← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 65

Sashe 38

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi miss Lailah ta yi ta ce. "Babu abin da kayi min. Kayi magana da zuciya, ba da gardama ba, ba da ƙiyayya ba. Kuma ni na gane zuciyar da take roƙon yafiya, tuni ta fara tuba. Na yafe wa mahaifinka, don kai ma ɗa na ne. Ba zan bari kuskuren sa ya zama ƙuntatawa a tsakanina da kai ba. Rayuwa ko yaushe tana koyar da mu cewa, ba duka laifi ake bi har ƙarshe ba. Wasu gafara ce take tsarkakewa. Ka tuna wannan, kai ɗin ɗan ƙawata ce ka ga kaima ɗana kuma zan ƙauna ce ka kamar yadda zan ƙaunaci ƴaƴana, ba don mahaifinka ba, sai don kai da zuciyarka mai taushi. Ka tsaya da gaskiya, ka nemi gafara da ɗoki. Wannan kaɗai ya isa ya sa a rungume ka da hawaye.
Kai ɗa na ne, kuma zan ci gaba da yi maka addu’a kamar ɗana na jini. Na yafe. Na manta. Allah ma ya gafarta mana gaba ɗaya".

Nan kowanensu ya amsa da Amin.

Dubansu Mom ta yi ta ce. "Yanzu dai ku tawo mu tafi gida yau akwai labarai kala-kala zan baku, kuma yau dole mu raƙashe na dawowar Maman triplet".

Nan take gaba ɗaya suka kwashe da dariya.

Tafiya suka fara yi a cikin dajin tsawon lokuta masu tsayi kafin daga ƙarshe suka isa bakin titi.

"Nan ai Kano ne". Cewar Zahra.

Kallonsu Sooraj ya yi ya ce. "Yanzu abinda za'a yi ku tawo mu je masarautar mu a sauke ku a masaukin baƙi idan ya so zuwa gobe sai ku tafi".

Nan Daddy ya ce. "Baka ganin da matsala kuwa, domin muna da fa yawa, ina ganin kawai mu kama hanyar jigawa".

"Aba Daddy sai kace bamu zama ɗaya ba, kada ku damu domin baku yi yawa, in ma ɗaki ɗaɗɗaya ku ke buƙata za ku samu ku dai ku tawo mu je".

Nan suka fara tsaida adaidaita. Mamaki ne ya kama mutane ganin Yarima a bakin titi na tsaran napep. Nan dai suka samu masu adaidaita suka tsaya, yayin da gaba ɗaya suka au napep sannan Sooraj ya kwatanta musu inda za su.

Ba tare da ɓata lokaci na masu napep suka yi hanyar gidan sarki.

Mintuna Talatin ya ɗauke su suka isa masarauta. Yayin da Sooraj ya sallami masu adaidaita suka tafi. Shiga ciki suka yi. Nan fadawa suka shiga miƙa gaisuwarsu sosai haka yi musu tarba mai kyau.

Fito wa Mami da mai martaba suka yi farin ciki ɗauke kan fuskokin kowanensu, cikin farin ciki Mami ta ce. "Maraba lale Miss Lailah muna miki barka da zuwa, barkan ku da zuwa".

Su Gimbiya Saratu kuwa suna laɓe jikin window suna kallon duk abinda ke faruwa, nan Mami ta kai su wajan ajiye baki na musamman yayin da ta sa ƴan aiki suka kawo musu abin taɓa wa sannan abinci.

Nan Mami ta bawa su Zahra ɗaki ɗaya su uku wanda za su zauna a ciki. Ya kasance a cikin part ɗin da suke ɗakin yake. Kowa ya watse inda Mami ta kasance a part ɗin da haka tarbi su Miss Lailah tana mai taya su hira".

Duban ɗakin da haka basu Safira ta yi ta ce. "Masha Allah ɗakin ba laifi ya yi kyau".

Nan Zahra ta ce. "Ke dai bari Safira, ina ɗan zuwa zan je wajen abokaina ina dawo wa".

"Su waye kuma abokan naki?". Cewar Amrah.

Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Idan na ce abokai ina nufin abokan faɗa na". Ta faɗa tare da fita kai tsaye part ɗin su Gimbiya Saratu ta nufa.

Tana kaiwa ƙofar part ɗin su ta ƙusa kai ciki, nan ta tarar da Zubaida ma na ciki.

Tafa hannu Zahra ta yi ta ce. To fa ga mu mun dawo ba abinda ya same mu, ƴan baƙin ciki sai dai su mutu wallahi. Yadda haka gan ni haka za a bar ni. Idan kiran mutuwa ta ne a bakin ku, to ku dinga shan ruwa domin bakin zai bushe.
Mutuwar da ku ke jira, ku gyara kujerun jiran. Domin mai rai yana ci gaba da numfashi, koda zuciyarku na ƙuna.
Ina roƙon Allah ya ba ku lafiya domin ku ci gaba da ganin cigabanmu, tunda hakan ke ba ku ciwon zuciya". Ta faɗa tana mai watsa wa Zubaida harara.

A fusa ce Samira ta ce. "Ammi ki bar ni na yaga mata rigar mutunci ta yadda koda fuskar mu ba za ta yi tunanin kalla ba".

Dakatar da ita Gimbiya Saratu ta yi da cewa. "Rabu da ita ai wanda ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake, ai shirin mu ba'a nan ya ƙare ba domin, kuwa akwai cigaba".

Murmushi Zahra ta yi tare da gyara zaman ɗankwalin kanta sannan ta riƙe ƙugunta ta ce. "Ku shafa wa zuciyar ku ruwan sanyi domin kuwa yanzu na dawo, kun sani cewa ni bana gajiya sai dai ku gaji, duk yarinyar da bata fasa shigowa gona ta ba to bata cika ƴar iska ba. Ni fa tunani na riga na gane cewa iskokai ke damunku, ya kamata ku je dawanau domin kuna buƙatar likitar mahaukata".

Tana gama faɗin hakan ta maida kallonta kan Zubaida sannan ta ce. "Ke kuma ya ranki?, wato harda turo wasu shashashun ƴan daba domin su kashe ni a asibiti ko?, wai duk nan saboda zafin kishi ko?, to ki sani yanzu ma haka soma dama ya furta yana so na, nima kuma sonshi nake, karki bari na saki a gaba dan wallahi ba za ki ji da daɗi ba, ba wai boka ko Malam zanyi miki ba, amma baƙin ciki ne zai kusa kashe ki, nafi son dama na zauna da irin ku masu zafin kishin nan domin koya muku hankali"

A fusa ce Zubaida ta nufe ta ta ce. "Wallahi Zahra ina miki kashe di ki fita daga rayuwar Sooraj, ni tashi ce shi kaɗai shi ma kuma nawa ne ni kaɗai, ba zai yu na raba namiji da wata ba wallahi".

Dariya Zahra ta kwashe da shi ta ce. "To a fara ɗaura auren tukun mu gani daga nan za mu ga ko za ki samu bakin magana. A da na ce zan bar miki Sooraj ki aure shi, amma tunda ki ka yi yunkurin kashe ni, to saina aure shi koda zuciyata ba ta so. Ke ƙarewarta ma nan da sati zan sa hakan ya kasance, idan kuma banyi ba ban cika haifaffiya ba".

Ta faɗa tare da fita daga cikin.

Babu abinda Zubaida ke faman yi sai huci.

________________

Ɓangaren John kuwa, har izuwa wannan lokaci ya kasa motsa wa, a sa inda gaba ɗaya ya fita daga cikin hayyacin shi yayin da numfashin sa ke barazanar ɗauke wa.

Da sauri yaronsa da suka zo gidan tare ya yi ƙoƙarin rayuwarsa amma ina hakan ya cutura. Domin ya gaza cetan sa rai ya yi halinsa. Nan yaronsa ya kurma ihuu yayin da ya ja gangar jikinsa a ƙasa har izuwa wajan mota. Nan Baba mai gadi ya fara tambayan shi su waye, yaushe suka shigo. Bai ba shi amsa ba ya cinciɓi John a kafaɗa sannan ya fice daga gidan.

_______________
Bayan fitowar Zahra suka yi kiciɓus da Sooraj. Murmushi ta yi sannan ta ce. "Yahya Sooraj ina za ka je?".

Kallonta ya yi ya ce. "Zahra kenen, daga dawowar ki ko huta wa baki yi ba, amma harkin je part ɗin su Ammi, tsabar masifa na cinki. Gaskiya ki dinga shan ruwan alwala ko ba laifi za ki ɗan samu sauƙin wannan masifar".

Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Ka fara ko, komai ka ce ina da masifa, ni fa ba masifaffiya bace kawai dai bana ɗaukar rainin hankali ne, muka zuwan da nayi ma gaishe su naje yi fa ba komai ba".

Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "Da a ce ban san ki ba ne shi ne za ki gaya min hakan na yarda, amma na sanki ciki da waje babu abin da za ki gaya min na yarda".

Daidai lokacin Zubaida ta fito daga cikin part ɗin. Zahra na ganin hakan. Ta kalle shi ta ce. "Wayyo masoyi ƙafana ya gurɗe". Ta faɗa tana mai faɗuwa ƙasa.

Da sauri Sooraj ya isa gare ta ya ce. " Me ya faru, sannu kinji ya faɗa tare da saɓata a bayansa sannan ya nufa hanyar ɗakin ta da ita.

Kallon Zubaida Zahra ta yi tare da yi mata gwalo.

Nan take Zubaida ta ji kamar ta haɗiye zuciya ta mutu.

Babu zato suka ji ta fasa ihuu!. Da sauri Sooraj ya sauke Zahra, a sa'inda ihuunta ya janyo hankalin su Mami da mai martaba tare da su Safira da kuma su Gimbiya Saratu. Nan da nan parlour ya cika.

Fashe wa da kuka Zubaida ta yi ta ce. "Gaskiya abinda ake min a gidan nan baya kyautuwa, an ce za'a aura min Yahya Sooraj amma har yanzu shiru, wai sai yaushe za'a yi mana auren, gashi kuma wannan Zahra tana son ya ƙwace min shi daga gare ni".

Cikin rashin fahimta mai martaba ya ce. "Kamar ya".

Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Kada ku tada hankulanku, ku koma dan Allah ciwon basir ke damunta shi ya sa ta ƙwallah ihuu, amma ku koma ni nan zan ji da ita".

Girgiza kai kawai Mami ta yi murmushi kan fuskarta, dan kuwa ya san cewa Zahra maida Zubaida ta yi kamar mahaukaciya.

DAN ALLAH KUYI LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH. SABODA ALLAH PLEASE🥹 🙏🙏🙏🙏🙏🙏

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎

*A'ISHA M.B*💞💞

*BOOK 2 PAGE1️⃣0️⃣2️⃣▶️1️⃣0️⃣3️⃣*
________________________
Bayan ficewar kowa ya rage sauran Zahra, Sooraj da kuma Zubaida.

Maida kallonta Zahra ta yi kan Sooraj ta yi ta ce. "Yarima na, ina son ka ɗan bamu guri zamu ɗan tattauna da Zubaida".

Girgiza kai kawai Sooraj ya yi ya nufi hanyar part ɗin mai martaba dama nan zai je.
Chapter 38 · 0% Book details