Sashe 19
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai wani abu ya fado daga reshe, tsuntsu ne, amma ba na duniya ba yana da fuskar jariri da jikin kunkuru, yana kuka da sautin da bai dace da rai ba. Ya nufo ta da karfi. Amrah ta ɗan ja gefe, ta bar shi ya faɗi ya karye kamar tukunya. Ba ta ce komai ba, kuma. Ba ta firgita ba.
“Na ji labarinki,” wata murya ta fito daga ƙasa, muryar da ta zo daga cikin rana, wato daga cikin inuwa.
“Ke ce ɗaya daga cikin ƴar wadda ta karya yarjejeniya.wacce ta ɓata jinin mu.”
Amrah ta tsaya, idonta cikin duhu. Ta furta a hankali.
“bangane ba, ni fa na zo neman hujjojin na mahaifiyata ne . Kuma ba zan fita ba har saina samu, ko da kuwa zan bar wannan duniyar".
Nan take ƙasa ta fara motsi. Fuskoki suka fara fitowa daga cikin ƙasa masu ido da baki, suna ihu ba da murya ba sai da zuciya. Sun yi shela da baki marar harshen.
"Idan kika tsaya... zamu ci zuciyarki. Idan kika ci gaba... zaki fuskanci azaba da kuma ƙalubale daga wajan mu".
Amrah ta ɗago fuskarta ba don tsaro ba, don taɗa gaba ta ce.
“Gaba ɗaya rayuwarta a daji nayi shi dan aka baku isa ku bani wani tsoro ba.”
A gabanta, wata halitta ta tashi daga cikin ƙura. tana da ƙafafu huɗu, fuka-fuki biyu, da fuskar mutum mai idon toka. Tana furzar da iska mai sanyi har huhu na daskarewa. Ta nufo Amrah. Amma Amrah ba ta ja da baya ba. Dai ƙara gyara tsayuwar ta da ta yi. Duba dajin ta yi ta ce.
“Ina son ku fito dukan ku, ku gaya min inda hujjoji da dukiyoyin mahaifiyata suke.”
Nan take dajin ya amsa da ƙara mai girgiza. Nan halittu suka fara fitowa daga cikin bishiyoyi, ƙasa, inuwa. Duk suna kallon Amrah mace ɗaya da ba ta da tsoro.
Kallonta halittun suka yi sannan suka ce.
“Me ya sa ba kya da tsoro? Me ya sa ranki bai rawar jiki ba? Me ya sa zuciyarki ba ta gudu kamar sauran mutane?”
Amrah ta tsaya. Ta dube su ɗaya bayan ɗaya, idonta kamar haske ne a cikin duhu.
Sai ta furta da murya mai sanyi, amma mai ƙarfi kamar guguwa da ke fitowa daga ƙasa.
“Domin an haife ni cikin duhu, An renani da cikin daji kuma na zamto rainon dawa. Sun koya min tsayuwa a ƙafata — koda duniya ta lanƙwasa. Tsoro bai da gurin zama a zuciyar da aka gama wa tukwane da zafi.”
Ta matso gaba.
“Ku halittu masu tsoro, kun rayu da duhu. Ni kuma ina rayuwa da dalili. Na zo nan ba don rayuwa ba — amma don gaskiya. Ko da na mutu a nan, ba zan ji babu dad'i ba.”
Sai wani daga cikin halittun mafi girma, mafi duhu ya yi shiru. Idonsa ya ɗan canza, kamar yana jin wani sabon abu da bai saba gani ba.
Sai ya ce da muryar da ke firgitarwa
“Kin shude mana kamar yadda mahaifiyarki ta yi.”
Amrah ta ce
“To ku kai ni inda hujjoji suke".
Dajin ya kaɗa. Halittu suka buga kasa da ƙafafunsu, suka buɗe wata hanya da ban sannan suka ce. Ki shiga cikin wannan hanyar ki cigaba da tafiya ba zamu iya nema miki ba saidai ki nema da kanki". Suna kaiwa nan gaba ki dayansu suka ɓace.
Ɓangaren Safira kuwa,
Ta tsaya a bakin ƙofar dajin, zuciyarta tana bugawa cikin sauri. A cikin wannan daji mai cike da ababen tsoro, take jin muryoyi dake ɓoye, da kuma abubuwa marasa ganewa waɗan da ke tashi daga cikin ƙasa. Tsoron ya rufe zuciyarta, amma ta san dole ne ta shiga. Saboda ta zo neman abu mai muhimmanci ne.
Ta shiga cikin dajin, ƙafafunta suna tsalle da kankara cikin ƙasa mai dumi. Cikin kowanne mataki da ta ɗauka, zuciyarta ta yi ƙara, kamar yadda cikin duhun daji suka fara bayyana halittu masu ban tsoro. Wasu suna ɗauke da gashinsu mai tsawo wanda ke kama da zaren wutar lantarki, wasu kuwa suna da idanu masu haske kamar na wata dabba mai ban tsoro.
Nan halittun dajin suka zagaye ta, suna kallon ta da idanunsu masu ƙarfi, suna gabatar da sautin murmushi da ya ƙunshi jin haushi da tsoro. A cikin wannan yanayi mai ban tsoro, Safira ta ƙara jin wani nauyi mai tsanani a jikinta, tana jin kamar wannan daji yana ƙin karɓar ta. Duk da tsoron da ke mamaye zuciyarta, ta yi ƙoƙari ta motsa, tana ƙoƙarin yin watsi da halittun da ke ta'azzara da ita.
Nan dajin ya fara canza wa. Kowane wuri da ta shiga yana zama mai duhu da kuma cike da ƙararrawa. Halittun suna bayyana cikin yanayi mai ban mamaki wata dabba mai ɗauke da ƙafafu hudu wanda suka yi kama da na wani dabba mai hawa, wata halitta mai jiki mai fata mai launin baka, da kuma wata itace mai motsi da ta fara bayyana kamar jikin wata dabba. Safira ta tsaya, idanuwanta suna a rufe saboda jin tsoro.
Ta fara jin wani motsi a cikin jikinta, wani abu da ke cikin zuciyarta yana ba ta ƙarfin zuciya. Duk da ta tsorata, sai kuma ta tuna cewa tana da wani iko a kanta. wanda yana ba ta damar motsa abubuwa daga nesa. Nan Safira ta ɗauki wannan damar, tana mai ƙoƙarin sarrafa halittun da ke zagaye da ita. Ta ƙara amfani da wannan iko don juyar da halittun da ke ciki cikin duhun daji, suna karkatar da hankalinsu daga gare ta.
Amma wannan bai kawo karshen tsoronta ba.
Zuciyarta ta ci gaba da bugawa, amma ta ƙudurta a ranta cewa wannan hanya ba ta da dawowa bace.
Ajiyan zuciya ta sauke ganin halittun sun ɓace. Nan take ta fashe da kuka. Chan ta hangi wani dutse shi ba a ƙasa ba kuma ba'a sama.
Da sauri ta isa inda wannan dutsen yake sannan ta ce. "Dan Allah ku buɗe min hanya na koma, na fasa zuwa ni na haƙura".
Nan take wannan dutsen ya fashe da dariya sannan ya ce. "Duk wata rai da ta shigo nan ba za ta fita ba sai ta yi abin da ya kawo ta, dan aka ki cigaba da tafiya domin akwai tafiya mai tsawo yana jiranki a gaba".
Bubbuga kafarta Safira ta fara a ƙasa kamar wata yarinya ƴar shekara takwas a sa'inda ta tsungunna a kusa da dutsen ta ce. "babu inda za ni muddin baku buɗe min hanya ba.
**********
Zahra Pov.
Zahra kuwa tsintar kanta ta yi cikin dajin wanda ya cika da ganyayyaki masu aman jini.
Taɓe baki ta yi kamar ko a jikinta a cikin zuciyarta kuwa fal yake da tsoro.
Tafiya ta fara yi tana mai rera waka kamar aka. "Bana tsoron abinda zai ya dawo.
Dajin duhu ko haske, ba ni da fargaba!
Aljanu, ku zo, ku tafi, ku dawo,
Ni Zahra ce, ba na jin tsoro"
Daidai wannan lokaci wasu halittu suka bayyana matsayin gajerun mutane yayin da kansu yake tamkar ƙwallon mangwaro babu gashi ko ɗaya sai ƙyalli yake kamar silver. Nan take suka zagaye Zahra
Binsu da kallo Zahra ta yi sannan ta kwashe da dariya ta ce. "Wai wayaga bansan ana yi ba, a cikin ku da ni wa zai da ki wani, dalla malamai ku matsa na wuce kafin nayi ball da ku".
Tsaya suka yi ba tare da motsa wa ba sai faman huci suke.
Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Wato dai ba za ku matsa ba ko?, ai kuwa zan yi maganin ku".
Tana kaiwa nan ta chafki ɗaya daga cikin su sannan ta riƙe ƙansa yayin da ta wulwula hannunta ta buga masa ranƙwashi a kai. Ji ka ke. "Raƙwass!, Kwass!".
Nan take wannan halittan ya kurma ihuu. Dariya Zahra ta kwashe da shi ta ce. "Gaskiya wannan kan naka akwai dad'in ranƙwashi bara na sake. Ta faɗa tana mai ƙara masa a kan na baya.
Tana gamawa ta chafki halittar nan ta fara wujijjigashi tana jefa shi sama tamkar wani jariri. Tana faɗin. "Kamo shi nan, kamo shi nan, yaro ya ji hannu mai laushi ba kamar wanda ya saba ji ba". Ta faɗa tana mai ƙara cilla shi sama tana mai faɗin. "Lilo da dad'i yaro ya faɗo ya karye a baya". Aka ta cigaba da yi, yayin da wannan halittan da take cillawa sama ya Jigata.
Da sauri sauran halittun suka ja da baya. Yayin da mamaki ya bayyana kan fuskokin su.
ZAHRA DUNIYA CE😂😂😂
KADA KU MANTA DA LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*BOOK 2*
PAGE 7️⃣9️⃣▶️8️⃣0️⃣
_________________________
"Har ke wa ce ce da za ki maida mu abin wasa?, shin baki san ko mu ɗin su waye ba?".
Ajiye wanda take lilo da shi Zahra ta yi sannan ta dube su ta ce. "Na sani mana, baku ba ne aljanun wannan dajin ba, ai na riga na san ku ɗin ba aljanu ba ne, inda da gaske ku aljanun ne da gaske me zai sa a ce ina wasa da ɗayan ku ya kasa yin komai. Kunga dama na daɗe banyi wasa ba dan aka ku zo muyi wasan taliya, taliya, ta ta tsinke a ɗakin masoyi na kunji".
Nan take gajerun aljanun nan suka fusa ta yayin da suka fara kai mata farmaki.
Da sauri Zahra ta kauce musu cikin ranta kuwa tunani take ta inda za ta yi maganinsu.
Kallonsu ta yi ta ce. "Wai ku mene ne matsalar ku ne?".
"Kece matsalar mu, idan har baki dakatar da wannan shirmen ba kin kama gabanki to tabbas zamu koya miki hankali". Cewar ɗaya daga cikin aljanun.
Binsu Zahra ta yi da kallo daga bisani ta kwashe da wata dariya. Cikin kyakyale da dariya ta ce. "Wai ku ɗin kuma, ku dube ku fa, uban mai za ku iya tsinana wa in banda shirme, wannan katoton kawunan naku ma kaɗai ya ishe ku. Ku fara ji da matsalar ku tukun kafin ku ce za ku yi magani na".
Nan take aljanun suka dubi junansu yayin da suka girgiza kai nan take suka fara rikiɗewa izuwa halittu masu ban tsoro.