Sashe 5
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Akwai (LAILAH INVESTMENTS) wato na zuba jari a kasuwanci ko cikin wasu kamfanoni wanda na gina a garin Jigawa".
"Na biyu (LAILAH INDUSTRIES)wato kamfanin samar da kayayyakin sawa da masana'antu, kamar su na'ura, kayan gida, da kayan masarufi shi kuma na gina a garin Kano".
na uku (LAILAH ENTERPRISES) na gudanar da daban-daban na fannin kasuwanci shima a garin Jigawa.
Sai (LAILAH VENTURES) shi ne na ƙirƙirar sabbin dama a fannonin kasuwanci kamar zuba jari, haɓaka sabbin fasahohi, ko samar da sabbin sabis shi kuma a garin Abuja".
(LAILAH GLOBAL). Yana faɗaɗa zuwa kasuwannin duniya, samar da kayayyaki ko sabis ga kasuwannin duniya, ko yin ciniki a kasashe da dama".
"In brief dai sunayen sauran sune, (LAILAH HOLDINGS) na riƙe kadarori daga wasu kamfanonin. Sai LAILAH CORPORATION, LAILAH TRADING wato na siye da siyarwa.
"( LAILAH SOLUTION). wato na warware matsalolin al'ummar muminai ga wanda basuda aikin yi tare da basu aikin da kuma biyan su kuɗi mai tsoƙa sannan na taimakon talakawa wanda ke a halin tsaka mai wuya, yayin da haka ɗauki masu aiki sama da ɗari biyu wanda suke aiki. Na ƙarshe shi ne (LAILAH GROUP)". Alhamdulillah na samu dukiyoyi marasa misaltuwa a sa'inda mutane ke tunanin ko maganin kuɗi nayi ganin lokaci ɗaya Allah ya ɗaukaka ni a duniya. Bayan kamfanonin da na buɗe na mallaki gidaje a ƙalla guda talatin da biyar, sannan na mallaki motoci sama da ashirin. Ina da gidaje na haya wanda ake wa lakabi da LAILAH HOUSES".
Yayin da Yahya na mai suna Ibrahim ya auri matarsa mai suna Zainab a shekara ta alif ɗari tara da shassa'in da biyar (1995).
Nida Abdullahi munyi auren soyayya. Farko mahaifi na bai so aurena da shi ba kasancewar ɗan siyasa, sai daga baya mahaifiyata Amina ta saka shi ya amince, bayan auren mu da shi Aliyu ya dawo wajen mu da zama sakamakon rashin haihuwa da ban samu da wuri ba. Aliyu ya na so na fiye da yadda yake ƙaunar mahaifiyarsa, nima kuma ina ƙaunarsa sama da kaina. Izuwa wannan lokaci ina da shekaru talatin a duniya, amma har izuwa wannan lokacin ban samu haihuwa ba.
"Ana tsaka da haka Musa ya zo min office ɗina tareda wasu takaddu da shi da mutanen da suke harƙallah da shi, sannan ya bani shawarar cewa na sanar da mutanen da ke ma'aikatan da ke aiki a ƙarƙashi na cewa su kawo yaransu za'a basu scholarship na karatu harda aikin yi a ƙasar waje, amma sai da sa hannu na hakan zata faru".
Jin hakan ya sani shiga cikin farin ciki mara misaltuwa ba tare da wani tunani ba na karɓi takardar sannan na saka hannu a ciki. Bayan sun tafi naje na sanar da duk ma'aikatan da ke kamfanoni na cewa su kawo ƴaƴansu an ɗauki nauyin karatun su. Cikin farin ciki mutanen da basu ji ba basu gani ba suka zo da ƴaƴan su washe garin ranar sannan a lokacin Musa ya zo da motoci suka kwashe yaran. Lokacin banyi tunanin komai a kansa ba kasancewar munyi University ɗaya da shi. A kwana a tashi ɗaya daga cikin ƴan aikin Abdullahi ya zo ya sanar da ni cewa ashe duk yaran da Musa ya saka a tafi da su ba karatu suke zuwa yi ba, yana amfani da su ne wajan yin baƙaƙen harƙallolin sa irin su karuwanci safaran miyagun ƙwayoyi, sata safaran mata. Hankali na ba ƙaramin tashi ya yi ba yayin da na sanar da mijina duk abinda ke faruwa, hakan ya sa mijina ya shiga kwantar min da hankali sannan ya ce zai sa a binciki gaskiya a kan Musa.
Naci kuka kamar ba gobe a yayin da nake jin kunyar ma'aikata na domin duk a cikin su babu wanda ya san abinda ke faruwa. Samm a lokacin ban san da wane ido zan dube su ba. Ganin ba zan iya jure wa ba hakan ya sa naje har gidan Musa sannan nayi masa gargaɗi tare da bashi umarnin cewa ya dawo da yaran da ya kwashe. A yayin da ya ce min ba zai dawo da yaran ba muddin mijina bai sauka daga kan kujerar siyasa ya bashi ba. Nan na nuna masa cewar indai kujera ce zai samu amma ya dawo da wannan yara, sannan na ce idan kuma bai dawo da wannan yara ba zan tona masa asiri.
Nan ya saki dariya sannan ya ce min nayi duk abinda na gadama.
Bayan barin gidansa da sati ɗaya ina gida haka kawo min letter na cewar inzo yanzu inga abinda ke faruwa a kamfani na. Cikin tashin hankali nida mijina muka je. Bayan mun isa chan naga abinda ya yi matuƙar tada min da hankali Nan take gaba na ya yanke ya faɗi. Wasu daga cikin yaran da Musa ya kwashe ya tafi da su ne kwance rai a hannun Allah yayin da dukansu matan suka mutu sakamakon cutar HIV/AIDS da suka kamu da shi tare da cutar Cancer.
Ɓangaren ɗaya kuma iyayensu ne ɗurƙushe suna kuka tare da dana sanin kawo yaransu.
Faɗuwa nayi kan gwiwowina ina mai fashe wa da kuka, yayin da nake ji tamkar raina zai fita. Ji nayi dama ban zo duniya ba. Duk ta dalili na waɗan mata guda ashirin da biyar suka rasa rayukansu, da a ce ban saka hannu ba da hakan ba ta kasance ba. Banyi aune ba naga ma'aikata na sun fara jifa na da duwatsuna, nan waɗan da ke bani tsaro suka shiga kare ni. Duk da hakan ban ga laifin su ba, domin gaba ɗaya laifi na ne".
"Nan mijina ya maida ni gida. Musa ya kai takardar da na saka hannu a kai na amincewar kwashe yara a tafi da su ƙasar waje zuwa kotu. hakan ya sa mutane suka yi zaton cewar ina safaran yara mata tare da miyagun laifuka. Nan take ko ina a garin ya ɗauki hakan cewar ni ɗin ina aikata miyagun laifuka hakan ya sa, katu ta bada umarnin cewa a kama ni domin yi min hukunci.
Bayan mahaifi na yaji labarin abinda ya faru ya sa shi zuwa har gida na sannan ya tsine min, yace babu ni babu shi, na janyo mana abin kunya a cikin ahalin mu, abinda nayi masa ba zai taɓa yafe min ba. A nan ne kuma ya samu ciwon hawan jini yayin da ƙafafuwan sa suka daina aiki ya koma yana zama a kan wheel chair.
"Nayi kuka sosai yayin da na rasa wa zai kaiwa kuka na, domin kuwa kowa ya guje ni. A lokacin ne na bayyana wa mijina sirrin da ban taɓa faɗawa kowa ba na cewar ina da ajiyayyun dukiyoyi cikin wani daji mai hatsari gaske kuma iya thumb print ɗina ne zai iya buɗe wa sai kuma wani abu guda ɗaya. A lokacin ban bayyana masa mene ne ɗayan matakin da zai buɗe wajan ba. Kafin nayi aune abinda na faɗa wa mijina yaje kunnen Musa. Ashe mijina da Musa bakinsu ɗaya. Nan Musa ya shiga lalube ina ne inda gaba ki ɗaya dukiyoyi na suke da takardun kamfanonin da na mallaka tare da gidaje na da motoci na.
"A lokacin na rasa inda zan saka kaina, yayin da naji kamar na kashe kaina na huta". Nan ƴan sanda suka ba zama nema na ko ina yayin da haka kafa hotuna na a yanar yaɗa labarai.
"Ina zaune nida Aliyu a parlour muka ji shigowar ƴan sanda da mijina yayin da mijina wato Abdullahi ya nuna ni sannan ya ce su kama ni su tafi da ni. Nayi mamaki sosai ganin mijina shima azzalumi ne, ban san da cewa Abdullahi zai iya butulce min ba sai a wannan rana. Nan na shiga roƙon su yayin da Aliyu ya tsaya a kusa da ni ya ce babu wanda zai tafi da ni. Nan Abdullahi ya ture Aliyu cikin rashin sa'a kan Aliyu ya bugu da bango sannan ya faɗi kan ƙarfen kujera. Nan take ya suma yayin da kansa ya fara fidda jini. Nan hankali na ya tashi yayin da suka kama ni suka saka min handcuff Aliyu kuma suka wuce da shi asibiti. Haka a gaban idanuwan mijina haka tafi da ni police station.
Ina police station naji cewar sanadiyata Aliyu ya samu cutar mantau. Nan mahaifina ya ƙara ɗora tsanar duniya ya a kaina. Nan haka yanke min hukunci kisa ta hanyar rataya. Na roƙi ƴan sanda su kaini naga iyaye na sannan na tambayi mijina a wane dalili zai ci amana ta sannan ina son naga Aliyu na nemi gafarar sa. Kamar yadda na buƙata haka ƴan sanda suka kaini wajan ƴan uwa na nan mahaifina ya kore ni sannan ya ce ayi min abinda yafi kisa idan akwai. Haka ma shiga kuka s yayin da babu wanda ya gane cewar duk sharri haka yi min sai mahaifiyata wacce ta yarda cewa ban aikata hakan ba. Nan suka kaini gidana wanda muke zaune nida Abdullahi shima muka tarar an rufe ƙarshe naji labarin cewa an siyar da gidan. Nan kuka yaci ƙarfi na ina rusa kuka na zama tamkar marainiya kowa ya guje ni, bani da wanda ya tsaya min lokacin da nake da buƙatar hakan. Nan suka kaini asibitin da haka kai Aliyu yayin da suka ce ba za su bani damar ganinsa ba. Ba yadda na iya haka suka mayar da ni police station.
**************
Hawayen da ke zubo wa kan fuskarta Zahra ta share. Yayin da su Safira, Amrah da su Umar tare da su Sooraj ke hawaye.
Buɗe page na gaba Zahra ta yi ta ga babu komai. Mamaki ne ya kamata sannan ta ce. "Me kuma ya faru a gaba?, wane ne zai bamu amsar sauran tambayoyin namu?".
Daga sama ji ance. "Ni ne nan zan baku amsar sauran tambayoyin ku". Cewar MK.
MANAGE PAGE PLS LOW BATTERY. NA GAMA TYPING WAYATA TA ƊAUKE BAN SAMU DAMAR TURA MUKU BA
ALƘALAMIN✍️
AISHA MB💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*BOOK 2*