Sashe 8
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai a kwanan nan naji labarin wai Lailah na raye amma babu wanda ya san inda take. Kuma nayi mamaki ganin Aliyu yana yi wa wanda ya yi wa wacce ya ɗauka kamar mahaifiya aiki. Nayi tunanin cewa ko Aliyu bai san halinsa ba ne, amma da nayi bincike sai na gano cewar kaima Aliyu kana taimaka masa ne".
Shiru Aliyu ya yi ya ce. "Ni ba taimaka masa nake ba ina yin hakan ne domin na tona masa asiri".
Share hawayenta Safira ta yi ta ce. "Toh wane ne ya taimaka wa mahaifiyar mu har ta kasance a raye?".
Amsa Mk ya ba ta da cewa. Ni ma ban sani ba iya wannan labarin kaɗai shi ne iya kacin abin da na sani".
Kallonsu Sooraj ya yi sannan ya ce. "Ni ne nan na taimaka mata".
Kallonsa Zahra ta yi da sauri tare da miƙe wa sannan ta ce. "Kodai mahaifiyar ta mu ce na gani kwanaki a asibitin da muka je tare?".
Girgiza kai Sooraj ya yi sannan ya ba ta amsa da cewa. "Ƙwarai da gaske ita ce nan".
Nan take gaban Zahra ya yanke ya faɗi!.
🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
NA SAN NAYI LAIFI AYI MIN AFUWA WALLAHI MAKARANTA CE TAKE SA BANA YI MUKU UPDATE A KAI-A KAI. KUYI MIN UZURI NA SAN DA CEWA KUNA HAƘURI DA NI DAN ALLAH A CIGABA DA HAƘURI🙏😓🙏.
LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
Follow the 🌺🌎A'ISHA M.B🌹 HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝
بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*BOOK 2*
PAGE 6️⃣5️⃣▶️6️⃣6️⃣
*INA YI WA KOWA BARKA DA SALLAH TAQABBALALLAHU MINNA WAMIN KUM EID MUBARAK ALAYNA WA ALAIKUM🙏🙏🙏🙏*
*KUNƊIN CINIKAYYA*
Kallon Sooraj Zahra ta yi sannan ta ce. "Bangane ba, kenen ka san mahaifiyar mu?". Murmushi Sooraj ya yi ya ba ta amsa da cewar. "Ƙwarai da gaske na san Mahaifiyaku shekarun baya da suka shuɗe".
Ana shirye-shiryen biki n gargajiya a wani ƙauye, ni da kuma Mami munje ƙauyen Jakadiyar Mami wacce Mami ta ɗauka tamkar ƴar uwa. Kasancewar ana bikin ƴarta hakan ya sa Mami ta ce na bita, dalilin cewa ni ɗin ina son zama likita domin a lokacin ma na gama secondary school na rubuta JAMB. Mami ta sani naje ƙauyen domin na ƙaro experience hakan likitan da nake son zama.
Kamar yadda Mami ta buƙata aka na bita muka nufi wannan ƙauyen Ɓaɓura. Mun samu tarba mai kyau kasancewar mu daga gidan sarauta. Babu wanda ya san da cewar mun tafi ƙauyen Jakadiyar Mami a masarauta sai mai martaba kaɗai.
Sosai aka tarbe mu yayin da aka dama mana fura da nono kasancewar akwai ƴan fulani a cikin su. Bara na kaiku kai tsaye cikin labarin.
Kallo na Mami ta yi ta ce min. "Sooraj ya ka ga ƙauyen? ya yi ko?". Murmushi na sakar mata sa'annan na mayar mata da martani cewa. "Tabbas ƙauyen akwai dad'i ga sanyi mai ni'ima na kaɗawa. Saida muka ɗau kwanaki uku ana biki ba tare da na fita ko ina ba. A kwana na ukun shi ne ranar auren inda aka kaita gidan mijinta sannan a wannan ranar wani abu da ba mu yi tsammanin zuwansa ba ya afku.
Bayan mutanen biki sun watse ya rage ni da Mami da kuma Jama'ar garin kaɗai. Kwatsam ina zaune cikin daƙi na jiyo ayaniyar mutane daga waje. Miƙe wa nayi tsaye sannan na leƙa ta taga ganin cunkoson mutane hakan ya sa na shiga ruɗani. Cikin kasala na fita waje tare da ƙarasawa wajan da mutanen suke. Take gabana ya yanke ya faɗi!, sakamakon harba da nayi da matar da ke kwance cikin jini, gaba ɗaya jikin duk raunuka, yayin da harbin bindiga ya kasance ta gefen zuciyarta. Ganin yadda hankalin Mami ya yi matuƙar tashi hakan ya sani cikin damuwa. Ɗaya daga cikin mutanen ne naji ya faɗin. "Munje rafi ɗebo ruwa shi ne muka tarar da gangar jikinta a yashe, gashi ta ji raunuka sosai ba lallai tana da sauran numfashi ba".
Kallon mutumin Mami ta yi ta ce. "Faɗi alkhairy ko kayi shiru, kallo na Mami ta yi hankali tashe ta ce. "Ka ga Sooraj na san baka zama likita ba, amma na san ka koyi abubuwa da dama wajan kawunka Sadiq, domin shima likita ne kuma a koda yaushe in zai yi aikin theatre ko wani abun kuna kasancewa a tare na san wannan ba zai gagare ka yi ba saboda na san basirar da ubangiji ya ba ka, please ina son ka taimaka ka duba ko tana da sauran rai sannan a kira masu magani su cire mata bullet ɗin nan".
Girgiza mata kai nayi hankali na a tashe na ce da ita. "Samm ba zan iya ba, domin a wannan lokacin ban san komai ba dangane da kiwon lafiya kasancewar kawuna Sadiq yana da na raka shi asibiti ne kaɗai ba wai yana bari na shiga ɗakin da suke duba marasa lafiya ba. Ran Mami ya yi matuƙar ɓaci jin cewar na ce ba zan iya ba. Ganin ranta ya soma ɓaci hakan ya sa zuciyata ta karaya a yayin da tausayin matar da ke kwance ya kamani. Gaba ɗaya ta galabaita ko motsi ba ta yi, hakan ya sa na isa inda take kwance a yashe, a sa'inda mutanen ƙauyen suka bini da kallo, durƙusawa nayi kusa da matar tare da kafa kunne na wajan saitin zuciyarta. Zaro idanuwa nayi waje jin numfashinta na ƙoƙarin ɗauke wa, a yayin da zuciyarta ke buga wa da sauri-sauri.
Saurin maida kallo na nayi kan jama'ar ƙauyen na ce, tana da buƙatar taimakon gaggawa, bugun zuciyarta ya ƙaru sosai kuma dole tana buƙatar ayi mata aiki kafin lokaci ya ƙure kuma wannan ba batun maganin gargajiya ba ne ana da buƙatar a kaita asibiti.
"Shin da akwai asibiti a ƙauyen nan?". Na tambayi mutanen ƙauyen. Ɗaya daga cikin su ya ce. "Akwai saidai gomnati ta daɗe da rufe asibitin sakamakon gurbataccen magunguna da ake badawa da kuma likitocin da aka saka waɗan da basu san komai ba dangane da kiwon lafiya, hakan ya sa gomnati ta rufe asibitin".
Ba zato na ji an damƙe min hannu a matuƙar razane na juya tare da maida kallona kan matar da ke kwance. Da mamaki na, naga ta buɗe idanuwanta yayin da babu abin da take faman furtawa sai kalmomi guda uku. "Me ya sa suka aitaka min aka?, Ku ceci yarana daga hannun azzalumai da suke ƙoƙarin ganin bayana, saboda dukiyata suka aikata min haka, wane riba suka samu a kaina?, dole ina da buƙatar koma wa kotu". Kalmomin da ta shiga maimaita wa kenen.
Cikin rashin fahimtar maganar ta na dube ta a yayin da Mami ta ƙaraso inda take ta ce. "Su waye yaran naki?, Su waye ke son kwashe dukiyarki?, kuma wane kotu ki ke magana a kai?". Jin shiru ba ta sake magana ba ya sa Mami ta sa aka cinciɓe ta sannan aka kaita wajan malamin gargajiya. Bayan kwanaki biyu aka tabbatar mana da cewar ƙwaƙwalwar ta samu buguwa kuma maganin gargajiya ba zai yi aiki ba sai an haɗa da na bature amma dai an yi nasarar cire bullet ɗin jikinta.
Nan Mami ta kira mai martaba ta sanar da shi halin da ake ciki. Take sarki ya sa aka turo da motar Asibiti daga Kano sakamakon cewar asibitocin da ke Jigawa sunƙi yarda a kawo ta domin suna iƙirarin cewa ita ɗin mai laifi ce. Nan aka fara mata aiki a Kano, aka sarki ya kashe maƙudan kuɗaɗe.
Sati guda ta yi a asibiti tana jinya, ana tsaka da aka naji ɗaya daga cikin likitocin na faɗin zai sanar da ƴan sanda cewar mai laifin da suke nema Mrs lailah tana nan a asibitin su. Jin hakan ya sa na yi gaggawar ɗauke ta daga asibitin sannan na kaita fadar mu tare da ajiye ta a ɓoyayyen ɗakin ajiyana wanda babu wanda yake shiga face ni kaɗai. Hakan ya sa na sakawa ɗakin password da sunanta tare da saka thumbprint ni kuma na ci-gaba da karatuna a lokacin na samu admissionna fara karatuna a ƙasar London.
Har izuwa wannan lokaci babu wanda ya san da zaman Mrs Lailah a fada sai ni da kuma Mami domin ita ce kawai bana iya ɓoye wa sirri na.
Domin kada wani abun ya samu lafiyar Mrs Lailah hakan ya sa Mami take gayyatar kawun mu Sadiq yana dubata a sirrance. Anyi nasara ta fara samun sauƙi bayan shekaru biyar na dawo daga ƙasar London a lokacin Sarki yake min albishir da cewa ya gina min asibitin kaina wanda ya gina da sunana wato Sooraj Health care. Jin hakan ya sa cikin farin ciki, bayan wanda sarki ya gina min nima na gina nawa na saka ma'aikata sannan suke kula da Mrs Lailah. Bayan wasu kwanaki ɗaya daga cikin ma'aikatan yake sanar da ni cewa BP ɗin ta ya yi rising sosai ga depression na damunta. Alamu sun nuna akwai abin da take so ba ta samu ba, sannan tana ɗauke da fansa cikin zuciyarta, kuma mun tambaye ta meke damunta taƙi sanar da mu alamun tana da zurfin ciki. Bayan nan ma ta fara samun mental problem za ta iya samun sauƙi ne bayan ta samu abin da take son cimma wa ko kuma ta ga waɗan da take ƙauna ko wanda ta sani.