Sashe 49
Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyan zuciya Zahra ta sauke sannan ta dube shi ta ce. "Me ya sa ba za ka so Zubaida ba?, kada ka manta ita ma fa matar ka ce, ni ko ba zaka so ni ba ban damu ba, amma ya kamata a ce kana faranta mata rai tare da kyautata wa zuciyarta domin kai ɗin mijinta ne. Bana jin daɗi yadda baka sakar mata fuska baka mata wasa da dariya ba mata da miji. Ya kamata a ce ka gyara domin samm wannan ba hali ba ne". Tana kaiwa nan ta fice ta bar shi a ɗakin.
Ajiyar zuciya Sooraj ya yi yayin da ya shiga tunanin maganar Zahra. Sauke nannauyan ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce. "Ta yi gaskiya, ko ba komai Zubaida kamar ƴar uwa ta ce kuma ya ci a ce ina sakar mata fuska". Miƙe wa ya yi tare da fice wa daga cikin ɗakin da ksi tsaye ya nufi ɗakin Zubaida. Ba tare da ƙwanƙwasa ba ya shiga ciki.
Nan ya tarar da ita a zaune ta yi tagumi. Shiru ya yi yaji a rashi cewar tabbas tana cikin kaɗaici. Nan ya ji ta bashi tausayi. Gyaraj murya ya yi. Sai a lokacin Zubaida ta lura da shigowar sa.
Da sauri ya miƙe ta ce. "Yarima kai ne?, ba laifi dai nayi ba ko?".
Murmushi ya sakar mata sannan ya ce. "Shin kina jin aushi na?".
Zaro ido ya yi ya ce. "Haushin ka kuma saboda me?".
Amsa ya ba ta da cewar. "Saboda irin abubuwan da na dinga yi miki wanda na tabbata baki ji daɗin su ba".
Ɗan jimm Zubaida ta yi ta ce. "Kayi gaskiya, amma ni yanzu komai ya riga ya wuce a waje na, saidai na ce Allah ya kiyaye gaba".
Murmushi ya yi ya ce. "Yanzu me ki ke yi?".
Amsa ta bashi da cewa. "Babu abin da nake yi".
Gyaɗa kai ya yi ya ce. "Toh ki shirya zamu fita".
Zaro ido waje ta yi ta ce. "Fita kuma da ni?".
Gyaɗa mata kai ya yi ya ce. "Eh da ke, ko da akwai laifi miji ya fita da matarsa".
Girgiza masa kai ta yi ta ce. "A'a babi laifi, ai ni a shirye nake na saina shiga na chanza ba".
Nan ya dube ta ya ce. "Je ki saka hijab toh".
Da sauri ta shiga ɗakin ta tare da ɗauko hijabi jiki na rawa ta saka. Yayin da zuciyarta ya cika da farin ciki kamar wacce haka yi wa albishir da gidan aljanna".
Bayan ya saka hijabin ta fito da sauri ta dube shi ta ce. "Na saka".
Nan ya dube ta tare da hijabi maroon da ke jikinta sannan ya ce. "Da wuri haka?. Kin san me?".
Girgiza masa kai ta yi ta ce. "A'a".
Amsa ya ba ta da cewa. "Kinyi kyau sosai".
Washe haƙora Zubaida ta yi sannan ta ce. "Da gaske?, naji daɗin hakan, amma duk kyau na ban kai ba".
Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "A'a ban kai ki ba, karki manta fa bayan ƙyawun ɗawisu sai mace, to ta ina zan kai ki kyau".
Murmushi Zubaida ta yi ta ce. "Naji daɗi hakan amma dai kai ma ka san ka fini kyau, duk inda za'a zaga ni za'a ce nayi dacen miji ba kai ba".
Shiru Sooraj ya yi ya ce. "Toh shi ke nen zamu iya tafiya?".
Gyaɗa masa kai ta yi da sauri. Riƙe hannunta ya yi sannan suka fita waje yayin da suka nufi parking space. Kallon Zubaida ya yi ya ce. "Na manta je ki kira Zahra mu tafi".
Nan walwalar fuskar Zubaida ya gushe. Kallon sa ta yi ta ce. "Dama ba mu biyu zamu tafi ba?".
Amsa ya bata da cewa. "Eh ba zai yu mu barta ita ɗaya a cikin gida ba".
"Shi ke nen". Kawai Zubaida ta iya furta wa sannan ta koma ciki domin kiran Zahra.
Tana zuwa part ɗin zahra ta fara bubbuga mata ƙofa kamar zata ɓalla. Zahra da ke zaune tana kallon "tere bina" a arewa ta jiyo ana bubbuga mata ƙofa. Nan ranta ya ɓaci. Da sauri ta tashi tare da nufar kofar sannan ta buɗe.
"Ya dai ki ke bubbuga min ƙofa kamar wacce ta yi sata?".
Tsaki Zubaida ta ja sannan ta ce. "An buga ɗin ne za ki yi?".
Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Kina don ki dan abin da zan yi?, to nan gaba ki ka sake yi min irin wannan sai na cire miki wannan dogon bakin naki mai kama da na jaɓa. Wai ke a rayuwar ki bakya son zaman lafiya ne?, kin san idan rashin ji ne na fiki, na tattaka ki a rashin ji, amma me na watsar da komai. Ni ina ji ana cewa idan mace ta yi aure tana ƙara hankali, amma ke naki hankalin raguwa yake, ki dai bi duniya a sannu dan wallahi zata kaiki ta baro ki".
Zubaida kuwa ji ta yi tamkar zuciyar ta zata fashe. Dubanta ta kai kan Zahra ta ce. "Kin san dai ni ba sa'ar ki bace ba ko?, kin san na fiki aji, class da sarauta, ke da ne ki ka fi ni?".
Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Kalle ni da kyau fara nake ba baƙa nake ba. Kina son ki san abin da na fiki da shi?. Toh farko dai kin girme ni amma na fiki hankali, sannan ni ina da sauran mutunci da daraja ta a gidan aure na domin na zo da budurci na, ke da me ki ka zo. Kuma abin aushin ma me makon ki chanza amma abin ƙara tubatsa yake".
Cikin fusata Zubaida ta ce. "Kenen gori za ki yi min?. To ina ruwanki ma idan ban zo da shi ɗin ba, jikin ki ko nawa?. Wallahi in baki bini a sannu ba zanyi miki dukan kawo wuka".
Nan take Zahra ta haɗe rai ta ce. "Ɗan halak ka fasa, idan baki dake ni ba baki cika ƴar halak na".
Sooraj da ke tsaye ya ji komai da suke tattaunawa. Ajiyan zuciya ya sauke!, sannan ya ce. "Me ke faruwa a nan ne?".
Nan take suka juyo tare da kallonsa. Amsa Zubaida ta bashi da cewa. "Babu komai, muna magana ne da ita".
Kallon sa Zahra ta yi ta ce. "Ƙwarai kuwa Zubaida ta yi gaskiya magana muke yi".
Nan Sooraj ya dube su ya ce. "Maganar me?". Shiru kowanensu ta yi . Nan Zahra ta ce. "Maganar sirri ne wanda uwar gida da kishiya suke yi".
"Kenen bani da damar ji?". Cewar Sooraj.
Girgiza kai Zubaida ta yi ta ce. "Kada ka damu ba da maganar a zo a gani ba ne".
Murmushin yaƙe Sooraj ya yi ya ce. "Akwai abinda ku ke ɓoye min, ina son kuma na san mene ne wannan abun da ku ke ɓoye wa".
Shiru kowacce su ta yi. Nan Zahra ta ce. "Ƙwarai kuwa, bamu so gaya maka ba, saboda muna don muyi maka bazata ne. Dama Zubaida yanzu haka tana ɗauke da juna biyu naka, dama cewa ta yi zata maka bazata shi ne muke shirya wa".
"Juna biyu?". Sooraj ya maimaita kalmar a ransa. Nan take zufa ya fara ƙeto wa Zubaida a jiki.
Kallonta Sooraj ya yi ya ce. "Juna biyu kuma a yaushe?".
Amsa Zahra ta bashi da cewa. "Eh mana tana da juna biyu yanzu haka sati ɗaya kenen da sani. Kai da ya kamata kayo farin ciki mene ne naka na damuwa?".
Sosai Zubaida ke yin mamakin ganin yadda Zahra take rufa mata asiri amma hakan bai sa ta ƙiyi mata rashin mutunci ba.
Ajiyar zuciya Sooraj ya sauke ya ce. "Ƙwarai kuwa, kinyi gaskiya ya kamata nayi farin ciki da hakan. Idan kun gama tattaunawar kuzo ina jiranku a cikin mota zamu fita". Yana kaiwa nan ya fice.
Kallon Zahra Zubaida ta yi ta ce. "A kan me za ki gaya masa cewar ina da juna biyu?, shin kinyi hauka ne".
Kallonta Zahra ta yi ta ce. "Lallai sai yanzu na ƙara tabbatar da cewa baki da hankali, yanzu na rufa miki asiri na ce cikinsa ne a jikin ki amma ki ke cewa dan me zan gaya masa?, to so ki ke na gaya masa cewar kina ɗauke da cikin shege a jikin ki me?".
A fusa ce Zubaida ta ce. "To bana son rufa asirin naki, shirme kawai, shin na buƙaci kiyi hakan ne, mara zuciya kawai". Tana kaiwa nan ta fita.
Shiru Zahra ta yi ta ce. "Ikon Allah, yanzu ni nayi laifi dan na rufa miki asiri?. Bakomai, gaba tafi baya yawa, kin kashe kasuwar gobe". Tana kaiwa nan ta shiga ciki ta ɗauki hijabi jalbab ta fito kai tsaye wajan motar ta nufa. Nan ta ga Zubaida a gaban mota. Taɓe baki Zahra ta yi sannan ta koma back seat ta zauna.
Nan Sooraj ya tada mota yayin da mai gadi Ya buɗe musu ƙofa suka fita.
Suna cikin mota suna tafiya Zahra ta fara waƙa. "So suke suga mu tsaya cak, gashi muna ta gaba, sunƙi Allah ya nufa maƙiya ban san me nayi muku ba. Kallon biri suke min, ina musu na ayaba".
Kallonta Zubaida ta yi ta ce. "Ke mene haka za ki zo ki dame mu da waƙa?, ko an ce miki ke kaɗai ki ka iya waƙa, kiyi mana shiru".
Dariya Zahra ta yi ta ce. "Ina ta waƙa uwata bata hanan ba, ina ta waƙa uba na bai hanan ba, ina ta waƙa sarki bai anan ba, ina ta waƙa Malam bai anan ba. To tunda har Malam bai anan ba, kowa ya ce zai ana ni ubansa zanci".
Nan Zubaida da Sooraj suka zaro idanuwa waje. A fusa ce Zubaida ta ce. "Hakan me za ki zagi uba na, banza matsiyaciya kawai".
Murmushi Zahra ta yi ta fara waƙar Ali jita kamar haka. "Dole ne a barki uwar gida, dole ne a biki uwar gida, a ci arzikin ki uwar gida.. dakatar da ita Zubaida ta yi da faɗin.