Sashe 31
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sunkuyar da kai ƙasa parrot ɗin ya yi ya ce. "Kayi haƙuri da a ce zan iya taimaka maka ne to zan taimaka maka, amma dokar wannan tsibirin indai haka shiga ba'a fita, dole ɗaya cikin biyu ya faru ko kuyi rayuwarku a nan tsawon numfashin ku na ƙarshe ko kuma halittun cikin wajan nan su kashe ku".
Karaya Sooraj ya yi yayin da ya sallama wa Allah komai. Basu yi aune ba suka ga Zahra ta buɗe idanuwanta yayin da farin haske ya fito daga idanuwanta wanda ya haskaka gaba ki ɗaya ilahirin dajin. Nan take ƙasar wajan ta soma girgiza. Yayin da anya ya soma bayyana.
MU HAƊU A PAGE NA GABA🙏🙏🙏🙏
KUYI SHARING DOMIN SAMUN UPDATE KAN LOKACI.🤸♀️
KADA KU MANTA DA LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏🙏🙏🙏🙏🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
بسم الله الرحمن الحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*BOOK 2 PAGE9️⃣0️⃣▶️9️⃣1️⃣
________________________
Mamaki ne ƙarara ya bayyana kan fuskar Sooraj, da sauri ya fito daga cikin tsibirin, yayin da ya tsinci kansa a dajin da ya ajiye motarsa. Da sauri ya nufi inda motarsa take sannan ya buɗe motar tare da saka Zahra a kujerar baya. Koma wa mazaunin driver ya yi tare da tada motat sannan ya bar harabar dajin da mugun gudu ya figi motar bai zarce ko ina ba sai hospital.
__________________
"Yanzu kenen in dai haka dawo da case ɗin mahaifin mu da miss Lailah za'a kashe mahaifin mu ne?". Cewar Ramlat wacce ke zaune kan kujera.
Girgiza mata kai Usman ya yi ya ce. "Eh za'a yi masa hukunci ne daidai da laifin da ya aikata, ai dama an ce duk abin da mutum ya shuka shi zai girba dan haka shi ma lokacin girban abin da ya shuka ne".
Khairiya wacce ta yi jugum ba ta tanka musu ba ce ta yi gyaran murya sannan ta ce. "Amma dai zamu je mu ga shari'ar da za'a yi ko?, dan ni ina son naga miss Lailah".
Murmushi Usman ya yi ya ce. "Karki da mu in sha Allah zamu je kuma za ki ganta. Yanzu dai fatana shi ne yahya Umar ya dawo gida lafiya duk da ina da saran cewa yana cikin ƙoshin lafiya, fatana ya dawo gida lafiya tare da Amrah".
Murmushi Ramlat ta yi ta ce. "Wai kun san cewa ya kira ni a ɓoye?, ya ce min yanzu haka suna garin Jigawa a gidan miss Lailah".
"What!". Usman ya faɗa sannan ya ƙara da cewa. "Yaushe haka yi hakan?, me ya sa ke kaɗai zai kira ba zai haɗa da mu ba duka?".
Dariya Ramlat ta saki sannan ta ce. "Ai ya ce so yake ya yi muku surprise, muka kasan wane abin mamakin ya ƙara faɗa min?, ya ce Amrah ba mutum ɗaya bace mutum uku ne".
Cikin rashin fahimta Usman ya ce. "Bangane ba, mutum uku kamar ya?".
Amsa Ramlat ta bashi da cewa. "Amrah ƴan uku ne kuma duk masu kammanni iri ɗaya, baka iya banbance su saboda tsananin kama ta jini, kana iya gane su ne kawai da idanuwansu tare da ɗabi'unsu. Muka duka ya faɗa min".
Kallonta Khairiya ta yi ta ce. "Abin mamaki yaushe ya faɗa miki hakan, mu kuma muna ina a lokacin?".
Amsa Ramlat ta ba ta da cewa. "A lokacin ina cikin kitchen ina girka mana abinci ku kuma kuna parlour kuna kallon film a lokacin ya kira ni ya sanar da ni".
Jinjina kai Usman da Khairiya suka yi.
_________________
A gigice nurse Nadiya ta miƙe zumbur ganin news ɗin da ake haskawa a tv. Farin ciki ne ya bayyana kan fuskar ta tamkar wacce haka yi wa albirshir da gidan aljanna.
"Na kasa yarda da hakan wai da gaske Lailah na raye?, wayyo Allah na, daɗi kashe ni, daga ƙarshe dai kin sake dawo wa, dama Allah ba azzalumin bawansa ba ne. Yanzu gashi za'a sake yin shari'ar ki da Musa, dama ai ramin ƙarya ƙurarre ne lokacin ka Musa ya riga ya ƙare, yanzu lokacin girban abin da ka shuka ne".
Tana gama faɗin hakan ta nufi hanyar ɗakin ta sannan ta ɗauko mayafin ta tare da fice wa daga gidan.
______________
Kai tsaye ɗakin ICU haka wuce da Zahra domin ceto rayuwar ta.
Babu abin da Sooraj ke faman yi sai kai kawo a cikin reception. Wayarsa ya ji tana ruri. Nan ya ciro ta daga aljihu, sunan Umar ne ya bayyana kan fuskar screen ɗin wayarsa. Da sauri ya ɗauka tare da karawa a kunnensa. "Hello". Daga ɗayan ɓangaren Umar ya ce. "Sooraj komai lafiya?, shin ka yi nasara ɗauko Zahra?".
Girgiza kai Sooraj ya yi tamkar yana gaban Umar ya ce. "Eh amma rayuwarta tana cikin hatsari, gaba ɗaya bata cikin hayyacin ta".
Jin hakan ya sa Umar shiga damuwa sannan ya ce. "Allah ya ya sa ayu nasarar cetar rayuwarta, yanzu haka ma ana shirye-shiryen dawo da shari'ar miss Lailah da mahaifina a ranar Monday. Ya kamata ka halarta".
Shiru Sooraj ya yi ya ce. "Gaskiya indai Zahra ba ta samu lafiya ba ba zan iya zuwa ba". Ya faɗa tare da ƙatse wayar.
Ganin tawowar likita hankali tashe ya sa Sooraj ya yi saurin nufar inda likitan yake ya ce. "Lafiy likita naga hankalinka a tashe?".
Amsa likitan ya bashi da cewa. "Mara lafiyar da ka kawo numfashinta na neman ɗauke wa. Kuma babu abin da take faman yi sai kiran sunan Sooraj, shin kai ne Sooraj?".
Girgiza masa kai Sooraj ya yi ya ce. "Eh ƙwarai ni ne, yanzu tana ina?".
"Tana chan ɗakin ICU".
Jin hakan ya sa Sooraj ya yi saurin nufar wajan.
Buɗe ƙofar ɗakin ya yi tare da shiga ciki. Da sauri ya maida kallonsa kan Zahra wacce babu abin take faman yi sai sunan Sooraj.
Da sauri Sooraj ya isa gare ta tare da ɗaga kanta hankali tashe ya ce. "Kina lafiya?, me ya sa me ki?, dan Allah kiyi min magana please!, wallahi idan wani abu ya same ki na gama yawo".
Shiru Zahra ta yi a sa'inda hawaye ke gangaro wa bisa fuskarta. "Kayi haƙuri ka yafe min duk abubuwan da nayi maka marasa dad'i, ina ji tamkar ba zan rayu ba, dan Allah ka kula min da mahaifiyata, kace ina ƙaunarta".
Rungume ta Sooraj ya yi tare da goge hawayensa ya ce. "Babu abin da zai same ki kinji, ki kwantar da hankalin ki, ni babu abinda ki ka yi min".
______________________
Nurse Nadiya ba ta zarce ko ina ba sai gidan miss Lailah Abdullahi. Tana zuwa ta fara ƙwanƙwasa ƙofa.
Su Aliyu da ke zaune kan kujera suna hira na yaushe gamo da miss Lailah, ya sanya su duba hanyar waje. Miƙe wa Aliyu ya yi tare da nufar hanyar gate.
Buɗe gate ɗin ya yi sannan ya dube ta ya ce. "wace ce ke?".
Ita kuwa nurse Nadiya babu abin da take sai leƙen cikin gidan ko zata hango miss Lailah. Maida kallonta ta yi kan Aliyu sannan ta ce. "Na zo wajan miss Lailah ne".
Shiru Aliyu ya yi tare da shiga cikin tunanin kamar ya san matar nan.
Dubanta ya yi ya ce. "Kamar na sanki a asibiti lokacin da muka kawo patient ko?".
Girgiza masa kai kawai nurse Nadiya ta yi ta ce. "Eh ni ce". Ita burinta kawai shi ne ta haɗu da miss Lailah.
"Shigo t.. Aliyu bai idda magana ba ya ga ta bangaje shi ta wuce cikin rawar jiki.
Sakin baki kawai Aliyu ya yi yana mai binta da kallo.
Shiga cikin parlourn gidan nurse Nadiya ta yi sallama riƙe a bakinta. Nan ta ci karo da family guda a parlour. Waige-waige ta soma yi. Chan ta hangi miss Lailah a zaune ita da su Amrah.
Nan take ta faɗi kan gwiwowinta tare da fashe wa da kuka.
_______________________
"John wai ba za ka rabu da Diana ba ne?, yarinya ta nuna ba ta sonka kai kuma ka nace". Baturen ya faɗa da yaren turanci.
Murmushin mugunta John ya yi ya ce. "Tunda ta ɗaga hannunta ta mare ni a gaban jama'a a cikin club, nima haka zan wulaƙanta ta a gaban jama'a, ba'a min na ƙyale, na rantse da yesu saina azabtar da ita".
Girgiza kai mutumin ya yi ya ce. "Ta ya ya za ka iya azabtar da ita bayan har yanzu baka san inda take ba?".
Shiru John ya yi ya ce. "Ka manta saboda ita na zo Nigeria, ai tunda na zo shi ke nen magana ta ƙare dole na nuna mata cewar ba'a min na ƙyale. Koda ƙarshen duniya zata je saina nemo ta kuma na ɗauki fansar abinda ta yi min".
_________________
Kallon su Yusrah Zubaida ta yi ta ce. "Wai ba za ku taimaka min ba wajan samun zuciyar Sooraj?".
Kallon juna su Yusrah da Samira suka yi tare da kwashe wa da dariya sannan ta ce. "Au wai ke a tunanin ki Yarima Sooraj kowace mace ce take burge shi?, ni nayi mamakin yadda ya faɗa wa soyayyar Zahra ma wallahi, yarinyar da ko girmama shi ba ya yi, ga shegen jiji da kai, ni wallahi dama ta mutu ma a inda ta je kowa ma ya huta".
______________________
Taɓa fuskarta Sooraj ya yi tare da saka ɗan yatsarta wajan hancinta. Nan take gabansa ya yanke ya faɗi!. "Zahra! Zahra! Zahr!". Sunan da yake ta furtawa kenen.
Da sauri ya fita daga cikin ɗakin tare da kiran likitoci.
Ɓangaren Zahra kuwa. Numfashinta ne ya ɗauke. Babu zato ɗakin ya fara kauraye wa da hayaki yayin da wasu halittu kyawawa mata suka soma bayyana cikin ɗakin. Zagaye Zahra suka yi sannan suka kalli juna.
"Bai kamata a ce wannan yarinyar ta mutu ba, tana da buƙatar rayuwa, ta faɗa a doguwar suma, ya kamata mu ceci rayuwarta".
Ɗaya daga cikin su ce ta ce. "Amma saboda me ya sa za mu cece ta?, ya kamata ita da kanta ta iya cetar kanta ba tare da taimakon mu ba, ita ɗin fa ba ɗaya daga cikin mu bace".