Sashe 29
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Maganarta ne ya tsaya chakk sakamakon shaƙe mata wuya da Mami ta yi. Zaro idanuwa waje su Samira suka yi ganin abin da ke faruwa. Nan take suka nufo inda suke.
Babu abin da Gimbiya Saratu ke faman yi sai zazzare ido.
Cikin huci Mami ta ce. "Har ki bar duniya kada ki kuskure bakin ki ya yi ƙoƙarin furta min kalmar karuwa idan ba haka ba sai kin gane cewa Allah ɗaya ne. Wai me ya sa wanda ya fiye shiru mutane ke raina wa ne?, shiru fa ba tsoro ba ne gudun magana ce, wallahi ku bini a hankali a masarautar nan, bana son fitina, banason nayi faɗa da kowa a cikin ku, amma tunda hanyar da ku ka zaɓa kenen shi ke nen mu zuba mu gani".
Daidai lokacin sarki da fadawa ke shigo wa wajan. Ganin hakan ya sa Gimbiya Saratu ta fashe da kuka.
"Wayyo Allah zata kashe ni, wuyana na shiga uku ni saratu zan mutu, a taimake ni a kawo min agaji". Ta faɗa tana mai fashe wa da kukan munafurci.
Daidai lokacin su Zubaida ke fitowa daga ɗaki.
Kallon su sarki ya ce. "Me ke faruwa?, A'isha ya haka kuma?".
"Ranka shi daɗe kaima ka faɗa, kalli yadda ta shaƙe ni kamar ta ga wata akuya dan Allah kace ta rabu da ni". Cewar Saratu.
Kallon fadawan sarki ya yi ganin hakan ya sa suka fice daga cikin wajan.
Mami kuwa babu abin da take faman yi sai hawaye yayin take ji tamkar kirjinta zai tsage zuciyarta ta faso saboda tsananin zafi da ƙunar da take ji kan abin da su Gimbiya Saratu suke yi mata.
Kallonta sarki ya yi ya ce. "A'isha sake ta!, umarni nake baki ba shawara ba".
Sakin wuyarta Mami ta yi yayin da ta bi kowanensu da kallo. Murmushin mugunta Gimbiya Saratu ta yi sannan ta ce. "Ranka shi daɗe dama na sha faɗa maka cewar, wannan uwar gidan taka ita ce take yawan tsakano faɗa a wajan mu, yanzu ai gashi nan ka gani da idanuwanka".
Kallon Mami sarki ya yi ya ce. "A'isha kin bani mamaki matuƙa, ban taɓa tunanin hakan daga gare ki ba, kenen duk haƙurin ki na banza ne da har za ki iya shaƙe wa kishiyar ki wuya, gaskiya kin bani mamaki".
Mami kuwa ba ta san lokacin da kuka ya ci karfinta ba, nan take ta faɗi ƙasa tare da fashe wa da kuka.
"Ya Allah wane laifi na aikata da nake fuskantar irin wannan kalubalen?, wannan wace iriyar rayuwa ce wanda babu farin ciki ko kaɗan a cikin ta?, yawanci mace tana samun kwanciyar hankali a gidan auren ta amma ni in banda tashin hankali babu abin da nake fuskanta". Share hawayenta Mami ta yi sannan ta ce. "Ranka shi daɗe dan Allah ka sauwake min kawai na koma wajan yahya na".
Kallonta sarki ya yi ya ce. "Maza koma ɗakin ki, A'isha zamu yi magana daga baya".
Jin hakan ya sa ta miƙe wa tare da nufar hanyar part ɗin ta.
Ganin hakan ya sa ya dube su sannan ya ce. "Ku kuma tsayuwar me ku ke a nan?, maza kowacce ta kama gabanta yanzu". Yana kaiwa nan ya bar wajan.
Tsaki Saratu ta ja sannan ta ce. "Ai ban so haka ba wallahi, na so a ce ya sauwake mata kowa ma ya huta da wahala".
Ta faɗa tana mai nufar part ɗin ta.
_____________________
D.p.o kuwa kai tsaye gidan Radio ya nufa tare da sanar da al'ummar gari cewa za'a sake shari'ar da haka gabatar shekarun ashirin da suka wuce kan case ɗin miss Lailah Abdullahi.
Nan take gari ya ɗauka yayin da haka buga news paper yayin da ƴan jarida da tashar labarai suka shiga bayyana wa a tv cewa miss Lailah na raye.
'''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''
"Wai da gaske ki ke wannan maganar?". Cewar Hajiya Binta yayin da farin ciki ya bayyana karara kan fuskarta.
Amsa matar ta ba ta da cewa. "Eh dazu a wayar ɗaya daga cikin gandirebas ɗin da ke wajan nan naji a rediyo an faɗa, wannan ai abin farin ciki ne".
Ɗaga hannayenta Hajiya Binta ta yi sama tana mai yi wa Allah maɗaukakin sarki godiya.
"A ƙarshe dai gaskiya za ta yi halinta, asirin gov. Musa zai tonu, ya kamata nayi mai wuya domin ganin an yi bailing ɗina daga cikin wannan kurkukun".
Kallonta matar ta yi ta ce. "Wai ke mene ne ya yi silar kawo ki cikin kurkuku ne?".
Shiru Hajiya Binta ta yi tare da saukar da nannauyan ajiyan zuciya ta ce. "Labari ne mai tsawo, ina ganin babu amfani wannan tambayar domin faɗa ma ɓata lokaci ne".
Girgiza kai matar ta yi ta ce. "Ni ko ya ya ne ki faɗa min, kuma naga kina ji da wannan miss Lailah ɗin, ko dai kin san ta ne a baya kafin ki shigo wannan kurkukun?".
Murmushi Hajiya Binta ta yi sannan ta ce. "Ƙwarai da gaske na santa sosai amma saidai ita ba ta sanni ba".
"To ki gaya min labarin ki dan Allah".
Girgiza kai Hajiya Binta ta yi alamun toh.
Sannan ta fara da cewa.