen na amince zan auri Zubaida. Shi ke nen kinyi farin ciki". Ya faɗa murmushi ɗauke kan fuskarsa.

Murmushi Mami ta yi ta ce. "Nayi farin ciki sosai Sooraj, Allah ya yi maka albarka, Allah ya faranta maka rai kamar yadda ka faranta min".

Amsa wa Sooraj ya yi da. "Ameen".

Daidai lokacin su Umar ke shigowa cikin part ɗin Sooraj.

Tarar da Mami suka yi a zaune. Ganin hakan ya sa suka yi sauri juyawa da zimmar fice wa.

Daga sama suka ji muryar Mami na faɗin. "Ina kuma za ku je?".

Juyowa suka yi yayin da Aliyu ya ba ta amsa da cewa. "Zamu ɗan je mu zagaya cikin masarauta ne".

"Karya ku ke, dan kun ganni a zaune shi ne za ku koma ko, ni fa kamar uwa nake a gare ku. Dan aka maza ku dawo".

Cikin jin kunya suka ƙarasowa wajan yayin da suka samu guri suka zauna.

Tashi Mami ta yi ta ce. "To ni zan wuce dan aka ku saki jikin ku, ku daina wani noƙe-noƙe ku ɗauka cewar nan tamkar gidan ku ne kunji ba".

Girgiza mata kai kawai suka yi. Nan Mami ta fice ta bar musu ɗakin.

Suna ganin ta fita ya sa suka maida kallon su kan Sooraj sannan Umar ya ce. "Guy what's going on?".

Kallonsu Sooraj ya yi ya ce. "Mami ce ta ce na auri Zubaida".

Zaro idanuwa waje suka yi sannan Aliyu ya ce. "Kuma wane amsa ka bada".

"Wane amsa kuwa zan bada inba na ce na amince ba. Na amince da zan auri Zubaida saboda naga ranta babu dad'i, ni kuma a kan farin ciki Mami zan iya yin komai domin faranta mata shi ya sa na amince". Cewar Sooraj.

Kallon Sooraj Umar ya yi ya ce. "Ita kuma Zahra fa, ya za ka yi da ita?".

Cikin rashin fahimta Sooraj ya ce. "Bangane ita kuma Zahra fa?, Bangane abinda ka ke ƙoƙarin faɗa ba".

Kallonsa Umar ya yi karo na biyu ya ce. "Ina nufin Zahra ba budurwar ka bace ita fa ina za ka saka ta?".

Girgiza kai Sooraj ya yi tare da sakin miskilin murmushi ya ce. "Ni wallahi ka bani dariya, an gaya maka cewar soyayya nake yi da Zahra ne?, ita ɗin fa kawai ƴar aiki ce a masarautar nan, kuma babu wani abu tsakani na da ita, ni in ba ma ciwon kai da take sanya ni me take yi, duk ta bi ta addabi mutanen masarautar nan, na faɗa maka ƙarshen ta ma kishiyoyin Mami da ƴaƴan kishiyoyin gaba ɗaya ba ta bar kowanensu ba duk saida ta yi faɗa da su. Ai duk wanda ya auri irin wannan yarinyar shi da kwanciyar hankali har abada".

Jin furucin Sooraj ya sa ran Umar ya ɓaci. Miƙe wa tsaye Umar ya yi ya ce. "Ƙarya ka ke Sooraj, ƙarya ne ka ce baka son Zahra, na tabbatar da cewa kana mutuwar sonta domin ni naga hakan a idanunka tun muna wannan dajin. Me ya sa a koda yaushe ka ke son bayyanar da abin da ba shi ne gaskiyar ka ba, na san cikin ranka ma addu'ar da ka ke yi shi ne kada ta kasance ita ce za ta mutu cikin dajineda suka tafi, kuma yanzu kace wai baka sonta. Ni fa abokin ka ne, na san ka ciki da waje dan aka baka isa ka ɓoye min komai ba".

Ajiyan zuciya Sooraj ta sauke sannan ya ce. "A kan me ya sa wai zan sota, idan ina sonta ai za ku sani, ai da tuni lokacin da Mami ta tambaye na faɗa mata, a kan me ya sa zan ɓoye. I don't love her kawai dai muna shiri da ita ne".

"Shi ke nen tunda ka ce baka sonta. Ko ba daɗe, ko ba jima gaskiya za ta yi halinta, idan ta yi tsami zamu ji".

**********
Jirgin Alhaji Abdullahi ya sauka da misalin ƙarfe huɗu da rabi (4:30) a garin Jigawa.

Nan su Mk da dpo suka zo suka ɗauke shi a airport. Nan suka yi masa tarba mai kyau.

Shiga cikin mota ya yi sannan Mk ya ce. "Yallaɓai yanzu ina za mu je?". Ya tambayi Alhaji Abdullahi.

Amsa Alhaji Abdullahi ya bashi da cewa ina son ka wuce gidan mahaifin Lailah wato matata.

Da mamaki Mk ya dube shi sannan ya ce. "Me za mu je muyi a chan kuma yallaɓai?".

Amsa Alhaji Abdullahi ya bashi da cewa. "Kai dai kayi abin da na ce idan munje chan za ka san koma mene ne

Babu musu Mk ya tada mota sannan suka nufi hanyar gidan. Mintuna ƙalilan ya ɗauke suka ƙarasa gaban gidan.

Horn suka yi yayin da mai gadi ya duba ko wane ne a wajan.

Ɗaga masa hannu Alhaji Abdullahi ya yi.

Mamaki baba mai gadi ya shiga yayin da ya shiga tunani a ina ne ya san wannan fuskar nan ya tuna da mijin Lailah ƴar mai gidan.

Washe haƙora Baba mai gadi ya yi sannan ya buɗe musu gate.

Nan motar su ta shiga cikin compound ɗin gidan.

Parking Mk ya yi daga bisani suka fito daga cikin motan. Jiki na rawa Baba mai gadi ya yi saurin rufe gate ɗin gidan yana mai ƙwalla kiran mutanen cikin gidan.

"Hajiya kuna ina ne ku fito ku zo ku ka wanda ya zo". Cewar Baba mai gadi.

Su Grandma da ke cikin gida suka jiyo muryar Baba mai gadi hakan ya sa su suka miƙe tsaye tare da nufar hanyar waje domin ganin Abin da ke faruwa.

Grandpa kuwa fitowa ya yi daga cikin ɗakin sa yana mai jan wheel chair ɗin sa sannan ya nufo parlour daga bisani ya nufi waje.

Zaro idanuwa waje su Grandma suka yi ganin mijin Lailah tsaye a gaban su. Share hawayen da ke ƙoƙarin zubo mata Grandma ta yi ta ce.
Chapter 16 · 0% Book details