Sashe 60
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya ɗan yi shiru, sannan ya ƙara da cewa
"Sannan an kore ki daga masarautar nan Allah ya shirya ki. Kuma wannan lamarin ya ƙarfafa mana darasin cewa a cikin masarauta, adalci shi ne ginshiƙin zaman lafiya."
Sosai Zubaida ke kuka da dana sanin abinda ya aikata. Nan fadawa suka fita da ita domin yi mata bulala tamanin. Haka aka fita da ita tana birgima tana kuka.
ALƘALAMIN
A'ISHA MB
ZINARIYAR JAJIRTATTU
[8/21, 8:03 AM] AyeesherM B: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*_THREE SIBLINGS FROM DIFFERENT PART OF THE WORLD_*🫁
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*BOOK 2 PAGE1️⃣1️⃣8️⃣▶️1️⃣1️⃣9️⃣*
________________________
Bayan an tafi da Zubaida, Sarki ya rufe taron. Inda su Sooraj da Aliyu suka ɗan taɓa hira. Gefe guda kuma Amrah na tare da Zahra a garden.
Kallon Amrah Zahra ta yi ta ce. "Amrah fatan kina rayuwa cikin farin ciki".
Girgiza mata kai Amrah ta yi ta ce. "Sosai ma kuwa, ya naki gidan fatan komai lafiya".
Ajiyan zuciya Zahra ta sauke! sannan ta ce. "Toh saidai na ce Alhamdulillah".
Murmushi Amrah ta yi ta ce matso da kunnen ki kiji".
Nan Zahra ta matso da kunnen ta. Nan Amrah ta raɗa mata magana a kunne. Zaro idanuwa waje Zahra ta yi cikin farin ciki ta ce.
"Da gaske ki ke Safira tana da juna biyu kema haka?".
Gyaɗa mata kai Amrah ta yi ta ce. "Eh ko jiya munje asibiti an bani magunguna sakamakon amai da nake yi".
Washe haƙora Zahra ta yi tare da rungume ƴar uwarta ta ce. "Gaskiya na tayaku murna, Allah ya sauke ku lafiya".
"Ameen". Amrah ta amsa. Sannan ya ƙara da cewa. "Kuma yanzu Yahya Umar yana koya min karatu yana min lessons, kasancewar ba a cikin mutane na tashi ba, ban san abubuwa game da karatu ba. Hakan ya sa yake koya min harda na addini".
Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Masha Allah, su abin farin ciki ne wannan, gaskiya kin yi sa'a wallahi. Ki cigaba da maida hankali in sha Allah kema wata rana za ki san komai da komai".
Daidai lokacin su Umar da Sooraj suka fito daga part ɗin Mami suka yi sallama da sarki da sauran mutanen cikin gidan kafin daga bisani suka fito wajan parking space. Nan suka hangi su Zahra a garden. Hakan ya sa Umar ya ƙwallah wa Amrah kira.
Jin hakan da Amrah ta yi ya sa ta miƙe wa ta ce. "Bara na tafi mijina yana kira na".
Miƙe wa Zahra ta yi ta ce. "Nima yanzu zamu tafi da shi". Ta faɗa tare da riƙe hannunta sannan suka nufi wajan parking space.
Sallama suka yi da su Umar tare da musu fatan su je gida lafiya, daga bisani kowa ya kama gabansa.
Sooraj na driving ya kalli fuskar Zahra ya ga ta haɗe rai ta turo baki gaba. Bai san sanda ya kwashe da dariya ba.
Kallonsa Zahra ta yi ta ce. "Kai kuma me ka ke wa dariya?".
Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Ban san yaushe za ki daina ƙiriniya ba, me haka miki ki ka wani haɗe rai?".
Kawar da kanta ta yi ta ce. "Kai ne ka ɓata min rai".
Dubanta ya yi ya ce. "Ni kuma?, wannan karon kuma me nayi miki?".
Gyara zamanta ta yi tare da facing ɗin sa ta ce. "Yanzu fa ka duba Safira da Amrah suna da juna biyu".
Washe baki Sooraj ya yi ya ce. "Masha Allah ai abin farin ciki ne, gaskiya na tayasu murna".
Turo baki gaba Zahra ta yi ta ce. "Da a ce baka juya min baya a baya, nima na san da ina da juna biyu". Zaro ido waje Zahra ta yi jin abinda ta faɗa. Da sauri ta rufe bakin ta tare da rufe idonta. Ji take kamar ta nutse ƙasa tsabar kunya.
Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "Wato kina son Baby kenen?".
Girgiza masa kai Zahra ta yi ta ce. "A'a karka yi min gurguwar fahimta, ba abinda nake son faɗa ba kenen".
Girgiza kai Sooraj ya yi tare da riƙe hannunta ya ce. "Zahra mene a ciki dan kin faɗa min hakan, karki manta fa ni mijin ki ne, mene abun jin kunya toh".
Shiru Zahra ta yi ba tare da ta furta komai ba.
Ɗaukar hannunta ya yi tare da sawa a wajan sajen gashin sa, sannan ya ce. "Kada ki samu damuwa, za ki samu Baby, yanzu sabuwar rayuwa zamu fara, zan nuna miki soyayya iya soyayya. Kin san dai ina sonki ko".
Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Da a ce a da ne kafin na aure ka zan iya yarda, amma yanzu ko duka jiki na kunne ne ba yarda zan yi ba".
Ajiyan zuciya Sooraj ya sauke!, sannan ya ce. "Kada ki damu yanzu ma za ki dawo ki yarda ne, wallahi Zahra ina son ki, bara na faɗa miki gaskiya tun ranar da na fara ganin ki a kasuwa, kina ta masifa cewar an sace miki kuɗi, nan naga kina da yarinta da kiriniya kin shiga raina, ban taɓa ganin macen da ta shiga raina ba kamar ke Zahra amma ganin cewar kina bala'i bainar jama'a nayi ƙoƙarin dakatar da ke".
Murmushin gefen baki Zahra ta yi kamar ba ta damu ba, chan kuma cikin zuciyar kamar ta kurma ihuu saboda daɗi.
Gyaran murya ta yi ta ce "sai kuma yaushe?".
Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "Kin tuna lokacin da na ce ki zo ɗaki na har na nuna miki shaddodi a waya na ce ki zaɓar min genzna, toh a ranar so nake kawai na dinga kallonki ina jin daɗi a raina, sai kika yi abinda ya ɓata min rai na zabar min ishirinka da ki ka yi".
Nan Zahra ta kwashe da dariya ta ce. "Ai kai ne ka bani aushi ranar shi ya sa na ce saina ɓata maka rai".
Nan Zahra ta ƙara cewa. "Amma me ya sa ranar auren mu kace baka so na, saboda kar a aura maka Zubaida ya sa kace kana so na?".
Ajiyar zuciya Sooraj ya sauke! ya ce. "Wallahi ni kaina ban san me ya sa na faɗi hakan a ranar, sai bayan na faɗa ne na zo ina tunanin me ya sa nayi hakan, kuma har zuciyata ba abinda nake nufi ba kenen, abin sai ya kasance kamar wanda haka yi wa sihiri".
Ya faɗa daidai lokacin ya hangi mai balangu, hakan ya sa shi ya yi parking sannan ya siyo kaji biyu gasassu.
Nan Zahra ta washe haƙora baki har kunne. "Yau zanci kaza". Ta faɗa daidai lokacin ya shigo cikin motar yayin da ƙamshin kajin ya cika cikin motar.
Murmushi Sooraj ya yi ganin yadda take ta bin ledar hannunsa da ido.
Kallonsa ta yi ta ce. "Me ya sa ka siyo kaza kuma?".
Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "Kin manta abinda ki ka ce min ne?, kin ce kina son Baby toh yau zamu yi abinda zamu samu Baby".
Zaro ido waje Zahra ta yi ta ce. "Ni fa wasa nake, ba abinda nake nufi ba kenen".
Shiru kawai Sooraj ya yi yayin da zuciyar Zahra ya dinga buga wa. Bai kai su lokaci ba suka isa gida.
___________
Zaune suke cikin ɗaki yayin da yake riƙe da hannunta.
"Tabbas na cutar da ke a baya, lokacin da ya kamata na tsaya tare da ke ban yi hakan ba saima tafiya da nay na barki". Cewar Alhaji Abdullahi.
Murmushi Miss Lailah ta yi ta ce. "Abinda ya wuce ya riga ya wuce, sai dai mu yi fatan Allah ya tsare gaba. Kuma ai kai ma ba laifin ka ba ne ba, kaima baka da zaɓi ne kuma najin daɗin hakan ma da ta kasance. Domin da a ce hakan ba ta faru da ni ba a baya. Da ba zan san su waye maƙiya da masoyana ba. Duk da cewar a baya na nuna fushi sosai amma kuma gashi yanzu komai ya riga ya wuce".
Murmushi Alhaji Abdullahi ya yi ya ce. "Na gode sosai matata". Ya faɗa murmushi kan fuskarsa.
____________
Ɓangaren su Sooraj kuwa bayan sun shiga cikin gida kai tsaye part ɗin Zahra suka nufa. Bayan shigar su cikin ɗakin.
Sooraj ya buɗe ledar kajin da ya siyo ya jera a gabanta.
Idanun Zahra suka ƙara buɗe wa, ta turo baki gaba tana murmushi.
Murmushi Sooraj ya yi ya ce. “Yau dai sai mu yi la’asar tare da kaji mai kyau. Ni da ke kawai.”
Nan Zahra ta ce.
“Aikuwa sai na cinye gaba ɗaya ba zan bar maka ko tsokali ba.”
Sooraj ya harare ta da wasa, yana ɗora kaza a faranti. "Toh sai mu ga ta ina za ki cinye".
Nan ta kwashe da dariya, dariyarta ta cika ɗakin da annashuwa. Suka zauna suka ci tare, duk lokacin da hannunta ya bugu da nasa sai ta kalli gefe tana murmushi cikin jin kunya, shi kuma ya riƙe hannunta yana matsewa da nufin ya ƙara tabbatar mata da soyayya.
Da suka gama ci, sai shiru ya ratsa ɗakin. Iskar shiru ta haɗu da bugun zuciyar Zahra wanda take ji kamar ana kirga shi.
Sooraj ya matsa kusa da ita, ya ɗora hannunsa kan nata. Kana ya dube ta ya ce. “Zahra yau dai ki cire wannan kunyar. Ni mijinki ne, ba zan cutar da ke ba. Ki bar ni in nuna miki irin soyayyar da ta daɗe tana yi min barazana a zuciyata.”
Kallon ƙasa ta yi tana taɓa yatsunta, zuciyarta na buga wa kamar ana buga ganga. Sai ta tuna maganganun shi a mota lokacin da ya ce tun farko i ta shiga ransa.
“Ni dai gaskiya kunya nake ji, ban saba da haka ba.” ta faɗa cikin muryar ƙasa.
Nan Sooraj ya kamo fuskarta da hannunsa, idanunsa suka zuba cikin nata. “Kunya ce ke nan, amma yanzu ni mijinki ne. Zan riƙe ki kamar zinariya. Ki yarda dani Zahra, ba zan taɓa cutar da ke ba.”