← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 65

Sashe 54

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Roƙon ta Sooraj ya shiga yi, yayin da Zahra ta ce wallahi ba za ta yi ba. Babu yadda ya iya haka ya haƙura ya koma part ɗin Zubaida. Kallonta ya yi nan ya ji ta bashi tausayi, ko ba komai ita ɗin ƴar ƙanin mar martaba ce. Dubanta ya yi ya ce. "Sannu kinji bari naje na kira a gida a kawo min kayan aiki na in ya so ni da kaina na duba ki".
Girgiza kai Zubaida ta yi ta ce. "A'a kada ka damu zai tsaya, na sha wani maganin tsaida amai in sha Allah zai tafi, ina tunanin abincin da na ci jiya ne ya ɓata min ciki, amma komai zai yi sauƙi".

Shiru kawai Sooraj ya yi domin baya tunanin wannan amai da Zubaida ke yi na abinci ne. Fita ya yi ya bar mata ɗakin.

Bayan fitar Sooraj Zahra ta shigo cikin ɗakin kana ta bita da kallo. Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Duniya rumfar kara, gaskiya duniya ta zo ƙarshe, wai a ce matar aure da cikin wani a jikinta ba na mijinta ba, tirrr da irin wannan ƙazamar rayuwar, ke yanzu ya za ki yi idan ya gano ina ɗauke da cikin wani a jikin ki?".

Kallonta Zubaida ta yi cikin raunatacciyar murya ta ce. "Dan Allah Zahra kada ki faɗa wa kowa please, na san ma babu wanda za ki faɗa wa".

Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Toh idan ma na faɗa ribar me hakan za ta haifar mun?, ni yanzu zuwa nayi na ɗan taimaka miki wajan ƙimtsa jikin ki, bawai da zuwa nayi na miki gyara ba, atohh dan ba ni na aike ki ba, ke ki ka kai kanki da kanki inda haka manna miki ciki, gashi an barki da wahala, shi wanda ya miki ɗin ma yana chan hankalinsa kwance. Tukun na ma wai waye ya miki wannan cikin faɗa min?".

Fashe wa da kuka Zubaida ta yi ta ce. "Wallahi ba da san raina nayi zina ba, tirsasa min a kayi, raping ɗina ya yi, gashi ya cuce ni ya gama da ni". Ta faɗa tana mai fashe wa da kuka.

Nan jikin Zahra ya yi sanyi. Dubanta ta yi ta ce. "Wane ne?, ni kuma zan taimaka miki wajan ganin an hukunta shi".

Share hawayenta Zubaida ta yi ta ce. "Shi ɗin ya kasance........ Maganarta ne ya tsaya sakamakon ringing da wayarta ke yi. Ɗaukar wayar ta yi nan ta ga number Mami a kai. Ɗaga wa ta yi tare da kara wa a kunnenta ta ce. "Hello Mami ina kwana".

Daga ɗayan ɓangaren Mami ta ce. "Lafiya kalau ƴata, yanzu Sooraj ya kira ni yake sanar min cewa wai baki da lafiya".

"Eh wallahi Mami amai nake yi tun da safe". Cewar Zubaida.

"Yanzu zan tawo in sha Allah me ki ke son na dafa miki kici?".

Girgiza kai Zubaida ta yi kamar tana gabanta ta ce. "A'a Mami ba sai kin zo na, na fara jin sauƙi kuma gashi Zahra tana tare da ni".

Nan Mami ta buƙaci Zubaida ta bawa Zahra waya. Nan ta bawa Zahra wayar yayin da suka taɓa hira kana daga bisani ta ce wa Zahra ta kular mata da Zubaida daga ƙarshe ta katse wayar.

Miƙe wa Zahra ta yi ta ce. "Bara naje na haɗa abincin karin kumallo ina nan dawo wa". Ta faɗa tare da fita daga part ɗin ta.

ALƘALAMIN
A'ISHA MB
ZINARIYAR JAJIRTATTU
[8/21, 8:03 AM] AyeesherM B: 🔥KUNDIN CINIKAYYA🌍

A’ISHA M.B 💞
BOOK 2 – Page
1️⃣1️⃣2➡️1️⃣1️⃣3️⃣

Zahra tana barin ɗakin Zubaida da niyyar had’a karin kumallo, zuciyarta cike da rudani da tausayin abinda ta ji. “Ya Allah, idan har Zubaida bata da laifi, ka bayyana gaskiya,” ta furta a hankali yayin da take tafiya.

A bangaren Sooraj kuwa, yana zaune a cikin parlour yana ɗan karanta wani rubutu akan wayarsa. Amma zuciyarsa bata zaune ba. Tunanin marin da ya yi wa Zahra ya shiga birkice masa kwakwalwa. "Ko da tayi laifi, bai kamata na mareta ba. me ya same ni haka?" Ya furta a hankali yana jin tsoron abinda zai iya biyo baya.

Zubaida na kwance a kan gado, hawaye na zubo mata. Kalmar da Zahra ta faɗa na ci gaba da ɗinbin zuciyarta – “Mutum da auren sa amma yana ɗauke da cikin shege?”

“Ya Allah, idan aka gano gaskiya me zan ce? Me zai hana su kore ni ko su...?” Ta fashe da kuka. Nan take ta yanke shawarar cewa muddin tana numfashi, dole ta nemo wanda ya ci amanarta domin ta samu mafita ko 'yanci.

Na take zuciyarta ta yanke mata hukunci
"Dole na faɗa wa Zahra komai, ita kaɗai nake jin zata iya taimaka min".

Da Zahra ta gama, ta jera abincin a faranti sannan ta nufi part ɗin Zubaida. Amma sai ta tsaya a ƙofar ɗakin kafin ta shiga.

Zubaida na jin shigowar ta ta ce cikin rauni,
“Zahra, don Allah zo ki zauna, akwai abu mai muhimmanci da nake son faɗa miki.”

Zahra ta ƙarasa cikin ɗakin a hankali, tana kallon Zubaida da idon tausayi.
“Me ke faruwa?". Zahra ta tambaya cikin dakiya.

Zubaida ta lumshe ido sannan ta ce.
“Wanda ya yi min hakan ba wani bane illa...”

Nan ta dube ta ta ce . "Wai wa?". Sai a lokacin Zahra ta lura Sooraj ya shigo cikin ɗakin. Da sauri suka basar da maganar. Kallonsu Sooraj ya yi da idon zargi ya ce. "Wai me ku ke faɗa ne?".

"Bakomai". Zahra ta furta.

WASHE GARIN RANAR .
Kai tsaye Zahra ɗakin Sooraj ta nufa domin ta gyara kasancewar jiha Mami ta faɗa mata ta yi hakan.
Dakin Sooraj tamkar dakin sarki ne, komai yalwa, tsafta, da tsari. Fararen tiles masu sheƙi, bango mai walkiya, gado mai girma da siliki, sai sanyi da ƙanshi na royal vanilla.

Zahra ta shigo a hankali hannunta rike da cleaning rag, tana sanye da doguwar riga mara ado. Fuskar ta a lumshashe cikin tunani da rashin kwanciyar hankali. Bata saba zuwa cikin ɗakin ba – sai yau. Amma zuciyarta ta cika da raɗaɗin da ba ta fahimta ba.

Tana goge mirror da nutsuwa, sai idonta ya sauka kan wayar infinix mai launi blue wayar Zubaida. Tana gefen madubi, kamar an aje ta a gaggauce.

Nan Zahra ta kalli wayar ta ce. "Kamar wayar Zubaida da Sooraj ya ƙwace". Ta tambayi kanta. Basar da wayar ta yi ta cigaba da abinda ke gabanta .

Zahra ta ci gaba da aikin, amma zuciyarta ba ta yarda ta wuce wayar haka nan ba. Bata taɓa aminta da Zubaida ba. Bata manta yadda komai ya rikice tun shigowarta ba.

Kafin ta ɗauke kai, wayar ta haska.

New Message From JUNAID

Zahra ta tsaya. Sunan da ta gani ya buɗe mata wani bargo na tambaya. Hannunta ya yi sanyi. Ta janyo wayar a hankali zuciyarta na bugawa kamar an saka mata ƙaho. Nan ta ɗauki wayar ta danna.

“Zubaida, na kai iyaka. Wannan cikin da kike ɗauke da shi nawa ne, amma ba da yardata ba. Kin cuce ni, kin saka min magani, sannan kin ƙetare iyaka da jikina. Na yi shiru har yau, amma yanzu sai na faɗa miki gaskiya,
Idan baki bar rayuwata ba, zan fallasa komai. Zan tona asirin ki a gaban duniya. Ki farka daga mafarkin ƙarya, ina da ƙarfi da gaskiya, ki ƙaurace min, ki manta da sunana saboda yanzu ke matar aure ce kuma yayana ki ka aura. Wannan shi ne farkon ƙarshe. Kar ki kuskura ki ƙalubalanci fushina".

Zahra ta runtse idonta da ƙarfi, zuciyarta ya shiga buga wa da sauri. Idonta a lumshe, numfashinta ya rikice. Wannan shine sirrin da ta ke neman fahimta tun farko. Sai kawai ta dafa bango tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi. ta maida wayar a inda ta ke kamar ba’a taɓa ta ba.

"Junaid?, ta ya ya hakan ta kasance?, dama cikin Junaid ne a jikin Zubaida, ta ya ya Sooraj zai juri hakan?, cikin ƙanninsa a jikin matarsa, wannan ba ƙaramin abu ba ne, ya zama dole na riƙe wannan sirrin". Zahra ta faɗa tare da goge message ɗin

Kamar a lokaci guda, ƙofa ta yi ƙara da sauti.

Sooraj ya shigo, yana sanye da rigar gida da after dress. Idonsa ya tsaya a kanta.

> “Zahra? Me kike yi haka kin tsaya kamar wata tsintsiya?”
“Eh... A’a. Na goge mirror ne kawai. Na ga wayar Zubaida na mayar.”
“Okay". Sooraj ya faɗa Ya ɗauki wayar ba tare da wani zargi ba, ya juyo da murmushi. Zahra ta ɗan ɗaure fuska tana ƙoƙarin daidaita numfashinta.

Sooraj ya fita, Zahra ta rufe ƙofar da hannunta, sannan ta dafe ƙirjinta. Zuciyarta tana bugawa da irin wutar da sirri ke ƙonewa da shi.

Bayan Sooraj ya fita da wayar, Zahra ta tsaya wani lokaci tana fuskantar madubi, tana kallon fuskarta da ba ta da haske. Duhu ya mamaye zuciyarta. Ta san wannan sirrin ba zata iya haɗiyewa ba.

Zuciyarta ta yanke shawarar abu daya: ta fuskanci Junaid da kanta, a gaban idonsa ta tambaye shi gaskiyar komai.

Tana jin ƙafafunta sun matse, amma zuciyarta ta ƙi juyawa. Ta ɗaura gyalen kanta, ta gyara rigarta sannan ta fita daga ɗakin Sooraj. Ba kowa a waje. Kai tsaye harabar waje ta nufa ta ga Sooraj. Alfarma ta nema tace tana son zuwa gaida Mami. Da ƙyar Sooraj ya amince inda driver ya kaita har masarautar. Nan Zahra ta sauka. Tana zuwa bakin ƙofa, ta tsaya na ɗan lokaci. Jikinta ya yi sanyi. Shiga ta yi ta tarar babu kowa a parlourn hakan ya sa ta nufi hanyar ɗakin Junaid Kai tsaye. Daidai lokacin suma su gimbiya Saratu suka ganta hakan ya sa suka bi bayanta.

Tana zuwa ga yi knocking. Junaid da ke kwance kan gado ya ji ana knocking hakan ya sa ya ce a shigo. Na ta shiga cikin.
Idon Junaid ya cika da mamakin ganin Zahra a wannan lokaci
Chapter 54 · 0% Book details