Sashe 3
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan take kidnappers ɗin suka fara dukan su Sooraj. Ganin hakan ya sa su Zahra suka saki wata iriyar razananniyar ƙara. Nan take kangon ya fara girgiza yayin da ginin ya fara rushe wa.
MANAGE PAGE PLS
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B 💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*BOOK 2*
PAGE 5️⃣9️⃣▶️6️⃣0️⃣
_______________________
Cike da tsoro kowanne a cikin su a ya ja da baya. Cikin tsantsar mamaki su Zahra suka dubi kansu.
Da sauri suka kai dubansu kan ginin wajan ganin yana ƙoƙarin faɗo musu ya sa gaba ɗaya suka ruga a guje tare da saurin fita daga cikin wajan, nan take kangon gaba ɗaya ta rushe yayin da ginin ya zama ƙasa mai laushi tamkar sahara, a sa'inda gurin ya washe tamkar ba'a taɓa gini a wajan ba.
Yarfe zufan da ke ƙeto masa Aliyu ya yi. Kallon juna Amrah da Safira suka yi, tare da kauda kai gefe.
Da sauri gov. Musa ya kira yaransa yayin da ya dubi Aliyu ya ce. "Na ɗauke ka aiki ka ci amana ta saina nuna maka cewar duk wanda ya ci amana ta to yana baƙuntar lahira ne".
Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Aliyu ya yi ya ce. "Kai a da tunanin ka ina maka aiki ne saboda kuɗi?, ko kayi tsammanin ni jami'i ne mai cin dunduniyar aikinsa da amanar sa?, ni samm ba haka nake ba, dama na kasance da kai ne domin kawo ƙarshen zaluncin ka ba wai na taimaka maka wajan cutar wasu ba".
"Kwanaki na faɗa maka cewar wani jami'i ya ceci matayen da ka sa a ayi safaran su, to ba kowa ba ne face ni ɗin nan da ɗanka Uwar, ka ɗauka bayan ka cutar da ƙanwar mahaifina Mrs Lailah sai na barka ka ƙara cutar da yaran ta, kaine kayi sanadiyar rabuwar su da mahaifyar su saboda wata banzar dukiya. Ka sa nayi kidnapping ɗin Safira da Zahra domin su je su nemo maka asalin inda dukiyar mahaifiyarsu yake, hakan ya sa nima kuma na biye maka domin ganin gudun ruwanka".
"Sakamakon ka domin Allah ba azzalumin bawansa ba ne tabbas ƙarshen ka ba zai yi kyau ba". Aliyu ya faɗa hawaye na sauka bisa fuskarsa.
Nan take tausayinsa ya kama kowanensu harda ma Safira wacce ta tsaya tana nadamar maganganu mara daɗi da ta faɗa mishi".
Girgiza kai gov. Musa ya yi ya ce. "Ba zan rabu da ku ba, sai kun gane wane ne ni, Umar kada ka biye musu tawo mu koma gida kaji".
Girgiza masa kai Umar ya yi ya ce. "Ba zan koma gidan ka ba, na tsane ka Abbah, me ya sa ka zaɓi zama cikin irin wannan ƙazamar rayuwar wacce bata da fa'ida?, ya kamata a ce ka zubar da komai, kamata ai a ce ka tuna da cewar mutuwa a koda yaushe zata iya riske ka, ya kamata ka shuka alkhairy kafin ka mutu, Abba ka tuba dan Allah".
Tsaki Abba ya ja!, sannan ya ce. "Kaima sun hure ma kunne ko, kaje zamu gani". Ya faɗa tare da shiga cikin motarsa yayin da kidnappers ɗin suka mara masa baya tare da barin harabar dajin.
"Wai ina Mk ne?, naga duk mun cika amma banda shi". Cewar Sooraj
"Oho waya sani, ya ga abinda ya fi karfin sa ne, ya sa ya fece".
sannan ta ƙara da cewa. "Yau naga abinda yafi ƙarfin kaina, ohh Allah mai iko, ya nake jin sunan da suke ambata sak irin na mahaifiyata, koda yake ma ai mamata ta daɗe da rasuwa. Na so tana raye domin ta ga yau na haɗu da masu kama da ni, ga gini ya rushe daga ihuun mu, me yake faruwa ne, ni samm bana fahimtar komai"".
Kallon Aliyu Safira ta yi cikin nadama ta ce. "Kayi haƙuri yahya Aliyu, nayi maka kuskuren fahimta ne, samm ban kyauta maka ba dan Allah ka gafarce ni". Ta faɗa tana mai fashe wa da kuka.
Ganin hakan ya sa Aliyu ya ƙarasa inda take tare da rungume ta sannan ya fara rarrashin ta.
Da ido Zahra ta bisu da shi tare da taɓe baki. Maida kallonsa Umar ya yi kan Amrah sannan ya ce. "Amrah naji ɗazu lokacin da muke wajan masu kidnappers kika ce Babana ne ya kashe Mamata ta ya ya ki ka san da cewa mahaifina shi ne wanda ya kashe mahaifiyata?".
Murmushi Amrah ta sakar masa sannan ta ce. "Ni ɗin ina iya karanta mutum sannan ina iya karantar abinda ke cikin zuciyarsa, da kuma abinda yake tunani ko kuma abinda ya aikata a baya".
Zaro idanuwa gaba ki ɗaya suka yi.
"Kaiiiiiii! Kaiiii!, kaiii!, chabb wa ya ga zuƙi ta malle, wannan ƙaryar ba zata yi alwala ba balle Sallah". Cewar Zahra da ke zaune ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Nan take hankulansu ya garzaya izuwa kanta.
Kallonsu ta yi ta ce. "Ya za ku wani bi ni da ido sai kace kunga wani abun al'ajabin?, ko naci wani abu ne ban baku ba?. Ku baku ji ƙaryar da wannan mai karen idanuwan take faɗi ba ne, wai tana karantar zuciyar mutum". Ta faɗa tana mai bushe wa da dariya.
Kallonta Umar ya yi ya ce. "Maganar ki gaskiya ce, babu ta inda hankali zai ɗau abinda Amrah ta faɗa".
Girgiza kai Amrah ta yi ta ce. "Ku yarda da ni tabbas gaskiya nake faɗa muku, idan baku yarda ba ku faɗa min me zan yi domin ku tabbatar?".
Miƙe wa tsaye Zahra ta yi tare da karkaɗe jikinta sannan ta ce. "Ni ce nan zan ƙure ƙaryar ki. Zan faɗi abu yanzu a zuciyata idan kin sa ki faɗa".
Girgiza kai Amrah ta yi ta ce. "Shi ke nen faɗi".
Kawar da kai gefe Zahra ta yi cikin zuciyarta ta ce. "Ni wallahi ma kashi nake ji sosai ya matse ni".
Dariya Amrah ta saki da shi sannan ta ce. "Haka ki ka ce kashi ki ke ji sosai kuma ya matse ki".
Nan take kunya ta kama Zahra. Dariya Sooraj da su Umar suka kwashe da shi.
Takaici ne ya kama Zahra ta ce. "Ƙarya ki ke ba haka na ce ba, haka na ce idanuwanki koraye tamkar koren ganye".
Girgiza kai Amrah ta yi sannan ta ce. "A'a ba haka ki ka ce ba, ki faɗi gaskiya".
Cikin fusata Zahra ta ce. "To sai me?, wane ne baya kashin?, ko ku nan za ku ce bakwayin kashin?, ta ya ya ma ki ka samu wannan baiwar?".
Amsa Amrah ta bata da cewa. "Nima ban sani ba".
Ɗaga hannu Safira ta yi ta ce. "Nima ina da baiwa wanda ban taɓa sanar wa da kowa ba".
Nan take kowanensu ya nutsu domin jin mene ne baiwar Safira.
Gyaran murya Safira ta yi ta ce. "Baiwa ta ita ce ina iya yin numfashi a cikin ruwa, sannan zan iya zama a nan wajan abu yana nesa da ni kuma na janyo abun ba tare da na tashi ba".
Ajiyan zuciya gaba ɗaya suka sauke!, kallon Zahra Sooraj ya yi ya ce. "To ke mene ne baiwar ta ki?".
Kallon kanta Zahra ta yi ta ce. "Ni?, ni ina da wani baiwa ne?. To ni dai baiwa ta bai wuce duk wanda ya nuna min shi jan wuya ne ina nuna masa ni gyatumar masa ce a janwuyanci, sannan bana ɗaukar raini ko shashanci, ina da neman tsokana sannan duk inda naga anyi ba daidai ba ina kokari wajan saita wajan. Karin daɗi kuma duk wanda ya taɓa ni ya tarowa kansa match domin ya ɗora ruwan dafa kansa ne". Wannan shi ne baiwa ta.
Taɓe baki gaba ɗaya suka yi, yayin da Aliyu ya ce. "Dama baiwar ki ba ta wuce ta rashin kunya ba".
Harara Zahra ta galla masa ta ce. "Malam ɗan sanda ka fita idona na rufe, zan maka rashin mutunci idan baka kiyaye ni ba".
Yatsune fuska Safira ta yi ta ce. "Excuse me, maintain your word's please, you can't just be talking to my boyfriend like that. Mind your word's please".
"Hahahaha!". Zahra ta kwashe da dariya tana mai yi tana mai tafa hannu. Binta gaba ɗaya suka yi da kallo.
Kallon Safira ta yi ta ce. "Inda ranka zaka sha kallo, mutum ba ɗan kowa ba amma sai ya nuna shi ɗan wani ne, wai ta ya ma haka yi muke kama da ku?, banso hakan ta kasance ba. Wa za ki zo kiyi wa waɗan nan ƙazaman turancin naki, kinzo kina tuta baki gaba sai kace wata agwagwa. To ki tsaya a matsayin ki, ni bana son gutsiri tsoma, idan ban tsoma mutum a magana ta ba, bana son yana sako kan shi ciki".
Nufar inda Zahra take ta yi tare da nuna ta tace. "Ke a wa za ki ce min kada na sa baki?".
Amsa Zahra ta bata da cewa. "Ni a matsayin Auntyn ki, wai ba na ce idan manya na magana yara su daina da baki ba?".
"Wace ce babbar a nan?". Safira ta tambaya.
Amsa Zahra ta bata da cewa. "Ni mana. Kinga malama baturiya mai turancin Abcd, ya kamata ki nutsu. Kuma ya kamata ki sauke hannun da ki ke nuna ni da shi danni banƙi na ɓalla hannun ba".
Girgiza kai Safira ta yi cikin takama da girman kai ta ce. "Hey you stinky poor girl. Idan har kina takama da abinda ki ke ji da shi nafi yafi naki".
Murmushi Zahra ta yi sannan ta ce. "Ai naki ba zai taɓa fin nawa ba domin kuwa aljanu casa'in da tara ne a kaina, kuma da zarar ɗaya ya tashi sai ya nakaɗa miki na jaki wanda ba za ki iya bambance wa shin a duniyar mutane ki ke ko na matattu".
"Wai dan Allah mene haka ku ke yi?, wannan samm ba girman ku ba ne ba, kuda ku ke kama da juna maimakon kuyi farin ciki amma shi ne za ku tsaya kuna musayar yawu da juna". Cewar Umar.
"Allah ya kiyaye, ni samm bana son ganinta ma domin ganinta ma tashin zuciya yake sanya ni, ni da zan zamu wanda zai chanza min fuska ma da gudu zanje domin banason ganin wannan banzar fuskar tata".