Sashe 13
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maida kallonsa ya yi kanta sannan ya ce. "Ya kamata ki ka girman ki, wannan ba abinda ya shafe ki ba ne, wannan rayuwata ce kuma ina ƴancin yin abinda raina yake so, ni kawai na ce muku ba zan so Zubaida ba kuma ba zan aure ta ba". Ya ƙarashe maganar yana mai barin wajan sannan ya nufi part ɗin sa.
******
"Tun ɗazu muke tafiya har yanzu ban ga wata bishiyar tsamiya ba". Cewar Zahra wacce gaba ɗaya ta bi ta kiɗime.
Daga nesa su Amrah suka hangi bishiyar tsamiya sai sheƙi take tamkar gwal. Dafa Zahra Safira ta yi ta ce. "Kinga chan wajan".
Nan Zahra ta bi inda Safira ta nuna da ido. Washe baki Zahra ta yi ta ce. "Laaa aikuwa ga bishiyar tsamiyar". Ta faɗa suna mai ƙarasawa wajan.
Ganin suka yi an coka wuka a jikin bishiyar. Kallon littafin suka yi domin ganin mene ne na gaba. A cikin littafin a ka rubuta cewa. "Wacce ta fara zuwa duniya a cikin ku za ta zauna a jikin bishiyar sannan ta cire wukan jiki ta yanki hannunta jini ya zuba a jikin bishiyar".
Take gaban Zahra ya yanke ya faɗi!, Nan ta dubi Safira ta ce. "Kece ki ka fara zuwa duniya maza je kiyi abinda aka ce".
"A'a kin manta kece fa kika fara zuwa duniya dan aka maza je ki". Cewar su Safira
.
KADA KU MANTA DA LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*BOOK 2*
PAGE 7️⃣1️⃣▶️7️⃣2️⃣
******
Ajiyan zuciya Zahra ta sauke!, sannan ta ce. "Kenen dai kuna nufin ni zan je?, kuma duk abinda ya faru da ni ya faru kenen an ci banza?, dama ke Safiran nan na fuskanci cewa ba so na ki ke ba, burin ki shi ne kawai ki ga na sheƙa, to ta Allah ba ta ki ba".
Kallonta Amrah ta yi ta ce. "Kada ki damu ba dai muna nan tare da ke ba, zamu kare ki".
Jin hakan ya sa Zahra ta haɗiye yawun bakinta sannan ta miƙa wa Amrah littafin hannunta tare da nufar inda bishiyar take. Zama ta yi kan bishiyar sannan ta zaro wuƙar jikin bishiyar. Rintse idanuwanta ta yi kana ta saita wukar saitin hannunta, a hankali ta yanki kanta tana mai sakin ƙara.
Nan take su biyun suma suka saki ƙara tare.
Nan da nan jini ya fara fita daga hannun Zahra yana mai ɗiga jikin bishiyar. Take bishiyar ta fara girgiza, da sauri Zahra ta tashi daga jikin bishiyar tana mai ja da baya.
Cikin tsantsar mamaki suka ga bishiyar ta tsage gida biyu yayin da ta ƙone ƙurmus. Nan take ƙadangaru suka fara fitowa daga jikin bishiyar.
Zaro idanuwa suka yi waje suna mai ja da baya.
Da sauri Zahra ta karɓi littafin da ke hannun Amrah sannan ta duba mene ne abu na gaba.
A cikin littafin kuwa ta ga an saka. "Kada ku sake ku ji tsoro domin kuwa da raunin ku za su yi amfani, kada ku tsaya jira maza ku cigaba da tafiya".
Kallonsu Zahra ta yi ta ce. "Maza ku tawo mu cigaba da tafiya". Ta faɗa tana mai yin gaba. Ganin hakan ya sa suka yi saurin binta a baya.
Tafiya suka shiga yi ba tare da tsayawa ba. Cikin zallar gajiya Safira ta dube ta ce. "Ku tsaya mu huta wallahi na gaji gashi ina matuƙar jin yunwa sosai".
Tsayawa Zahra ta yi yayin da daga nesa suka hangi wata ƙogo mai matuƙar girman gaske. Kallon su Zahra ta yi ta ce. "Ina tunanin fa cikin ƙogon nan za mu shiga. Ku tawo mu je daga nan sai mu huta".
Girgiza kai Safira ta yi ta ce. "Gaskiya ba zan iya ƙarasa wa ba. Ciki na yana min ciwo". Ta faɗa hannunta dafe kan cikin ta. Guri ta samu a ƙasa ta zauna.
Nan take ita ma Zahra ta zauna tana mai kwanciya a ƙasa a sa'inda cikin ranta take faɗin. "Wai yaushe ne za'a mu isa inda muke son zuwa ne?, gaba ɗaya na soma gajiya". Zaro idanuwa waje ta yi kamar ta tuna da wani abu ta miƙe zumbur sannan ta maida kallonta kan hannunta. Nan take ta ga babu gurin da ta yanka ɗazu.
Mamaki ne ƙarara ya bayyana kan fuskarta. "Laa kun ga abin mamaki, inda na yanka ɗazu da wuƙa ya ɓace, ban ganshi ba, na kasa yarda da hakan".
Ba zato suka ji yo gurnanin Safira. Da sauri suka juya tare da maida dubansu kanta. Zaro idanuwa waje suka yi ganin yadda take juyi a ƙasa hannunta dafe da cikin ta. Da sauri Amrah ta isa inda take tana mai ɗaga ta ta ɗora kanta kan cinyar ta ta ce. "Ƴar uwa me ya sa me ki aka?, mene ne abin da yake damunki".
A hankali Safira ta ce. "Yunwa, yunwa nake ji sosai, ciki na yana min ciwo sosai. Bana da juriyar riƙe yunwa, please
ku taimaka min da abinda zanci".
Dariyar da Zahra ke riƙe wa ne ya subuce mata ji kake. "Hhhhhhh kyal, kyal, a'ayyee". Saida ta ƙaraci dariyar ta sannan ta ƙara da cewa. "Iya yunwa ba ta da hankali, ba ta san yaro da babba ba. Wallahi ka girma a talaka ma wani abun ne, ni da Amrah da yake mun saba da wahala ko muna jin yunwar ma zamu iya riƙe wa, amma ke aje butter ba za ki iya ba. Da ki ke cewa mu nemo miki abin da za ki ci, kinga kitchen a nan ne ko kinga gidan restaurant?, Ina ga ko akwai inda mutanen ɓoye wanda su suke ganin mu ba mu muke ganinsu ba suke saida abinci a nan sai a siyo miki".
A fusa ce Amrah ta miƙe tsaye sannan ta ce. "Wai ke me yake damunki?, samm ba ki da tausayi ne?, kina ganin ta cikin wannan halin shi ne za ki na faɗar wannan kalaman, ya kamata ki gane cewar da mu ƴan uwa ne ba maƙiya ba".
Riƙe haɓarta Zahra ta yi ta ce. "Iyyee, wato ƴar daji har ta samu bakin magana an waye za'a fara mana wa'azi".
A fusa ce Amrah ta nufi inda Zahra take tana mai gurnani.
Ganin Amrah ta nufo ta ya sa ta ƙara gyara tsayuwar ta. Amrah na isa inda take ta ƙwarfe Zahra ta faɗi ƙasa, sannan ta shaƙe mata wuya.
Kakari Zahra ta fara yi tana mai ƙoƙarin ƙwace kanta daga wajan Amrah amma hakan ya citura. Tattaro ƙarfinta ta yi tare da ture ta gefe sannan ta miƙe tsaye.
Ganin suna ƙoƙarin cigaba da fadan ne Safira ta yi saurin dakatar da su da faɗin. "Ku bari mana, sai kace ba ƴan uwa ba, Amrah ki ƙyale ta kin san dama tunda a prison ta taso dole halinta ya kasance na ƴan jagaliya".
Kallonta Zahra ta yi ta ce. "Eh gwara ni a hakan ma na fiki, keda har cikin akwati aka taɓa saka ki kina yarinya aka jefar da ke kan titi, shi ne za ki gaya min maganar banza".
Murmushi Safira ta yi ya ce. "Eh naji dai amma dai ni na samu uwa da uba waɗan da suka raine ni har izuwa girma na, sannan na samu gata iya gata, kuma bayan nan na samu ilimin boko nayi karatu, ke mene ne abin da ki ka samu in ba hauka da rashin hankali ba?, ke fa babu marabanki da masu bara a titi suna neman na abinci. wai har kura ce za ta ce da kare maye". Ta ƙarashe maganar tana mai kwashe wa da dariya.
Danne zuciyarta Zahra ta yi domin idan ta ce. "Bata ji zafin abinda Safira ta faɗa ba ta yi ƙarya. Nan take idanuwanta suka ƙada suka yi ja yayin da ta fara huci tamkar zakanya.
Cikin huci ta ce. "Ni ce babu maraba ta da waɗan da suke bara a titi?, ba laifin ki ba ne ba kinji, ki faɗi duk abin da ki ka gada ma, lokacin ki ne amma kada ki manta ki tsimayi jiran abinda ki ka aikata".
Kallonta Amrah ta yi ta ce. "Zahra kiyi haƙuri kinji". Ta faɗa tana mai riƙe hannunta.
Bin hannunta da Amrah ta riƙe ta yi yayin da take ƙara jin wani irin ɓacin rai na taso mata.
"Maza sake min hannu na".
Girgiza kai Amrah ta yi ta ce. "A'a Zahra kiyi haƙuri".
"Nace ki sake min hannu na". Ta faɗa a karo na biyu.
Ƙin sakin hannunta Amrah ta yi domin ba ta son Zahra ta tsani Safira domin kuwa ta riga ta karanci zuciyar Zahra, kuma ya cika taff da tsanar Safira a ranta.
Cikin daka tsawa ta ce. "Sake min hannu na". Da sauri Amrah ta sakar mata hannu ganin irin tsawa da walkiyar da ya wanzu a wajan.
Da sauri Amrah ta ja da baya. Miƙe wa tsaye Safira ta yi tana mai sakin baki.
Kallon juna Amrah da Safira suka yi yayin da suka maida kallonsu kan Zahra.
Ganin Amrah ta juya tana tafiya ya sa Amrah ta yi saurin bin ta tare da dakatar da ita ta hanyar zagayowa gabanta.
"A'a Zahra ki tawo mu cigaba da wannan tafiyar tare kiyi haƙuri dan Allah". Amrah ta faɗa tana mai haɗa hannayenta waje guda.
Ajiyan zuciya Zahra ta sauke sannan ta ce. "Naji shi ke nen amma bana son waccan yarinyar ta tsaya a kusa da ni".
Girgiza kai Amrah ta yi ta ce. "Tom shikenen".
Ta faɗa tana mai jan hannun Zahra suka koma inda Safira take.
Zama suka yi su ukun. Kallon su Amrah ta yi ta ce. "Bara naje na ɗan zagaya ko zan samu wani abu na kayan marmari da zamu iya ci".
Gyaɗa mata kai kawai Zahra ta yi. A sa'inda tsoron Zahra ya cikashe zuciyar Safira.
Tashi Amrah ta yi sannan ta fara ayewa kan bishiyoyi yadda ta saba a lokacin da take dajinsu. Aka ta shiga yin tsalle ɗaya bayan ɗaya tana awa kan kowace bishiya tare da tsinko mangwaro.
Kallon Zahra Safira ta yi ta ce. "Kiyi haƙuri a kan abinda na faɗa miki ɗa zu".