Sashe 1
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*BOOK 2*
PAGE 5️⃣7️⃣▶️5️⃣8️⃣
_______________________
Cikin tsantsar tashin hankali da firgici! su Suraj suka ja da baya yayin da zufa ya fara ƙetowa kowanne daga cikin su. Nan take zuciyoyin kowanne a cikin su ya shiga bugawa da sauri sauri! yayin da suka rasa mafita, nan suka dubi su Zahra da ke kwance ƙasa a sume yayin da suka fara nufar inda suke cike da mamaki suke binsu da kallo.
Cikin rashin sa'a su huɗu suka ji saukar allura a bayan wuyansu nan take suka faɗi ƙasa cikin fitar hayyaci suka fara nufar inda su Zahra suke domin kuɓutar da rayukansu, amma cikin rashin sa'a kidnappers ɗin suka bubbuga musu bayan bindiga a kansu. take suka faɗi sumanmu ba.
ganin hakan ya sa kidnappers ɗin suka fara ɗaukan su ɗaya bayan ɗaya suna shigar da su kangon da ke tsakiyar dajin tare da kwantar dasu cikin kangon sannan suka ɗaɗɗaure su ɗaya.
Ɓangaren DPO kuwa aka ya saka police suka yi masa investigation a kan inda Zahra take. Jin labarin cewar Zara tana masarautar da ke garin kano hakan ya sa Dpo ya nufi kanosannan ya nufi kano ba tare da ɓata lokaci ba. Yayin da ya shiga kallon wannan littafin da ke hannunsa tare da tunanin. "Ko mene ne a wannan littafin?". Ya tambayi kansa.
*****
Ranka shi daɗe mai martaba gaskiya ne abinda na gani sam Zahra bata aikata wa laifin da ake zargin ta da shi ba, ba Zahra bace ta saka wa mami guba ba tabbas naga su Samira sune suka je suka sawa wa Mami guba a lemo. Gudun abin da zai je ya dawo ya saka na yi mata video lokacin da suke sa wa".
"wannan maganar karya ce, ta yaya za'a ce Samira ce ta saka wa Mami guba ba fitsararren yarinyar nan Zahra ba? wannan sam karya ne tabbas na san Samira baza ta iya aikata hakan ba. Saboda me zata sa wa Mami guba? ai idan ta sa wa Mami guba tamkar ta sa mun ne domin kuwa Mami tamkar uwa take a gare ta akan me ya sa zata aikata hakan a gare ta?". Cewar Gimbiya Saratu.
Murmushin takaici kawai Junaid ya yi sannan ya ce. "aba gimbiya ya ya za ki yi karya kiji tsoron Allah fa. Tabbas naga Samira da ido na idan baku yadda ba ku kalli wannan bidiyon ku gani". Junaid ya faɗa tare da ajiye wayarsa sannan ya kunna videon da ya yi wa Samira lokacin da take saka wa Mami abu a cikin lemo. take gaban kowanne a cikin su ne ya faɗi ganin yadda Samira take zubawa Mami abu a lemo tana waige-waige hakan ya sa ran mai martaba ya ɓaci!, yayin da ya ji zuciyarsa babu daɗi kallon kowanne a cikin su ya yi sannan ya ce . "Shin da gaske abinda nake gani gaskiya ne? mene ne Mami ta aikata muku da zaku yi yunkurin kashe ta ita? dan tamkar uwa take a gare ku me ya sa zaku yi yunkurin kashe ta?. ku sani cewar wannan abun da ku ka aikata sannan ku ka sa muka zargi yar mutane hakan ba zai tafi a banza ba domin kuwa sai an bi mata haƙƙinta. Dan aka dole na ɗau hukunci akanki Samira tare da su Fasma sannan da ke Yusra gaba ki ɗayan ku sai na yanke muku hukunci". Nan take sarki ya sa fadawa su kama su Samira domin zartar musu da hukunci.
Mai da kallon sa sarki ya yi kan gimbiya Saratu da Talatu sannan ya ce "Kuma ba zan barku ba domin na san ku ne ku ke goya musu baya a duk abubuwan da suke, na san in ba in ba ku ba babu wanda zai sa su suyi wannan aika-aikan dan na san kune jagaban su. Don aka dole ne na zartar muku da hukunci mai tsanani sannan kuma ba zan lamunci ko wacce a cikin ku ta ɓata min sunan masarauta ta ba don haka gaba ki ɗayan ku na umarci ko wacce a cikin ku ta koma gidan uban ta sai na neme ta".
Zaro idanuwa waje gaba ki ɗaya ƴan parlor suka yi. Jin hakan ya sa gimbiya saratu da talatu suka tsugunna kan gwiwowin su tare da fara bawa sarki haƙuri sannan suka fara nadamar abinda suka aikata wa Mami hakan ya sa suka fara kuka wiwi hawaye na bin kan ƙuncin su. Ganin hakan ya sa Mami ta ce. 'afuwa ranka shi daɗe, kayi haƙuri dan Allah kada ka yanke musu wannan hukuncin kaga sun tara yara sannan kuma ba zai yi daɗi a ce suna gimbiyoyi kuma a ce su koma gidan iyayen su ba, ya kamata a ce kayi tunani kan wannan hukuncin da kayi na san sun yi nadama akan abinda suka aikata kawai dai ka yafe musu dan Allah dan annabi ba dan ni ba ko dan 'ya'yan da suka haifa".
ɗan jimm sarki ya yi alamun yana nazari a kan abinda Mami ta faɗa. Lokaci ɗaya ya dube su baki ɗaya sannan ya ce da su shikenen ku miƙe tsaye saboda ita na yafe muku abinda ku ka aikata amma dole ku gurbi abinda ku ka shuka wata rana idan har ku ka cigaba da wannan hali sai na kora ku gidan iyayen ku sannan ba iya kora zan yi ba zan yanke muku hukunci mai tsanani ne nan gaba, dan aka ku bawa Mami haƙuri".
Cikin kiɗima gaba ɗaya suka miƙe tsaye cikin jin daɗi sannan suka kalli Mami suka ce. "Dan Allah kiyi haƙuri ki yafe mu, ba zamu sake aikata miki aka ba, mun tuba mun koma ga Allah". suka faɗa kansu a sunkuye.
Murmushi kawai Mami ta yi sannan ta ce. "Babu komai, muna yi wa Allah laifi yana yana yafe mana balle mu ƴan adam, ni na yafe muku duniya da lahira".
Cike da farin ciki suka yi wa Mami godiya. Kana sarki ya umarce su da su koma ga ɗakunan su.
Maida kallonsa ya yi kan fadawan da ke riƙe da su Samira sannan ya umarci Fadawan da su suka su Samira cikin kurkuku kana suyi musu bulala ɗari ɗari ga ƙowacce a cikin su.
Jin hakan ya sa su fashe wa da kuka suna mai neman Mami da cece su. Duk yadda Mami ta yi dan cetar su Samira gaba ɗaya ya tafi a banza domin kuwa sarki bai saurari Mami ba ko kaɗan. Hakan ya sa fadawa suka tasa ƙeyar su Samira gaba sannan suka kai su ɗakin hukunci.
Cikin jin daɗi Junaid ya ɗauki wayarsa wacce ita ce shedar komai sannan ya nufi part ɗin sa.
Maida kallonsa sarki ya yi kan Mami sannan ya ce. "A'isha ina mai baki haƙuri bisa ga duk abinda suka aikata miki dan Allah kiyi hakuri na san ba laifin su ba ne ba laifi na ne da na haɗa ku guri ɗaya ku ke zama da a ce na raba muku guri da hakan ba zata faru ba"
"Murmushi Mami ta yi tare da girgiza kai sannan ta ce. " A'a yadda ka haɗa mun guri ɗaya shi ne zaman tare hakan kuma yafi domin kuwa sai mun fi haɗa kanmu, idan ka raba mu kaga ba zai yiwu mu haɗa kawunan mu ba don haka ni banga wani laifi akan aka ba, baka mun komai ba dan haka bana bukatar kama bani haƙuri, ni yanzu buri na shi ne kawai Zahra ta dawo mu nemi afuwar ta domin kuwa anyi mata sharri kan abinda bata aikata ba".
murmushi sarki ya yi sannan ya ce. "in sha Allahu zan nemi duk inda da Zahra ta shiga sannan nasa a kawo ta domin mu bata haƙuri , na san Suraj yana tare da ita a halin yanzu. Gaskiya A'isha kina da matuƙar sauƙin kai Allah yayi miki albarka, ina mai gode wa Allah da ya bani mata mai matukar sauƙin kai da biyayya kamar ki".
Murmushi Mami ta yi sannan ta ce nima ina mai godiya ga ubangiji wanda ya bani miji wanda ya maida ni gimbiya cikin masarautar sa sannan ya maida ni gimbiya a cikin zuciyarsa".
Ta faɗa tana mai sunkuyar da kanta ga mai martaba.
"WANE NE MAI MARTABA?, WANE NE SOORAJ?".
BARA MU WAIWAYA BAYA DOMIN SANIN TARIHIN WANNAN MASARAITA.
Sarki Haruna Yusuf shi ne asalin mahaifin Kabir Yusuf wato mai martaban yanzu sarki haruna ya kasance mutum mai mulkin mutane cikin adalci ba tare da zalunci ba, ya kasance mutum mai sauƙin kai tare da taimakon talakawa yana da mace guda daya tilo mai suna Hafsat.
Sun kasance suna zaman lafiya tare da matarsa Hafsat ba tare da sun samu matsala ba. Yana da ɗa daya wato Kabir sarki yana ji da shi tamkar rayuwarsa amma Sarki yana fama da cutar ɓarin jiki hakan ya sa bayan girman Kabir yake fafutuka wajan neman wa mahaifin sa maganin waraka amma duk abubuwan da za'ayi gaba daya suna tashi a banza ne, hakan ya sa hankalin gimbiya Hafsat ya ƙara tashi sosai fiyeda da yayin da koda yaushe tana cikin addu'ar Allah ya warkar da mijinta.
Kabir ya haɗu da Mami ne lokacin da yaje kasar malaysia karatu hakan ya sa suka haɗu sannan suka fara soyayya wadda har ya kai ga amfara maganar saka ranar aurensu ana tsaka da haka a kaji labarin cewa zuciyar sarki ta buga yayin da ya rasu. Hankalin kowa a masarautan nan ba ƙaramin tashi ya yi ba yayin da aka yi ta koke-koke domin an yi babban rashi na sarki. Bayan an suturta shi an kaishi gidan sa na gaskiya ita ma Gimbiya Hafsah zuciyar ta ta buga ta faɗi ƙasa, nan rai ya yi halinsa. Ranar ya zamar wa Kabir bakar rana wanda bazai taba mantawa ba.
Bayan wasu kwanaki da rasuwar iyayensa ne aka naɗa Kabir zuwa sabon sarkin wannan masarauta nan ya yi aure wato matar shi ta farko A'isha duda cewar ɗan uwan A'isha wanda ke garin Jigawa baya son auren amma ba yadda ya iya aka ya amince saboda farin cikin ƙanwarsa. Bayan wasu kwanaki A'isha ta samu juna biyu sannan ta haifo ɗanta mai suna Sooraj.