← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 65

Sashe 43

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sooraj kuwa ɗakin shi ya shiga ya saka jallabiya tare da fito wa. Nan ya ga Zubaida ba ta ɗauki kazarta ba. Nan ya ɗauki kazar sannan ya nufi part ɗin Zubaida da shi. Ya zuwa ƙofar ɗakin ya ƙwanƙwas ƙofa.

Da sauri Zubaida ta miƙe tare da fara gyare-gyare. Nan ta ce. "Come in".

Murɗa handle ɗin ƙofar ya yi tare da shiga ciki. Nan take gabansa ya yanke ya faɗi ganin irin shigar da Zubaida ta yi. Da sauri ya juya bayansa sannan ya ce. "Maza ki nemi hijabi ki saka yanzu".

Taɓe baki Zubaida ta yi ta ce. "A kan me fa?, kai ɗin fa miji na ne, kuma ni ɗin matar ka ta sunna ce, ya za ka ce na nemi hijabi na saka a gidana kuma ɗaki na?".

Rintse idanuwansa Sooraj ya yi ya ce. "Kawai kiyi abinda na ce miki".

Tashi Zubaida ta yi. Tare da zuwa wajan wadrobe ɗinta sannan ta ɗauko maroon ɗin hijab ba dan ranta na so ba.

Saka hijabin ta yi ta ce. "Shi ke nen na saka".

Jin hakan ya sa shi juyo wa sannan ya ƙarasa ciki tare da ajiye mata kazar ya ce. "Gashi, yau a ɗakin uwar gida zan kwana gobe naki".

Nan take kishi ya mamaye zuciyar Zubaida.

"Kenen kana nufin zuwa za ka yi ka kwana da wancan ƙazamar yarinyar?".

Ɗago da kansa Sooraj ya yi a fusa ce ya ce. "Kada na sake jin irin wannan furucin ya fito daga bakin ki, wai ba ɗazu na gaya yi muku nasiha ba, bana son irin wannan Zubaida, ki kiyayi harshen ki. Na ce zan yi ƙoƙari wajan ganin na sauke nauyin ku da ke kaina, amma naga ke kamar bakya fahimta. Dan Allah Zubaida ki bani haɗin kai, bana son wani hayaniya".

Sooraj ya faɗa tare da fita daga ɗakinta.

________

Ɓangaren Umar kuwa shiga ya yi da leda ɗakin Amrah, yayin da ya sa suka ci kaza tare da yin Sallah suka yi wa Allah godiya. Nan suka yi shirin kwanciya. Ganin Umar ya kwanta kusa da ita ya kashe fitila. Ya sa Amrah ta miƙe zumbur tare da kunna fitila.

Sannan ya koma ƙasa ta kwanta.

Dubanta ya yi mamaki ƙarara kan fuskarsa ya ce. "Amrah lafiya kuwa?, ki dawo kan gado ki kwanta mana, ke ɗin fa yanzu matata ce".

Girgiza kai Amrah ta yi tare da duƙunƙune wa guri guda ta ce. "A'a ni tsoro nake ji, kai ka kwanta a nan ni zan kwanta a ƙasa".

Murmushi Umar ya yi ya ce. "Amrah kenen, matata ta kaina, karki damu kinji babu abinda zai faru".

"Ka tabbata?". Amrah ta tambaye shi.

Girgiza mata kai ta yi ya ce. "Ƙwarai kuwa, maza tawo ki kwanta".

Cikin farin ciki Amrah ta koma ta kwanta. Nan Umar ya kashe fitila tare da rungume ta.

(NI KUWA NA CE SAIDA SAFEN KU).

Ɓangaren Aliyu kuwa ledar kaza ya kaiwa Safira ɗakinta sannan ya dube ta ce. "Gashi nan ki ci kiyi wanka kiyi Sallah. Ni zan je na kwana a ɗayan ɗaki. Saida safe. Ya faɗa babu alamun fara'a a fuskarsa sannan ya shirin fita daga ɗakin.

Da sauri Safira ta miƙe tare da rungume shi ta baya kana ta fashe da matsanancin kuka.

"Dan Allah ka yafe min, wallahi ina sonka, ba zan iya juran ganin ka a cikin wannan yanayin ba, me ya sa ba za ka yafe min ba, ka maida komai ba komai ba. Kayi haƙuri dan Allah". Ta faɗa tana mai durƙusawa ƙasa ta cigaba da sharɓar kuka.

Zuciyarsa Aliyu ya ji ta karaya. Ajiyan zuciya ya sauke!, tare da ɗaga ta sama sannan ya share mata hawayenta. Murmushi ya sakar mata ya ce. "Aba Matana ya da kuka kuma a ranar aure?, karki damu na yafe miki, komai ya riga ya wuce kinji koh, Allah ya bamu zaman lafiya da haƙuri da juna. "Ya faɗa tare da rungume tare da yi mata sumbata a goshi. Nan ya zaunar da ita sannan ya fara bata kazan da kansa a baki, da ƙyar take ci saboda kunya. A haka suka ci rabin kazan tare da haɗa wa da yoghurt. Ragowar da ya rage. Aliyu ya ɗauka ya saka a freezer.

Dawo wa ya yi ya sa suka yi wanka tare da yin Sallah sannan suka yi wa Allah godiya. Daga bisani kuma suka kwanta.

___________________

Kai tsaye part ɗin Zahra Sooraj ya nufa nan yaji ƙamshi ya daki hancin shi. Lumshe idanuwansa ya yi jin yadda ƙamshin ya ratsa har cikin ƙwaƙwalar sa. Nan ya ga bata cikin parlourn ta. Hakan ya sa shi nufa kai tsaye ɗakin ta Buɗe ƙofar ɗakinta ya yi sallama riƙe a bakinsa. Nan ya sake jin wani ƙamshin na da ban ya sake dakan hancin shi. Tabbas su Mami sunyi ƙoƙari ganin Zahra ta fita kunya.

Mamaki ne ya bayyana kan fuskar sa ganin ta cinye kaza guda ta shanye yoghurt duk ta tattaune kashushuwan kazan.

Sakin baki Sooraj ya yi yana mai binta da kallo. Murza idanuwansa ya yi cikin zuciyarsa ya ce. "Ko dai imagination nake yi ne". Nan ya dai ga tabbas da gaske Zahra ta cinye kaza guda.

Kallonta ya yi ya ce. "Zahra ke da wa ku ka ci kazar nan?".

Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Kamar ya?, ni kaɗai ce mana, laifi ne dan na ci kazar amarci na?, na san in na ajiye shi ma, ƴan zuwa ganin amarya ne za su cinye, ni kuma wallahi ba zan bada ba. Ga kazar ka nan na ajiye, in ba za ka ci ba na ajiye zuwa gobe na cinye".

Girgiza kai Sooraj ya yi cikin zuciyarsa ya ce. "Tabbas da aiki a gaba na".

Maida kallonsa ya yi kanta ya ce. "Kinyi Sallah?".

Girgiza kai ta yi alamun A'a.

Nan ya sata ta yi wanka sannan suka yi alwala a tare da suka yi Sallah bayan sun iddar da Sallah suka yi wa Allah godiya.

Bayan sun gama Sooraj kalli Zahra ya ce. "Nayi farin cikin ganin ki matsayin matata ta sunna".

Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Nima kuma haka, ina farin ciki".

Ajiyan zuciya ya sauke Sooraj ya sauke ya ce. "Zahra ina son na faɗa miki wata magana".

Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Ina jin ka masoyi".

Tattaro nutsuwarsa Sooraj ya yi ya ce. "Zahra kiyi haƙuri da abinda zan faɗa miki, ni tunda nake ban taɓa jin sonki a raina ba".

Nan take murmushi kan fuskar Zahra ta gushe yayin da ta nemi walwalarta ta rasa. "Me ka ke nufi?". Zahra ta faɗa fuskarta ɗauke da damuwa.

Gyara zaman sa Sooraj ya yi ya ce. "Ƙwarai kuwa Zahra gaskiya nake faɗa miki, ban taɓa jin sonki a zuciyata ba, asali ma ni bana sonki".

"Toh me ya sa kace kana so na?". Zahra ta faɗa yayin da hawaye ya fara bin kan ƙuncinta.

Nan Sooraj ya ce. "Nayi hakan ne saboda Zubaida, a lokacin da Zubaida take nuna min cewa tana so na, na rasa yadda zan bi da ita hakan ya sa na ce ni ke nake so, a lokacin da ake ƙoƙarin ɗaura mana aure ni da ita, na fito na faɗa wa kowa ke nake so, ba wai dan ina sonki ɗin ba, saidai dan Zubaida ta ji ta fasa aure na. Duk da hakan Zubaida bata daddara ba ta cigaba da bibiyata, ni kuma na cigaba da yi kamar ina sonki. Gaba ɗaya duk abinda na faɗa miki a dajin nan, da abubuwan da ya faru har izuwa yau wanda ya kasance ranar auren mu, duk ƙarya ne. Zubaida ce ta sa nayi miki ƙarya, nace ina sonki saboda bana son a aura min ita, yanzu a ƙarshe an aura min ku biyu, bana sonta, ke ma kuma bana sonki. Na faɗa miki gaskiya ne saboda bana son na cigaba da yaudarar ki da kalaman da ba na gaskiya ba, kiyi haƙuri Zahra, na san ba za ki ji daɗi ba. Ina son wannan ya kasance sirri daga ke sai Allah. Zan kula da ke ba zan ane ki da komai ba. Bana son kiyi min mummunar fahimta".

Nan take jikin Zahra ya mutu, yayin da ta rasa me ke mata daɗi. Saurin share hawayenta ta yi. Nan ta ji tamkar an hura mata wutar tsanar Sooraj a zuciyarta.

Miƙe wa ta yi baki na rawa ta ce. "Toh yanzu me ya kawo ka ɗaki na, maza ka fita". Ta faɗa tare da nuna masa hanyar waje.

Da sauri Sooraj ya kai dubansa kan Zahra. Nan take ya zaro idanu waje ganin Zahra a halin da bai taɓa ganinta a ciki ba.

WANNAN SHI AKE KIRA CHAKWALKWALIN CHAKWAKIYA, ANA WATA GA WATA, DAMA CHAN SOORAJ BA SON ZAHRA YAKE BA. TABBAS AKWAI ƘURA. MUJE DAI ZUWA.💃💃💃💃💃💃💃💃

DAN ALLAH KUYI LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH. SABODA ALLAH PLEASE🥹 🙏🙏🙏🙏🙏🙏

ALƘALAMIN ✍️

A'ISHA M.B💞💞

ZINARIYAR JAJIRTATTU

*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎

*A'ISHA M.B*💞💞

*BOOK 2 PAGE1️⃣0️⃣8️⃣1️⃣0️⃣9️⃣*
________________________
Rintse idanunta Zahra ta yi ta ce. "Dan Allah Yahya Sooraj ka fita". Ta faɗa tare da tsugunnawa ƙasa kana ta yi ruff da ciki.

Jikin sa ne ya yi sanyi yayin da ya ji dama bai faɗa mata gaskiya ba.

Shiru ya yi na ɗan wasu lokaci kafin daga bisani ya dube ta ya ce. "Kiyi haƙuri, bana yi hakan ba ne dan na tozarta ki, nayi ne dan bana son na auri Zubaida sai kuma gashi daga ƙarshe ku biyun an ɗaura mana aure".
Chapter 43 · 0% Book details