Sashe 41
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari da safe misalin ƙarfe 9:00 sarki ya nemi da a bawa Sooraj auren Zahra a wajan Alhaji Abdullahi. Sosai suka yi farin ciki da wannan tayin. Inda a ƙarshe haka saka musu ranar aure.
Yayin da Miss Lailah ta buƙaci a ɗaura wa duka ƴaƴan nata aure a rana guda tunda duk suna son juna. Kamar yadda ta buƙata haka aka yi domin su su Umar
Nan Mami ta buƙaci zata bi su Miss Lailah Jigawa domin ta taya su gyaran jiki na amarya.
JIGAWA STATE RANAR MONDAY
(KOTU)
An buɗe zaman kotu da ƙarfe 10:00 na safe. Cikin ɗakin motu shiru ne ya mamaye sararin wajan. Jama'a sun cika harabar kotu wanda suka zo ganin gaskiya zata yi halinta. An shigar da wanda ake ƙara wato Gov. Musa Muhammad cikin sarƙa an tura shi gaban alƙali.
Nan Alƙali ya ce. "Bayan sauraren lauyoyin ɓangarori biyu, bayan binciken shaidu, sannan bayan duba kwafen bayanan asibitoci, rahoton ƴan sanda, da kuma bayanan waɗan da abin ya shafa. Kotu ta tabbatar da cewa".
"Gwamna Musa Muhammad Ya aikata laifin kisan kai da gangan, bisa ga sashe na 221 na panel code ya aikata laifin satar yara da safaran su, a sashe na 274 ta ci amanar ofishi da ƙeta dokar tsaron jama'a".
Nan Alkali ya tashi tsaye cikin nutsuwa ya ce.
"Gwamna Musa Muhammad kotu ta tabbatar da cewa, ka kashe rayukan marasa laifi, ka saci yara, ka firgita zukatan iyaye da jama'a, ka wuce iyaka. Bisa laifin da aka tabbatar, da kuma tanadin doka a karkashin sashe na 221, kotu ta yanke maka hukuncin kisa ta hanyar rataya. Wannan hukunci zai kasance karatu ga duk wani mai iko ko madafa wanda ya ɗauka cewa zai wuce doka. Doka ba ya rufe ido na, za'a aiwatar maka da hukunci nan da kwanaki arba'in daga yau a filin babbar kurkuku Jigawa".
Nan ɗakin kotu ta kauraye da da muryoyin jama'a, wasu na kukan farin ciki, wasu na ihuu. Iyayen waɗan da aka zalunta na rungume juna suna murya da jin daɗin adalcin da kotu ta yi. Miss Lailah wacce haka riga aka wanke ta share ƙwalla a gefen idonta tare da kallon sama tana mai yi wa Allah godiya.
Ɓangaren Umar kuwa, tashi ya yi kawai ya bar cikin kotun. Inda polisawa suka fita da Gov. Musa Muhammad waje. Mami kuwa ta kasa furta komai domin halin da ta zo ta tarar da ɗan uwanta. Ta tausaya masa amma idan ta tuna irin mutanen da ya zalunta saita ji ranta ya ɓaci. Su Usman da su Khairiya kuwa babu abinda suke faman yi sai kuka.
Fita gaba ɗaya haka yi waje. Nan Gov. Musa ya buƙaci yana son yi wa ƴan uwansa magana na ƙarahe. Kamar yadda ya buƙata haka aka bashi dama.
Zuwa ya yi inda su Miss Lailah yake ya ce. "Yanzu idan haka kashe ni ribar me ku ka ci. Toh ku sani ba zan mutu ba domin saina ɗauki fansar abinda ku ka aikata a gare ni".
Kallonsa Mami ta yi ta ce. "Kenen ba za ka yi dana sani ba?, duk da kasancewa ta ƴar uwarka banji tausayinka ba domin kai ba abin tausayi ba ne, daidai da sau ɗaya bayan rabuwata da kai baka taɓa zuwa nema na ko ji lafiya ta ba, haka zalika nima ban damu ba domin na san tsaff ba damuwarka bace, yanzu kuma matar da ka zalunta da jama'ar da ka zalunta suna farin ciki domin sun kawo ƙarshen zaluncin ka gare su. Dole mutune su dinga yi maka tofin Allah tsine".
Karɓe maganar Alhaji Abdullahi ya yi ya ce. "Na ɗauke matsayin ɗan uwa na ba wai aboki ba, na yarda da kai, ban taɓa tunanin yin wani abu na cutarwa a gare ka ba. Amma kai saboda son abin duniya ka juya min baya, ka tozarta ni da matata tare da ahalinta a idan duniya, amma duk da abinda ka aikata mana muka ce mun yafe maka. Wannan hukuncin da kotu ta yanke maka, ba na abin da ka aikata mana ba ne, na yara ashirin da kayi silar mutuwar su ne, tare da yaran da duk ka sace ka ke safaransu. Dubi ƴaƴan ka su kansu ma ji suke dama na kai ne mahafin su ba. A lokacin baya ka raba uwa da ƴaƴanta, yanzu kuma gashi kotu kaima ta raba kai da ƴaƴanka, yanzu mene ne ribarka?".
Share hawayenta Miss Lailah ta yi ta ce. "Kayi haƙuri domin ni kaina bada son raina haka yanke maka hukuncin kisa ba, na so a ce kotu ta buƙaci ka biya diyyar waɗan da ka kashe sannan ka tuba ka koma ga Allah. Amma sai dai hukuncin kotu shi ake bi". Maida kallonta miss Lailah ta yi kan su Umar ta ce. "Dan Allah ku yafe wa mahaifin ku, sannan nima ku yafe mun, bana da san raina haka yanke masa wannan hukuncin ba".
Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "Mu ne ya kamata mu nemi yafiyar ki ba wai ke ba".
Nan take ran Gov. Musa ya ɓaci inda ya yi ƙoƙarin guda. Tare da bin kan titi. Cikin rashin sa'a kuwa babbar mota tayo kan titin yayin ta yi hawan gaba da gangar jikin sa.
Nan take hankulan jama'a ya karkata izuwa wajan, yayin da mutane suka fasa ihuu. Nan take jami'ai suka zagaye wajan. Nan take su Khairiya suka faɗi a wajan sumammu. ambulance na asibiti ne ya ƙaraso wajan. Da sauri haka ɗauki gangar jikin Gov. Musa, sannan haka wuce da shi asibiti, saidai abinda basu sani ba ya riga ya daɗe da mutuwa.
Su Khairiya kuwa yayyafa musu ruwa Umar ya yi. Nan suka farfaɗo tare da fashe wa da kuka.
Shiga cikin motoci suka yi tare da koma wa gida. Da sannu a hankali Umar ya shiga kwantar musu da hankali.
Ana haka ne haka kira Umar a waya domin ya zo ya ɗauki gawar mahaifin sa a asibiti. Nan Umar ya je yayin da haka ɗauki gawar Gov. Musa sannan haka yi mata wanka tare da sallace ta, kana daga bisani haka bunne gawar.
Bayan sadaka bakwai. Umar ya ɗauki gaba ki ɗaya abinda ya shafi dukiyar mahaifin shi ya rabar a gidan marayu, yayin da ya saida gidan da suke da zama tare da bawa iyayen wanda Gov. Musa ya zalunta. Duk wani abu da ya shafi gov. Musa, kama daga kamfanoni, motoci, gidaje, da sauransu. Duk saida ya saida su sannan ya bawa waɗan da ya zalunta. Farko basu so karɓa ba, amma ganin yadda Umar ya nace musu tare da basu haƙuri hakan ya sa suka karɓa.
Bayan nan Umar ya sa suka tare a sabon gidansa wanda ya gina da kuɗin kansa. Sannan suka fara zama a ciki.
Ɓangaren Miss Lailah kuwa ta kaiwa Hajiya Binta ziyara a kurkuku ita da Zahra. Yayin da ta saka haka yi balling ɗinta sannan ta bata sabon gida. Tare da saka Hajiya binta a matsayin manager na ɗaya daga cikin kamfanonin ta. Sosai farin ciki ya mamaye zuciyar Hajiya Binta. Inda ta shiga yi wa Miss Lailah godiya.
Ɓangaren Mk kuwa, ya buƙaci nurse Nadiya ta aure shi. Kamar yadda ya buƙata haka ta amince, inda haka shirya gaggarumar biki na buga wa a jarida. Nan Alhaji Abdullahi ya basu babban gida wanda ya cika da kayan more rayuwa sannan ya basu mota, tare da kuɗi domin gudanar da rayuwarsu.
___________
Ɓangaren su Zahra kuwa, sosai Mami ta sa hake yi musu gyaran jiki, yayin da ita ma kuma ɓangaren Zubaida hakan take domin su Gimbiya Saratu sun bazu sai mata gyara suke.
Su Sooraj gaba ɗaya sunyi order duk abinda suke da buƙata ba shirye-shiryen biki. Har izuwa wannan lokacin Aliyu da Safira basua magana kowa harkar gabansa yake, yayin da ita kuwa Safira hakan na damunta. Grandma da kuma Mom kuwa sai ɗura musu maganin mata suke. Gaba ɗaya su ukun babu wacce bata ji gyara ba.
BAYAN WATA ƊAYA DA SATI ƊAYA.
Gidan sarauta na sarkin garin Kano ya wayi gari cikin shauƙi da annashuwa. Ana ta ɗaukaka waƙa da kaɗe-kaɗe tun karfe huɗu na asuba. A rana irin wannan, gari ya kan farka kafin alfijir. Domin yau ne rana ta musamman, ranar da Yarima mai jiran gado wato Sooraj zai angwance.
Gidan sarki ya sha ado da fure masu ƙamshi, fitilu masu launi fari da launukan ado na launi zinare na alamomin sarauta.
Daga ƙofar shigo wa har bakin farfajiyar fada, an shimfiɗa tabarma na masarauta masu zanen gargajiya da tambarin gidan sarki.
An wayi gari da hayaniyar masu hidima, matan fada, dattijai, da matasa na cigaba da gyara gida.
Ɓangaren masu yiwa amare ƙwalliya, sun baza kayan ado ƙwalli, janbaki, turaren wuta, da man shafawa daga maroko.
Ɓangaren ƴan aiki an hura wuta a manyan tukwane ana dafa shinkafa, tuwon masara, miya wanda yaji naman rago da saniya, kilishi da kunun aya.
A cikin ɗaki mai ɗauke da fitilu da labulaye na alfarma, Zahra da su Safira na zaune. Gogaggun mata suna yi musu lalle wanda haka haɗa da ruwan magarya, aka zana daga tafin hannu zuwa gwiwa.
Gaba ɗaya babu abin da ke tashi a jikin su sai ƙamshi.
__
A harabar fada jama'a sun cika kama daga sarakuna daga nesa, sarkin Zazzau, sarkin katsina da mai martaba sarkin Kano. Gefe guda kuma, fitattun ƴan kasuwa da ministoci mata da maza, duk sun sha ado da babban riga, gyale da hula mai launin masarauta.
Fada sai sheƙi take ana ta kaɗe-kaɗe wanda ya haɗa da, algaita, kalangu, ganga da sarewa ana ta raye-raye.
Ɓangaren angwayen kuwa, shadda ce ta Saudiya, tare da rawani na masarsuta da takalmi masu haɗe da gold. Yayin da suka ƙaraso wajan da rakiyar manyan dodanni na fada kamarsu, gwaraza, dogarai da limamai.