Sashe 53
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɓangaren su Khairiyya da Ramlah kuwa, makarantar suka koma na University F.U.D inda suka cigaba da karantun su. Yayin da Usman ya tafi ƙasar waje domin ƙarasa master's ɗin sa.
__________________________
TWO WEEK'S LATER
Kano
Shigo wa Sooraj ya yi hannunsa riƙe da leda yayin da ya kira so Zubaida da Zahra izuwa parlour. Cikin mintuna ƙalilan suka hallara a parlourn.
Zama suka yi suna mai fuskantar shi. Kallonsu ya yi ya ce. "Dama na kira ki ne domin faɗa muku cewar na siya wa kowaccen ku sabuwar waya". Maida kallonsa ya yi kan Zubaida ya ce. "Zubaida za ki bani wayar hannun ki da layin da ke ciki, wannan sabuwar wayar da na siya na saka wa kowaccen ku sabon layi a ciki".
Ɓata fuska Zubaida ta yi ta ce. "Kamar ya na bada waya na da layi na?, idan ƙawayena suka kira ni baya shiga fa?, ko kuwa Babana ya kira ko aka yi min kiran gaggawa ya sanyi?".
Haɗe rai Sooraj ya yi tamkar bai taɓa dariya ba ya ce. "Wannan ba damuwata bace ba, ni ke da iko a kanki dan haka ni ke da damar yanke duk abin da na gadama, maza ki ajiye wayar ki da sim card ɗin ki".
Yamutse fuska Zubaida ta yi kamar za ta yi kuka ta ce. "Toh ita Zahra ba za ka ƙwace nata ba sai ni kaɗai ".
Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "Zahra ba ta da waya, shi ya sa ki ka ga ban tambaye ta ba".
Babu yacce Zubaida ta iya haka ta ɗauki wayarta da sim card ɗin ciki ta bawa Sooraj.
Nan ya miƙa mata sabuwar waya wacce ta kasance android Samsung Galaxy ya bata, sannan ya ɗauki iPhone 15 ya miƙa wa Zahra.
Nan take ran Zubaida ya ɓaci. Zumbur ta miƙe sannan ta ce. "Wannan ai rashin adalci ne, ya za'a yi ka siya min android phone ita kuma ka siya mata iPhone, wallahi nima iPhone ɗin nake so". Ta faɗa tare da riƙe ƙugu tamkar wacce zata yi dambe.
Ajiyar zuciya Zahra ta sauke, kana ta miƙe tsaye ta maida kallonta izuwa su biyun sannan ta dubi Sooraj ta ce. "Ni waya bata dame ni ba, saboda tunda nake ban taɓa riƙe waya nawa ba, dan haka ka bata guda biyun kawai, ita da ya dame ta sai ta riƙe. Ni yanzu ko ka bani wayar ma ban san me zan yi da ita ba".
Ta faɗa tare da kokarin koma wa part ɗin ta.
Nan ta ji muryar Sooraj daga sama ya ce. "Kada ki kuskure ki ƙara taku koda ɗaya ne". Chakk Zahra ta tsaya yayin da ta juyo kana ta maida kallonta kansa.
Haɗiye fusatar da Sooraj ya yi ya ce. "A kan me zan siyo muku abu kowaccen ku ta ce bata buƙata?, kenen ni ne wanda ban san me zan yi da kuɗi ba kenen. Ba laifin ku ba ne, laifi na ne".
Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Mai gida kenen, ai dama chan baka San abin da za ka yi da kuɗi ba, da a ce ka san mahimmancin kuɗi a yanzu dai ba za ka ɗauko mana batun waya ba, a masarauta ma'akaita nawa ne suke rasa na bawa ƴaƴansu abinda zasu da a baki?, matsayin ka na Yarima guda a gari kamata ai a ce kana taimakon mutane tare da basu sadaka, amma ni tunda na sanka ma ban taɓa ganin ka bada zakka ba, shin ka ta.......
Bata ƙarasa ba ta ji ya gauraye ta da zafafan mari har guda biyu, wanda ya sa Zahra yin mutuwar tsaye.
Nan take idanunsa suka kaɗa suka yi jajir. "Zahra ban yi niyyar marin ki ba dan dole kin san na mare ki, aikin banza kawai". Ya faɗa tare da wurga musu wayar sannan ya ce. "Idan kun gadama ku ɗauka, idan baku ɗauka na gaba ta kaini wallahi". Ya faɗa tare da shiga part ɗin sa.
Ɓangaren Zubaida kuwa sosai marin da Sooraj ya yi wa Zahra ya mata daɗi. Nan ta fara zargin cewa kamar Sooraj baya son Zahra. Ɗaukar android phone ɗin ta yi tare da barin Zahra wanda ke riƙe da ƙuncinta a tsaye. Kana ta nufi ɗaƙin ta ranta fal.
Ƙunci da baƙin ciki ne suka bi suka cunkushe guri guda a zuciyar Zahra. Share hawayenta ta yi kana ta girgiza kai ta koma part ɗin ta ba tare da ta ɗauki wayar da Sooraj ya siya ba.
Da daddare da misalin ƙarfe takwas Sooraj da Zubaida suka ci abinci a dining ba tare da Zahra ta fito ba. Shi kuwa Sooraj ko a jikinsa.
Bayan sun gama cin abinci. Kamar ance ya juya, nan ya juya ya ga wayar da ya siyo a ajiye Zahra bata ɗauka ba.
Kallon Zubaida ya yi ya ce. "Kema baki ɗauki wayar ba ko?". Girgiza masa kai Zubaida ta yi ta ce. "Na ɗauka mana, me zai ana ni ɗauka tunda na san banda wani zaɓi".
Girgiza kai ya yi kana ya nufi inda wayar take ya ɗauka sannan ya nufi part ɗin Zahra.
Shiga ya yi cikin part ɗinta nan ya ga bata cikin parlourn ta hakan ya sa shi shiga ɗakinta, nan ya ga ta duƙunƙune guri guda cikin bargo kan gado. Mamaki ne ya kama shi.
Dubanta ya yi ya ce. "Ke Zahra ki daina wannan wasan kwaikwayon ki karɓi wayarki, kinga bana son a ce mun fara samun matsala da ke".
Jin ta yi masa shiru hakan ya sa shi ajiye wayar kusa da ita sannan ya ja tsaki tare da juya wa zai fita. Nan wani zuciyar ya ce da shi kada ya fita. Dawo wa ta yi tare da taɓa ta.
Nan ta ɗago da kanta daga cikin bargon. Nan take gaban Sooraj ya yanke ya faɗi!, da sauri ya ja da baya. Take hankalin sa ya yi mugun tashi z ganin yadda fuskar Zahra ta kumbura ta yi jaa alamun kuka tayi".
Da sauri ya isa inda take sannan ya fara share mata hawayenta ya ce. "Na shiga uku dan Allah kiyi haƙuri, ni kaina bada son raina na mare ki ba, I'm so sorry please, ba zan sake marinki ba kinji".
Saurin ture hannunsa Zahra ta yi ta ce. "Kada ka ƙara taɓa ni, ka fita ka ƙyale ni, yau na gama tabbatar da maganar da ka faɗa cewar baka so na, wallahi ka bani mamaki, kuma Allah sai ya yi mana hisabi..... Da sauri ya haɗe bakinsa da nata guri guda wanda ya sanya Zahra shiru ba tsammani.
Sauri take domin ta cire bakinta daga nasa amma hakan ya citira. Nan take ta fashe da wani marayan kuka. Ganin hakan ya sa Sooraj sakin leɓenta. Riƙe leɓenta Zahra ta yi ganin yadda yake mata zafi da raɗaɗi ya sanya ta faɗi. "Allah ya isa na wallahi mugu kawai, kuma wallahi saina faɗa wa Mami abin da kayi min tun da kai ka zama abinda Malam ya ana ni faɗa".
Sooraj kuwa bai san sanda ya fashe da dariya ba ganin yadda ta jigata. Girgiza kai kawai ya yi ya ce. "Kin san Allah, idan baki min shiru ba sai na zo na yi miki abinda ya fi hakan".
Jin hakan ya sa Zahra ta yi gumm kamar mutuwa ta gifta.
Murmushi ya yi ya ce. "Good girl ashe dai kina jin magana, yanzu na gano lagwan ki, duk sanda ki ka min abu ba daidai ba ta wannan hanyar zan bi na dinga koya miki hankali".
Haɗe rai Zahra ta yi ta ce. "Ai wallahi ba isa ba, ko ka manta wacece ni?".
Murmushi Sooraj ya yi tare da ƙoƙarin yowa kanta. Ganin hakan ya sa Zahra ta buga tsalle kana ta shige banɗaki ta ƙulle. Dariya ya kwashe da shi ya ce. "Haka ce bakya ji". Ya faɗa tare da barin ɗakin.
Jin cewa ya fita ya sanya Zahra fito da daga banɗaki tana mai sauke ajiyan zuciya ta ce. "Haka kurum na zauna ka cire min leɓe ka cuce ni a banza. Ni wallahi ƙyanƙyami ma nake ji, aikin banza kawai". Ta faɗa tare da koma wa toilet ta ɗauki brush domin wanke bakinta.
__________________________
"Wai ni kamm Junaid yaushe za ka kawo min suraka gidan nan?, kai ma ya kamata a ce kayi aure fa". Cewar Mami.
Murmushi Junaid ya yi ya ce. "Mami kenen, ai ni ban shirya ba yanzu sai dai nan gaba kamm, dan yanzu wacce nake so karatu take yi, sai ta kammala tukun zan kawo ki ganta". Ya faɗa tare da miƙe wa ya ce. "Ni yanzu zan je na kwanta zuwa safiyya zamu yi magana".
"Toh mu kwana lafiya". Cewar Mami. Nan Junaid ya amsa da "Ameen".
Sannan ya fita daga cikin ɗakin ta. Shiru Mami ta ɗan yi na wasu lokacin domin a fuskar Junaid samm babu walwala ta fuskanci cewar kamar yana cikin damuwa. Basar wa ta yi kana ta fara shirye-shiryen bacci.
______
Washe Gari
Tunda gari ya waye Zubaida take ta faman amai babu gaggauta wa, inda hankalin Sooraj ya bi ya tashi. Ya yi da ita su je asibiti a duba ta, amma samm Zubaida taƙi amince wa. Ganin hakan ya sa ya buƙaci Zahra ta zo ta taimaka mata wajan gyara wa Zubaida part ɗin ta.
Girgiza kai Zahra ta yi jin wani irin rainin hankalin da haka zo mata da shi. "Lallai ma, wato ni ce zan je na gyara mata ɗakin ta, gani ƴar aiki ko?". Kallonsa ta yi ta ce. "Ai ba sunana saratu ba balle ka ce naje na gyara mata ɗaki, ita ta san me ke damunta, babu ruwa na da abin da ya shafe ta, kowa ya kama kansa".