Sashe 27
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
KADA KU MANTA DA LIKE, COMMENTS, AND SHARE FISABILILLAH 🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
بسم الله الرحمن الحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎
*BOOK 2 PAGE8️⃣6️⃣▶️8️⃣7️⃣
***************
Huci Zahra ta soma yi yayin da ta fara waige-waige. Cikin rashin sa'a ta ji sun saka mata sarƙa a jikin ta wanda ya ɗauki matuƙar zafi. Ba ta san lokacin da ta kurma ihuu wanda saida gaba ki ɗaya ilahirin wajan ya amsa.
Ƙara!, ta sake ƙwallah wa a karo mara adadi. Nan take ta faɗi ƙasa yayin da idanuwanta suka soma rufe wa.
Basu yi aune ba su ka ga an fara wani iska mai haɗe da guguwa a yayin da guguwar nan ta cire sarkar da suka saka wa Zahra.
Nan take guguwar nan ta soma wujijjiga waɗan nan halittun ganin wannan guguwar na shirin hallakar da su ya sa su gaba ɗaya suka ɓace daga wajan.
Zahra kuwa ta soma fita daga cikin hayyacin ta, a sa'inda numfashi yake barazanar ɗauke wa.
"Ya Allah!". Zahra ta furta murya a rauna ce.
******
"Me ke faruwa haka?, me ya sa me ku kuma?". Cewar Mom
Rirrike jikinta Safira ta yi tana faɗin. "Jiki na yana ɗaukar zafi, ina ji tamkar ana ƙona ni da wuta, dan Allah ku zuba min ruwa a jiki na".
Kamar yadda Safira ke fama da raɗaɗi, haka ita ma Amrah domin gaba ɗaya suke jin wannan zafin.
Kallonsu Mrs Lailah ta yi ta ce. "Tabbas akwai abin da ke faruwa da ƴar uwar ku, hakan ya sa ku ke jin zafin abin da ita ma take ji a chan. Idan haka ne to tabbas rayuwar ƴar uwar ku na cikin hatsari. Ya Allah ka kare su gaba ɗaya, ka duba waɗan nan bayi naka, ka sassauta musu raɗaɗi da zafin da suke ji". Mrs Lailah ta faɗa hannayenta a sama.
*********
Sooraj kuwa, tafiya ya shiga yi ba tare da ya yi harba da komai ba. Babu abin da yake ji sai zallar kukan tsuntsaye.
Chan ya hangi dutse mai zaman kanta. Saidai abin da ya yi matuƙar ɗaga masa hankali shi ne ganin dutsen na zubda hawaye.
Tsoro ne ya bi ya mamaye zuciyarsa. Amma lokaci ɗaya wannan tsoron ya gushe daga zuciyarsa kasancewar ya tuna cewa rayuwar Zahra ya zo ce ta.
Inda wannan dutsen yake ya nufa sannan cikin ransa ya ce. "Allah mai iko, tunda nake ban taɓa tunanin ganin irin wannan koda kuwa a mafarki ne ba, gashi yanzu na rasa ta ina ne zan samu Zahra
Ya Allah ka kawo mana agaji baki ɗaya". Sauke ajiyan zuciya ya yi yayin da ya yinkura domin cigaba da magana.
Kamar a mafarki ya tsinci muryar dutse na faɗin. "Ka dawo gare ni ni nan zan taimaka maka, na san wacce ka zo nema".
Zaro idanuwa waje Sooraj ya yi ganin abin al'ajabi da ya wanzu a daidai wannan lokaci.
Nan take hankalin shi ya tashi yayin da ya gigice tamkar ya nutse a ƙasa saboda tsananin tashin hankali da ya shiga. Nan take ya soma haɗa zufa tamkar ana kwarara masa ruwan zafi.
A karo na biyu dutsen ya ƙara cewa. "Ka dawo gare ni, ni nan zan taimaka maka, kada ka ji tsoro na, ni bana cutarwa".
Haɗiyan yawun tsoro Sooraj ya yi. A wannan karan kuwa ya gama sallame wa cewar tashi ta zo ƙarshe.
Matsa wa ya yi kusa da dutsen sannan ya ce. "Dama dutse ya magana ne?".
Girgiza jikinsa dutsen ya yi wanda ya sa Sooraj ya yi saurin ja da baya.
"Kada ka tsorata, tabbas ina magana domin ni ba irin dutsen da ka saba gani ko ka saba ji ba ne, ni bana sawun irin waɗan nan dutsen, ni mai magana ne kuma mai ceto, ni ɗin asali ba dutse ba ne, maida ni hakan haka yi shi ya sa nake iya yi wa bil adama magana. Na riga na faɗa maka cewar kada ka tsorata domin bana son idan mutum ya ji ina magana ya tsorata. Yanzu maza ka tura ni izuwa hanyar dama ka cigaba da tafiya, zan taimaka maka wajan nuna maka inda wacce ka zo nema take".
Shiru Sooraj ya yi na ɗan wasy lokuta yayin da ya dubi dutsen ya ce. "Ta ya ya zan iya tura ka, ba ka ga kalar girman ka ba ne?, gaskiya ba zan iya tura ka ba".
Girgiza jikinsa dutsen ya sake yi ya ce. "Na san za ka iya, kana jin tsoron abin da zai je ya dawo hakan ya sa ka ce ba za ka iya tura ni ba, amma tabbas za ka iya".
Furzar da iska mai zagi Sooraj ya yi waje ya ce. "Shi ke nen naji".
Ya faɗa yana mai zuwa daff da dutsen. Ajiyan zuciya ya sauke!, tare da rintse idanuwansa ya yi wanda suka bayyana tsoro ƙarara sannan ya ɗora hannayensa a kan wannan dutsen.
Babu ɓa ta lokaci ya soma tura wannan dutsen izuwa hanyar dama kamar yadda dutsen ya ambata.
Tura shi ya shiga yi da ita ƙarfin saida ya zo daff bakin ruwa sannan ya tsagaita da turawa.
Kallon dutsen ya yi ya ce. "Gashi nan dai na kawo ka wajan nan naga babu hanya sai ruwa da bishiyoyi, naga kuma wannan ruwan kasu gida uku kuwa color uku".
Girgiza jikinsa dutsen ya yi alamun ya ji abinda Sooraj ya ce. Sannan ya ce. "Eh za ka ga wacce take da launin baƙi, to ita za ka shiga, a nan ne wacce ka zo nema take".
Girgiza kansa Sooraj ya yi cikin ransa ya ce. "Ita ma Zahra in banda abin ta ga ruwa fari da ja amma ta rasa wanne za ta shiga sai baƙi".
Girgiza jikinsa dutsen ya yi alamun ya ji duk abin da Sooraj ya faɗa a ransa. Hakan ya sa shi faɗin. "Dama haka ƙaddararta take, haka kuma yake a rubuce. Shi ya sa ta shiga wannan baƙin, kuma tabbas tana sane ta yi hakan, domin ta ceci sauran ƴan uwan nata".
Cikin rashin fahimta, Sooraj ya ce. "Bangane ba, ka fahimtar da ni, ta ya ya zai kasance tana sane?, ta san zai cutar da ita kuma za ta shiga?".
Girgiza jikinsa dutsen ya yi ya ce. "Ƙwarai da gaske duk abin da take yi tana sane, kuma ta riga ta san wannan baƙin ruwan na mutuwa ne, hakan ya sa ta shiga ciki domin cetan sauran ƴan uwanta, sannan kuma ta riga ta san cewar ita ce za ta mutu tun farkon shigowar su wannan tsibirin. Ta yi jihadi kuma ta yi babbar sadaukarwar da ba kowane ɗan uwa na jini ne zai iya yin hakan ba, ta yarda ta bada rayuwarta domin cetan ta sauran, shin akwai sadaukarwar da ta kai wannan?".
Nan take idanuwan Sooraj suka ciko da hawaye cikin tausaya wa Zahra ya ce. "Allah sarki, amma ta ya ita ita yin hakan, ta ya ya ta san cewar baƙin ruwan na mutuwa ne?".
Amsa dutsen ya ba sa da cewa. "Saboda tana ɗauke da baiwar da ba kowane mutum a duniya yake da irin wannan baiwar ba, ta ɗauke da baiwar ƙarfi da iko wanda ko da aljanu guda ɗari za'a tara basu da shi, baiwar ta ya fi tunanin mai tunani, ta samu wannan baiwar ne a ranar da ta fara shakar iskar duniya, wato lokacin da ta zo duniya".
Nannauyan ajiyan zuciya Sooraj ya yi ya ce. " tana da irin wannan baiwar, me ya sa ta kasa cetar kanta?".
Amsa dutsen ya basa da cewar. "Domin baiwar ta ba'a koda yaushe yake tashi ba, ita kanta ba ta san tana da wannan baiwa ba hakan ya sa ba ta iya cetar kanta ba".
Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Shi ke nen ni nan zan shiga in ceto ta". Ya faɗa tare da faɗa wa cikin wannan ruwa".
__________
Kwantar da su Mrs Lailah ta yi kan kujera, lokaci ɗaya su Safira suka nemi zafin da suke ji suka rasa.
Miƙe wa Safira ta yi ta ce. "Mama kinga na daina jun zafin komai, kenen hakan yana nufin ita ma Zahra ta kuɓuta daga cikin wannan hatsarin da take ciki?".
Shiru Mrs Lailah ta yi na ɗan wasu lokuta sannan ta ce. "Allah shi ne masani".
Kallonsu gaba ɗaya Aliyu ya yi ya ce. "Yanzu ya ci a ce mu harhaɗa hujjoji mun tafi kotu domin kotu ta yanke ranar da za'a ƙara zama na shari'a domin yanke wa gov. Musa hukunci".
Ya faɗa tare da kallon Umar sannan ya ce. "Kayi haƙuri Umar, na san da cewa shi ɗin mahaifin ka ne, kuma abin da ƙuna, babu yadda muka iya ne shi ya sa ka ga ina hakan. Ya zama na cewa ba za mu iya yafe masa ba domin ya tarwatsa ahalin da suke cikin farin ya raba su na tsawon shekara da shekaru sannan ya ɓata mana suna. Hakan ne ya sa muka ce ba za mu bari abin da ya yi ya tafi a banza ba".
Murmushi Umar ya yi ya ce. "Tabbas kayi gaskiya, dole naji babu dad'i, amma ai duk rashin jin dad'i da zan ji ba zai kai wanda ku ka ji ba lokacin da ya lalata sunan ahalin ku, ni kaina na san shi ne wanda ya kashe min mahaifiya saboda san zuciya da son abin duniya irin nashi, kada kuyi duba da kasancewa ta ɗan sa, ni ba kamar shi nake ba, bani da muttacciyar zuciya irin nasa, kuna da damar yin duk abin da ku ke so ba zan ji komai ba, suma kuma ƙanne na na san za su fahimta".
Kallon sa Mrs Lailah ta yi ta ce. "Kenen kai ɗin ɗa ne a wajan Musa?".
Kallonta ya yi murmushi ɗauke kan fuskarsa ya ce. "Eh Mama ɗan sa na fari".