Sashe 62
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da safe ya shirya, ya ɗauki motarsa ya nufi Jigawa. Cikin hawanni uku ya isa chan. A can ya tarar da Zahra tana tare da Miss Lailah suna hira. Da idanuwansa suka sauka kanta zuciyarsa ta yi wani irin bugawa.
Da sallama ya shiga, ya kalli Zahra cikin murmushi
“Zahra” ya ce da nutsuwa. “Na yi ƙoƙarin haƙuri amma wallahi na kasa. Ki shirya mu tafi gida.”
Zahra ta yi shiru, ta sunkuyar da kai. Miss Lailah ta dubi Sooraj ta ce. “Sooraj, ka bari tukunna. Tana bukatar hutu".
Sooraj ya girgiza kai, ya ce. “Umma, hutu ya isa haka. Ni ba zan iya jure wa ba, Zahra matata ce. Ina son ta dawo tare da ni yanzu.”
Miss Lailah ta yi murmushi cikin hikima, ta ce. “Toh Zahra, ki bishi. Kin san fa aure haƙƙi ne. Shi ma mijinki yana bukatar ki".
ba da son ranta ba, Zahra ta miƙe. Haka ta tattara kayanta ta bi shi, zuciyarta cike da kaɗaici, amma tana jin daɗin yadda yake nuna kulawa da kuma damuwa a gare ta.
Bayan sun gama arba’in a gidan su Mom, Safira ta koma gidan Aliyu. Shi kuwa ya cika da farin ciki da sabuwar rayuwa. Jaririya Meenal ta kasance abar shaƙuwa a wajen su duka.
Amrah ma ta dawo gida daga wajen su Mom bayan arba’in. Umar ya rungumi sabuwar rayuwarsu da farin ciki, suna tare da jaririyar su Khadijah.
Haka gidan ya cika da farin ciki, kowa na jin daɗin sabuwar ƙarni na albarka da yaran da aka samu.
ƁANGAREN MASARAUTA KUWA
A falon masarauta mai ɗauke da fitilu, an shimfiɗa tabarma irin ta sarauta, Mai Martaba ya zauna a kan kujerar zinare, gefensa kuwa akwai Mami da Gimbiya Saratu.Yayin da gefe ɗaya Junaid ke tsaye kansa a ƙasa a gabansu cikin nutsuwa da ladabi.
Mai Martaba ya gyara murya cikin izza ya ce
“Junaid, yau ka iso da magana. Mun ji cewa ka na da wanda zuciyarka ta amince da ita. Ka faɗi sunan wacce kake so a matsayin mata, domin masarauta ta san yadda za ta taya ka farin ciki.”
Saratu ta yi murmushi, Mami ta ɗaga gira tana jiran jin sunan wata gimbiya ko ƴar manya. Amma Junaid ya lumshe ido, ya saki ajiyar zuciya sannan ya ce da karfin hali.
“Mai Martaba, da izinin ku, ba wata gimbiya ce ko ƴar masarauta zuciyata ta ɗauka ba. Ramlat ce nake so. Ƙanwar Umar".
Mami ta juyo da murmushi a fuskarta, ta ce. “Junaid ɗana, ka tabbatar cewa Ramlat ita ce yarinyar da zuciyarka ta zaɓa? Kuma a ina ku ka fara haɗuwa? Ko kuwa soyayyar ku ta jima tana tafiya ne?”.
Gimbiya Saratu ma ta ƙara da dariya tana dubansa. “Yau dai gaskiya ta fito fili, ɗana ya tsinci soyayyarsa. Amma mu ji daga bakinka, ya ku ka fara?”.
Junaid ya ɗan sunkuyar da kansa cikin ladabi, murya a sanyaye ya amsa. “Mai Martaba, tun a lokacin bikin auren Yahya Umar da su Yahya Sooraj na fara ganin ta. Lokacin nan zuciyata ta tsaya a kanta, sai daga baya muka sake haɗuwa a wajen ziyara, a can muka fara fahimtar juna. Wannan soyayya ba ta yau bace, tun watannin baya take ƙara girma a cikinmu.”
Mai Martaba ya jinjina kai yana murmushi, kafin ya ce. “Da alama zuciyarka ta tabbata, idan haka ne babu abin da zai ana mu taya ka murna. Soyayya halal ce idan la yi bisa ka’ida.”
Mami ta ƙara kallon Junaid da wani kallo na uwa mai alfahari, ta ce.
“Allah ya sanya alkhairi. Na ji daɗin yadda ka fito da gaskiya. Idan har ita ka zaɓa, to mu ma mun yarda da zaɓinka".
Bayan wannan al’amari na farin ciki, su Mami da su Talatu suka nufi Jigawa gidan Umar domin su yi magana da shi kan batun neman auren Ramlat.
Umar ya tarbe su da fara’a, ya zaunar da su a cikin falonsa. Bayan an gaisa da mutunci, sai Mami ta gabatar da maganar cewa sun zo neman auren Ramlat a gare shi.
“Eh gaskiya wannan magana ta zo min da mamaki amma kuma da farin ciki. Ramlat yarinya ce mai hankali da ladabi. Sai dai ku sani tana cikin karatu, kuma bana son a katse mata hanya. In har za a bari ta cigaba da karatunta a gidan Junaid to ni na amince da wannan aure.”
Wannan maganar tasa ta ƙara faranta zuciyar su Mami, sai suka yi masa godiya sosai.
Bayan nan ne Umar ya ce. "Amma dai akwai abin da ba zan iya barin shi a gefe ba, tunda Miss Lailah ce take matsayin uwa da uba a wajen mu, dole ne a tafi gidansu a yi magana a kanta.”
Nan take suka nufi gidan Miss Lailah da kayan halatu da kayan girmamawa domin neman izinin aurar da Ramlat. Nan aka samu Miss Lailah cikin nishadi da karramawa. Da aka gabatar da maganar neman auren, sai ta yi murmushi cikin murna, ta ce. “Wannan rana kam ta zame min alheri, na ji daɗin wannan zabi da aka yi. Allah ya sanya albarka, kuma nima ba abinda zai ana ni amince wa".
Ana haka aka kira wo Ramlat wacce a halin yanzu ita da Khairiyya sun dawo gidan Miss Lailah da zama. Da aka gabatar mata da batun, ta yi shiru cikin jin kunya, ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta. A hankali ta ce. “Na amince. Allah yasa hakan ya zamo alkhairi a gare mu gaba ɗaya.”
Wannan magana ta sa suka yi shewa da farin ciki a falon. Aka rufe da addu’o’i da fatan alheri.
Bayan kwanaki kaɗan, an shirya babban taro mai ɗaukar hankali. An yi bikin Engagement ɗinsu Ramlat da Umar a cikin farin ciki da ɗumbin jama’a. An yi shagali, an yi zance, an yi dariya tare da fatan Allah ya dawwamar da soyayya a tsakanin su.
Sosai Sooraj da Zahra suka yi farin ciki da wannan Engagement ɗin da haka yi tsakanin Junaid da Ramlat.
Bayan wata uku
A cikin masarauta. Gari ya cika da shagali da farin ciki. An ɗaura auren Junaid da Ramlat a cikin babban masallacin masarautar, inda limamai da manyan malamai suka jagoranci ɗaura auren cikin tsari da daraja.
Ana gama ɗaura auren aka bazama domin gudanar da shagalin walimar aure. An ƙawata fada da fitilu masu kyalli, labulen masu launin zinare, sannan aka shimfiɗa taburmai masu ɗimbin kyau irin na sarauta. Ganguna da kakakin baka suna shela. "Masarauta ta ƙara ɗaura aure! Ɗa ga Sarauta ya samu matarsa ta gari, Allah ya albarka ce su!"
Shagalin Walima
An gabatar da rakuma da aka yi musu ado da zobba da rawani masu kyalli, aka shigar da su cikin fada a matsayin alamar alfarma. 'Yan mata masu rawa da waƙoƙi na gargajiya suna rawa cikin kida, yayin da mawaka daban-daban suka dinga rera waƙoƙin aure na yabon amarya da ango.
Umar da matarsa Amrah tare da ƴar su Kubrah wato Khadijah sun halarta cikin shigar alfarma, shi cikin babban riga da rawanin sarauta, ita cikin atamfa mai kyau da ado.
Safira da Aliyu suma sun sha ado, Aliyu cikin suit na zamani, Safira kuwa cikin shadda.
Miss Lailah wacce suka ɗauke ta matsayin uwa, ita ma ta sha ado cikin shadda mai tsada, fuskarta cike da murna tana yi wa Ramlat addu’o’i.
Mom Alhaji Abdullahi da sauran manyan dangi suma sun taru don shagalin.
An fito da amarya Ramlat, aka lulluɓe ta da ƙyallen alfarma na sarauta, ana ta busa sarewa, ana yi mata waƙoƙin yabon amarya. Fuskar ta cike da jin kunya amma tana ta annuri.
Junaid kuwa an kawo shi cikin shigar rawanin sarauta da hula mai ado da lu’u-lu’u, yana tare da abokansa da ‘yan uwa suna yi masa waka.
An yi abinci iri-iri, tuwo da miya, shinkafa jollof, kayan zaƙi, kayan sha. Kowa na dariya da murna. Aka ci aka sha aka yi rawa.
Daga baya aka shirya gasa ta rawa da kuma waƙar soyayya ta musamman don Junaid da Ramlat.
An rufe bikin da addu’ar malamai, inda aka yi fatan Allah ya albarkaci rayuwar amarya da ango. Wannan aure ya zama abin koyi da tarihi a masarautar, domin shagali da tsarinsa ya zarce dukkan auren baya.
Bayan an gama shagalin biki, sai aka tafi da Ramlat cikin jerin gwanon sarauta zuwa sabon gidanta da aka yi mata, babban gida mai faɗi, mai ƙayartarwa da ƙayataccen tsari. Gidan ya yi kama da aljannar duniya, ko wacce mace ta gani sai ta yi sha’awa.
Bayan an shigar da ita haka yi musu wa'azi sannan haka kaita ɗakinta. A nan aka zaunar da ita bisa kujera aka yi mata addu’ar samun zaman lafiya da yalwar albarka a tsakanin ta da mijinta.
Bayan nan kuwa kowa ya watse.
A masarauta kuwa Sooraj ya janye matarsa Zahra sun tafi gida ba tare da kowa ya sani ba, yayin da su Umar ma suka yi hanyar Jigawa su da su Aliyu.
Ɓangaren su Miss Lailah kuwa kwana suka yi a chan inda washe gari suka shirya wa Amarya da ango abinci suka aika musu.
Saida Miss Lailah ta yi sati ɗaya a masarauta kafin daga bisani ta yi sallama da su Mami inda mai martaba ya sa haka haɗa mata da goma na arziƙi daga bisani kuma ta tafi.
BAYAN WATA UKU DA SATI UKU.
Kwance Zahra take kan cinyar Sooraj inda suke kallon tv tare. Ɗago da kanta ta yi tare da shafa cikinta wanda ya kumburo sosai dan kamar a kowane lokaci zata iya haihuwa.
kallonsa ta yi tare da shafa gemunsa wanda suka kasance lallausa ta ce. "Habibi ni kam yaushe zan haihu ne?".
Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "Ta ya zan sani Maman Ahmad ni da ba Allah ba".
Taɓe fuska Zahra ta yi ta ce. "Ta ya ba za ka sani ba kai ba likita ba ne, kuma sannan ni na gaya maka mace nake so. Dan haka ka daina cewa Maman Ahmad, Maman Zee saka dinga faɗi kaji ni da kyau". Ta faɗa tare da jan gemunsa. Ɗan ƙara ya saki ya ce.
"Kin fara ko". Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Bani bace na ja Zee ce ta ja maka ta ga Baban ta baya jin magana".