← Book details Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 65

Sashe 50

Kundin Cinikayya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Karya ki ke wallahi, bani na ci arzikin ki ba ke ki ka ci arziki na".
Ganin sun ishe shi ya tsaya Sooraj ya daka musu tsawa. "Wai me ke damunku ne haka?, wai ba yanzu na ga kuna hira ba a ciki, wannan wace iriyar shirmen banza ne, toh wallahi duk wacce na ƙara jin bakinta wajen nan saina sauke ta".

Kallonsa Zahra ta yi ta ce. "Sauke ni kawai, domin ni baki na ba zai iya shiru ba, dan Allah ya gani waƙata nake yi kuma ba da kowa nake ba, ya za'a ana ni sukuni?, gaskiya indai zanyi shiru ka kunna mana waƙa ta cikin mota, in ba haka ba ni na cigaba da nawa".

Nan Zubaida ta ce "Ba za'a kunna waƙar ba motar ta ubanki ce sheg....
Bata kai ga idda maganarta ba Zahra ta wanke ta da mari. A fusa ce Zahra ta shaƙe mata wuya.

Da sauri Sooraj ya nemi guri ya yi working.

Cikin huci Zahra ta ce. "A kan me za ki yi magana kan mahaifi na?". Ƙoƙarin ƙwace kanta Zubaida ke yi amma hakan ya cutura.

Cire hannun Zahra Sooraj ya daga jikin Zubaida ya ce. "Baki da hankali ne Zahra dan me za ki mare ta?".

A fusa ce Zahra ta ce. "Dan me na zan mare ta ba, wannan ai rashin mutunci ne". Babu zato ta ji ya wanke ta da mari. A fusa ce ya dube ta ya ce. "Fitar min daga cikin mota".

Dafa fuskarta Zahra ta yi ta ce. "Ni ka mata?". Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Ƙwarai kuwa na mare ki domin rama mata nayi, kin san tana ɗauke da juna biyu kuma za ki mata haka saboda baki da tunani?, ke hanya ya kamata a kira ki da matar aure kuwa?, samm rayuwa da irin ku a gidan aure na masifa ne, ban san me ya sa na na yarda haka ɗaura mana aure da ke ba wallahi. gaba ɗaya baki da hankali, kuma wai mata ta, tirr ni dai banyi dace ba samm. Maza fice min daga cikin mota kuma ki juya ki tafi gida".

Sosai maganar da ta ratsa zuciyar Zahra. Share hawayen da ke ƙokarin zubo mata Zahra ta yi ta ce. "Wannan shi ne karo na biyu da ka mare ni. Bakomai ba laifin ka ba ne". Tana kaiwa nan ta buɗe murfin motar tare da fice wa daga ciki. Maida kallonsa Sooraj ya yi kan Zubaida ya ce.
"Kina dai lafiya ko?, dan Allah kiyi haƙuri a kan marin da ta yi miki ba ta da tunani". Cikin hawaye Zubaida ta ce. "Mu koma gida dan Allah".

"Shikenen". Sooraj ya faɗa tare da juya motar suka koma gida.

Ɓangaren Zahra kuwa bayan fitar ta daga cikin motar. Ta samu guri ta zauna hawaye na bin kan fuskarsa. Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Wato bai yi dacen mata ba ko? Hmmm ba laifin ka ba ne Soo... Ba ta kaiga ƙarasawa ba ta fashe da kuka yayin da ta saka kanta tsakanin cinyoyinta tana ta rusa kuka. Gefe guda kuma mutane suna wuce wa suna kallonta.

Har haka yi sallar Isha'i Zahra bata dawo gida ba, shi kuwa Sooraj ko a jikin da. Ɓangaren Zubaida kuwa ranta fal babu abinda ya dame ta.

Har ƙarfe goma na dare ta yi ba Zahra ba labarin ta. Hakan ya sa Sooraj ya fara shiga damuwa. Ganin ba zai iya jure wa ba. Hakan ya sa da sauri ya ɗauki maƙulin motarsa tare da fita daga gidan. Kai tsaye hanya ya shiga dubawa ko zai ganta. Saida ya yi nisa sosai a tafiya sannan ya hango ya daga nesa kwance kusa da bishiya.

Parking Sooraj ya yi tare da nufar inda take. Nan ya dube ta ya ce. "Zahra taso mu tafi gida". Ya faɗa yana mai ƙoƙarin taɓa ta. Nan ya ji ta ce. "Kada ka kuskure ka taɓa ni. Me ya kawo ka gare ni?". Ta faɗa tana mai miƙe wa tsaye.

Cikin rashin fahimta Sooraj ya ce. "Kamar ya me ya kawo ni gare ki?, kin manta ke matata ce?".

Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Zahra ta yi ta ce. "Au wai dama ni ɗin matarka ce?, kuma kake cewa samm baka yi dacen mata ba?".

Ajiyar zuciya Sooraj ya yi ya ce. "Yanzu ki bar wannan maganar ki taso mu tafi gida".

"Ba zan koma gidan ka, me zan zo nayi bayan kace baka san dalilin da ya sa ka yarda ka aure ni ba, kenen ma ba da don ranka ka aure ni ba. Toh masha Allah faɗuwa ta zo daidai da zama. Yanzu ka rubuta min takardar saki kaga saina koma gidan mu".

Shiru Sooraj ya yi ya ce. "Kiyi haƙuri Zahra, ɓacin rai ne ya sa na faɗi abinda na faɗa ɗazu. Ki tawo mu tafi".

Rai ɓace Zahra ta ce. "Ba zan tafi ɗin ba, wallahi ka bani mamaki, ban taɓa tunanin haka daga gare ka ba". Ta faɗa tare da fashe wa da kuka.

Share hawayenta ta yi ta ce. "Daga yau babu ni babu kai, kowa ya yi hanyarsa. Ni dai ba zan iya cigaba da zama a matsayin matarka ba, saboda babu amfanin zama da mijin da bai san darajar ta ba. Dama kuma kaga babu abinda ya shiga tsakani na da kai. Zamu iya rabuwa".

Furzar da iska Sooraj ya yi. Nan ya janyo ta jikin da tare da rungume ta.

ALƘALAMIN
A'ISHA MB
ZINARIYAR JAJIRTATTU
[8/21, 8:01 AM] AYEESHER MB💞💞💞: BISSMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

KUNDIN CINIKAYYA
BOOK 2
1️⃣1️⃣6️⃣➡️1️⃣1️⃣7️⃣

Da ƙyar Zahra ta amince suka koma gida bayan Sooraj ya lallaɓa ta da kalamai masu taushi.

Dutse, Jigawa
Aliyu na zaune a falo yana kallon wasan kwallon kafa, murmushi a fuskarsa. Safira ta shigo, tana sanye da doguwar riga mai kyau, farin ciki a idanunta.
"Guess what?" ta faɗa tana kallonsa kai tsaye.

"Mene ne?" ya tambaya, yana ɗaga gira.

Safira ta ɗan ja numfashi ta ce,
"Ka kusa zama Uba domin ina da juna biyu."

Aliyu ya buga tsalle cikin murna, ya ambaci sunan Allah cikin farin ciki, sannan ya rungume ta yana daga ta sama. Suka yi dariya, suka yi wani irin jujjuyawar soyayya kamar yara biyu.

Ba tare da ɓata lokaci ba, Safira ta ɗauki waya ta kira Mrs Lailah da Mom. Dukansu suka yi murna, suka ɗauki abin sha da kayan masarufi da magungunan masu ciki, suka zo gidan domin taya murna. Aka yi hira, aka sha dariya,

sannan suka tafi.

Aliyu yana cikin farin ciki ya ce,
"Yau ni zan yi girki saboda babbar kyauta da Allah ya bani." Girgiza kai kawai Safira ta yi fuskarta ɗauke da murmushi.

Bangaren Masarauta – Babban Falo

Sarki na zaune a kujerarsa mai daraja, fuskarsa cike da natsuwa, amma idonsa na bincikar kowane motsi a cikin fadar. Mami tana gefe tana tattauna wasu al’amura da masu aikin cikin masarauta.

A can ɗayan gefe, Gimbiya Saratu da Gimbiya Talatu suna zaune suna yi wa Mami kallon wulakanci. Nan suka fara magana cikin ƙasa-ƙasa, amma saboda kusa suke da sarki, Sarki ya iya jiyo su.

Saratu ta ce da murya mai ɗauke da raini
"Ni fa na gaji da ganin wannan Mami tana shisshigi cikin harkokin fada kamar ita ce ta fi kowa. Shin ita kaɗai ce ta isa wajen Sarki?"

Talatu ta ɗan yi dariya
"Ke ma kina gani? Har ta fara yin kamar ita ce uwa ba mu ba. Wata rana sai ta san da wace ta yi wasa."

Mami ta ji kalaman, amma ta yi shiru saboda girman kanta da kiyaye mutunci. Sarki kuwa ya tsaya yana sauraren su har suka gama, zuciyarsa na tafarfasa saboda ganin matansa suna yi wa uwargidan fada rashin kunya a fili.

Sai ya tashi a hankali, ya nufo inda suke. Idanunsa suka yi ja, muryarsa ta yi ƙarfi.
"Ku biyun, ku tsaya a nan!"

Dukkan fadar ta yi shiru. Duk wani motsi ya tsaya.

"Na ji maganganunku, kuma na gane niyyar ku. Kun raina Mami saboda kishin iko da girman kai. Wannan ba dabi’ar mace mai imani ba ce, balle uwa a masarauta."

Ya ja numfashi sannan ya ci gaba
"A matsayin Sarki, a ka’ida ta ya zama dole sai nayanke muku hukunci zama a ɗakin hukunci har sai na neme ku, mace a matsayin matar Sarki dole ta kasance mai biyayya, ladabi, da girmama sauran matan gida. Wannan da kuka yi babban zunubi ne".

"Daga yau, duk wata dama ta shiga harkokin tafiyar da fada ta ƙare a hannunku. Za ku koma gidan iyayen ku, ku daina shiga harkokin masarauta har sai na ga alamar tuba. Kuma dole ku nemi gafara daga Mami a fili, a gaban kowa."

Saratu da Talatu suka durƙusa, idanuwansu cike da hawaye, suka ce a tare
"Mun tuba, ranka ya daɗe. Ka yafe mana."

Sarki ya girgiza kai tare da sauke ajiyar zuciya yace
"Ni na yafe muku, A'isha za ku bawa haƙuri bani ba. Sannan kar ku manta girman ku a fada yana tare da halayenku, ba kawai saboda ku matana ba. Idan kun sake, hukuncin zai fi haka tsanani."

Sai ya umarci masu fada su tafi da su domin su zauna a ɗakin hukunci, su yi tunani kan abin da suka aikata.

Bayan an tafi da su Gimbiya Saratu da Gimbiya Talatu zuwa ɗakunansu, fadar ta cika da shiru mai nauyi. Kowa ya fahimci cewa wannan karon, Sarki ya yi hukunci mai tsauri amma adali.

Mami ta zauna cikin natsuwa, zuciyarta tana cike da godiya ga yadda Sarki ya tsai da gaskiya, ba tare da nuna bambanci tsakanin matansa ba. Dattijuwan fada da sauran matan masarauta suka fara kallonta da sabon girmamawa domin sun ga ta jure rashin kunya ba tare da ta mayar da martani ba, kuma adalcin Sarki ya fito fili.

A cikin ɗakin, Saratu da Talatu sun zauna cikin damuwa. Kalaman Sarki suna ta maimaituwa a kunnuwansu. "Girman ku a fada yana tare da halayenku, ba kawai saboda ku matana ba ne."

Saratu ta ce a hankali, tana share hawayenta. "Talatu, wallahi mun yi kuskure. Wannan kishin da ke cikin zuciyarmu ya rufe mana ido."
Chapter 50 · 0% Book details